Tsutsar Nama Book 2 Hausa Novel

Tsutsar Nama Book 2 page 47

*_Typing_*

 

 

 

*_TSUTSAR NAMA….!!_*
_(Itama nama ce)_

 

_ _

 

_ _
_ _

……Ina kitchen ina ƙoƙarin haɗama Ummie madara kamar yanda na saba a kowanne dare yanzu saboda naga tana sonta sosai Hajiya Mammah ta shigo. Kamar ko yaushe tsaff take cikin kwalliya mai ɗaukar ido da ke nuna ita ɗin wacece. Sosai take matuƙar bani mamaki matar nan. Itafa dare baya hanata kwalliya kamar jikanyar ifiritai, musamman idan akace tana da baƙuwa da zata kwana a gidan. Gaisheta nai a ɗarare da ƙoƙarin kauda kai daga kallon ƙurillar da take bina da shi daga sama har ƙasa. Kadaran kadahan ta amsa min sai dai fuskarta a sake. Juice ta ɗauka ta ɗaura a samar tray tare da glass cup, sai ƙaramin bowl da aka yanka fruit yay ƙyau sosai musamman yanda kalolinsu suka fito a farin glass bowl ɗin kamar an zana, sai kuma wani haɗaɗɗen kula shima mai ƙyau duk ta ɗora, har zata ɗauka sai kuma ta dakata. Kallona tai tare da tukunyar da nake dafa madarar.
“Kandala mi kike dafawa anan?”.
Fuskata a ɗan cinkushe, na ce, “Hajiya madarar Ummie ce”.
Kanta ta jinjina tare da faɗin, “Okay Masha ALLAH. Ta kusa kammaluwa ne?”.
“A’a yanzu na ɗora ai babu jimawa”.
“Okay! To kinga zonan kimin wani aiki sai na jire miki. Awwab zaki miƙama wannan part ɗinsa. Azizat ya saka Paah ɗinsu kuma ya sakata aiki, Awwab kuma baya son jira zai iya fasa sha kuma nasan ba wani abu yaci ba”.
Ji nai kamar na fasa ihu, sai dai nasan ban isa cewa bazanyi ba. Amma a cikin raina na ɗan yi mamaki, to amma ina ruwana ba yayar babansa bace. Cikin haɗiye yawu da ƙyar na amsa tray ɗin, ɗauke juice ɗin tayi da glass cup ɗin tana faɗin, “Banda wannan nawane. Kiyi maza zan koma sama ne”.
“Okay maa”. Na amsa mata cike da jin haushi. Acan ƙasan raina kuwa jinake kamar na haɗiyi zuciyata na huta. Amma dai ba komai, dan nima kai fruit salad ɗin zai min amfani, dan dama ina son ganinsa. Dan akwai bashina a kansa, bazan taɓa barin maganar daya gasamin ɗazun da safe ba sai na maida murtani, idan ba hakaba zan iya kasa barci ma wlhy. Kamar koyaushe a nutsena nake tafiyata. Jikina da hijjab iya gwiwa mai hannu kamar kullum. Duk fa amatsayin ƴar aiki nake gidan kamar yanda shaiɗanin ya ƙalabamin akoda yaushe zaka sameni cikin tsaftata, dan inada ƙyanƙyami, ga son wanka kamar ƴar agwagwa. Komai a gidan free ne har gamu masu aiki, banbancin kawai komai zakayi kai da kanka ne masu gidan kuwa mune ke musu. A hankalin ƙamshin turaren da Ummie ta fesamin ɗazun har a cikin gashina ke tashi, sosai turaren ya kwanta min a zuciya. dan yana fidda wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa zuciyar mai shaƙa harma da kai daka saka. Na ɗakko ne zan saka mata ta fisge ta hau min feshi da shi a jikina tana dariya, bata kuwa barsa ba sai da nayi dabarar amshewa. Koba’a faɗa ba nasan an sayesa ne da kuɗaɗe masu nauyi. Murmushi na saki mai sanyi, dan yanda yake bama Ummien kulawa a gidan da kowanne nau’in abubuwan more rayuwa duk da lalurar dake tare da ita na ƙayatar dani. Sau kusan uku ina knocking amma babu alamar za’a buɗe min. “Ɗan wulaƙanci fitinanne mai girman kai”. Na faɗa a hankali ina murguɗa baki da hararar ƙofar. Cikin jin zafi na murɗa handle ɗin ƙofar na shiga falon. Kamar kullum babu yawaitar haske. Sai uban sanyin ac da mayataccen ƙamshinsa daya gama mamaye komai. Hatta kusa da mutum idan ya tsaya ko wani dalili yasa ya taɓaka koya zauna guri ya tashi ka zauna sai ka ɗeba mayen ƙamshin nan nashi. Narasa da wane shegen turare yake amfani haka. Koda yake ya wuce na tsafi. Na bama kaina amsa ina murguɗa baki. Ƙoƙarin ajiyewa nake a Centre table ɗin falon aka shigo da sallama bayan anyi knocking. Bakowa bane face Hayatu, dan haka na amsa sallamar tasa a zuciyata kawai batare dana kallesa ba na ƙarasa ajiye tray ɗin.
“Barka da dare Maa”.
Ya faɗa cikin girmamawa kamar yanda yake min yanzu musamman idan babu kowa a waje. Harara na ɗago na balla masa ina mai jan sirrin tsaki. Shiko yay ƙasa da kansa. Ƙafa na ɗaga zan bar wajen da sauri ya ce, “Dan ALLAH kiyi haƙuri. Ki kai masa bedroom inba hakaba bazai shasa anan ba. Dan muna uzirin fitane, Ummie kuma bata ƙaunar zamansa da yunwa duk yau babu abinda yaci kuma sai chocolate.”
Wata hararar na sake balla masa. Shiko ya sake marairaicewa da faɗin, “Dan ALLAH dan ƙaunar da kike ma Ummie”.
Idanuna na rumtse da ƙarfi. Kamar kar nayin sai kuma dai na ɗauka dan ni shaidace, duk randa Ummie ta cika fitina a gidan to dan gudan jinin nata ne. Sai dai kuma daya raɓeta babu sauran zaman lafiya musamman ace ya shiga ɗakin da take ko yazo kusa da ita sosai. Sai dai ya kasance a nesa da itane yanzu zata fa zuba masa ido kamar mai son tuna wani abu a kansa kosan sanin wanene shi har hotonsa haka take masa. Cikin ƴar fusatar da Hayatun ya sake saka min nai knocking ƙofar bedroom ɗin nasa da ƙaddara tasa zan masa shiga ta biyu. Nasan latsin rainin wayonsa. Zai ma iya kasancewa yana jina yay shiru, niko ina son komawa na kaima Ummie madararta tasha magani. Agadarance na murɗa ƙofar na shiga ina mai sake tsuke fuskasta da haɗa baƙar maganar dazan gasa masa da nake fatan ta hanashi barci. Wayam babu kowa a ɗakin, sai dai anan ɗin ma hasken akwai ƙaranci, sai dai yafi na falon dan anan ana iya ganin komai. Kayansa daya watsar a kan lallausan milk carpet ɗin dake a gaban gadon na ballama harara da taɓe baki. A bayyane na furta, “Ƙazami kawai sai iyayi da feleƙe, amma ba’a iya yima kai komai.” a saman bed side drawer na nufi ajiye tray ɗin, sai idona ya sauka akan bindiga. Sosai na waro idanu, jikina har tsuma yake wajen ajiye tray ɗin hannuna kaɗan ya rage ban zubar da shi ba na dai gyara masa zama ina ɗaukar bindigar. (Ta tabbata dai guy ɗin nan ɗan ta’addane. Yo anya ma ba ɗan fashi da makami bane? Kambu aiko yau zan tona asiri, zai ko tabbatar ya kawo ƴar jarida gidan nan) na ƙare zancen a zuciyata ina sakin ƙwafa a fili. Ƙofa na zabura zan nufa ina ƙoƙarin soke bindigar a cikin jikina. Dai-dai nan aka buɗe ƙofar bathroom. Naji firgici, dan yanayina ma ya nuna hakan sakamakon a yanda na jiyo na kalla wajen. Ganin shine ɗaure da towel iya ƙugu zuwa gwiwa yana riƙe da ƙarami a hannunsa zai kai shi fuskarsa amma ya tsaya yana kallona nai saurin ɗauke idanun nawa tare da zaburar son nabar ɗakin kafin ya farga da abinda na ɗauka. Sai dai me ina isa jikin ƙofar naji ta bada ƙitt alamar rufewa, duk da kuwa a rufen take dama. Ban fasa kai hannuna jikin handle ɗin ba, na murɗa na murɗa amma ko gezau tabbacin dai an kulle. (To ta yaya?) Zuciyata ta tambaya, rashin amsa da makama ya sani juyowa, sai ko idanunsu suka sauka akan ƙaramin black & golden remote dake hannunsa alamar da shi ya kulle ƙofar. Dan yanda ya ɗauke kansa tamkar baiyi komai ba ya sake tabbatar min da hakan. A ɗan zamana gidan na fara haddace mugayen halayensa a cikin kaina. Dan babu ubanda yake ragamawa da wannan murɗaɗɗen halin nasa na rashin mutunci. Ko kallona bai sake yi ba ya nufi gaban mirror ɗinsa hankali kwance. Saurin kauda idona nayi daga kansa dan dama dai a gaba ɗaya cikin sakanni da baifi goma bane komai ya faru, ban kuma iya masa ko kallon sakan ɗaya cikakke ba saboda yanayin da yake ciki, dan ma babu yawaitar haske a ɗakin ne shiyyasa.
A bazata cikin dakewarsa da daƙilallen yanayi irin na mugayen muskilan mutane a silent voice ɗin nan nashi ya furta, “K idonki bazai daina gane-gane ba ko?”.
Sam da farko bammayi zaton shine yay maganar ba. Sai da nai ɗan jimmm sannan na fahimta. Baki na murguɗa batare dana kallesa ba cike da tsiwa nima na furta, “In dai masu mugun halin ta’addanci na a inda nake gane-gane ma yanzu ya fara ai. Kuma in kere na yawo zabo na yawo wataran za’a gamu. Adai juri zuwa rafi. Saboda wataran tulu zai fashe a tsakkiyar kasuwa. Dan in ma an binne wani abun wani bazai binnu ba. Musamman ma Samraah Abdul-wahab Gwarzo”.
Shiru bai tanka min ba. Ni kuma na kasa iya ɗaga ido na kallesa saboda a yanda yake samandagari guda babu riga ƙaton kawai. A bazata matuƙar bazata naji tsaiwar mutum a kaina daf, ai bamma san sanda na ɗago ba a harmutse. Ƙamshin turarensa ne yay mugun rige-rigen shiga min hanci saboda iskar razana dana shaƙa da ƙarfi. Kusancin namu yayi yawa dan haka nai matuƙar zabura baya ina ƙyaƙyƙyafta idanu uwa ya na namijin biranya. Hannu ya miƙomin alamar na bashi. Nasan bindigarsa yake nufi, amma sai na balla masa harara na ɗauke kaina. Dan ya kafeni da muggan idanunsan nan na maguna. Sai dai yanda nake a tsorace yasa a ankare nake karya shammaceni. Ina kuwa ganin ya motsa na sake zabura baya. Ganin kaina yayo na ɗage zan falla da gudu koda cikin bathroom ɗinsa ne tunda ya kulle nan mugun yasa ƙafa ya taɗoni, sai gani zube a saman gadonsa…….✍️

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected