Tsutsar Nama Book 2 Hausa Novel

Tsutsar Nama Book 2 page 32

★★

Muna shiga ya sakar min hannu. Ganin yana neman raɓani ya wuce nasha gabansa wani irin kuka mai ƙarfi na suɓuce min. Ƙin kallona yayi, ya sake raɓawa zai wuce ta side ɗin dama ta. Nan ma taresa nayi hannayena duka riƙe da ƙuguna. Tuni na cire duk wani tsoronsa da shakkarsa cike da tsiwa na ce, “Malam wai mi kake nufi da ni ne? Ka maidani gaban iyayena daka ɗakkoni bazan iya rayuwa a wannan gidan da ba’a san darajar ɗan adam ba”.
Tamkar bazai kallan ba sai kuma ya yamutse fuska tare da sake tsuketa. Cikin gadara ya furta, “Ki gayama wanda ya kawoki. Sannan bana son rashin kunya”. Daga haka yay wucewarsa. Wani irin takaici da bakin ciki ne suka sake turniƙe ni. Tuni na shiga kokawar maida hawayen dake neman zubomin. Dole ne fa ayita yau ta ƙare dan bazan iya wannan zaman ƙasƙancin ba saboda ni ba jaka bace ba. Bazan taɓa zama a maidani yanda aka maida mahaifiyarsa ba. Kaina tsaye na nufi hanyar da yabi dan idanuna sun gama rufewa da masifa. Babu ko gezau a tare dani na bankaɗa ƙofar farko dana gani a wajen. Sai da zuciyata ta jijjiga saboda karo da abinda banyi zato ba. Da sauri na juya masa baya ina mai rumtsewa da ƙarfi, jikina har rawa yake dan tunda nasan kaina ban taɓa ganin namiji babba a yanda yake yanzu ba. Su Yaya Musaddiq ko da boxer da singlet basa zama a gida. Balle kuma ace daga su sai pant kamar yanda yake. Gashi a tsaye ƙyam da suffar ƙarfi dogo masha ALLAH. Bazan iya kallon wannan abin kunya ba, dan haka na fara laluben hanyar komawa inda na fito cikin sassarfa, amma sai hakan ya gagara. Maimakon kama handle ɗin ƙofa da nake lalube sai na damƙi lallausar fata mai santsin tsiya. Da sauri na cire hannun nawa tare da daka tsalle baya ina buɗe rumtsatstsun idanun nawa. Idanu huɗu mukai da shi, tsabar rashin kunya kuma yana a yanda na gansan. Sake juya baya nayi da sauri jikina na rawa. (Wannan wane irin fitsararren mutum ne haka wai) na faɗa a zuciyata ina ƙoƙarin riƙe numfashina da tsumar da jikina keyi……..✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected