Ajiya A Duhu BOOK 1 Na Billyn Abdul

Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 27

????2??7??

……..Maimakon Hajiya Basariyya taji haushin furucin ?ar tata sai ta tuntsure da dariya tana fa?in, “Ja’ira wato ke ?ar da?i soyayya ko? Kwantar ma da hankalinki komai zaizo da sau?i bani lokaci dai nayi tunani.”
“To Ummi nidai dan ALLAH kar tunanin naki ya wuce yau da gobe dai. Dan a matse nake gashi nayi kewarsa ina son ganinsa.”
Anan ?in ma dariya Hajiya Basariyya ta sanya abinta.

__________?

A can ?angaren Aunty Sabuwa ma shiri takema ?arta na mugayen mallaka, dan hatta da Hajiya Yaya aba’a ?yaleba tuni sunanta na wajen boka. Kai shi kansa Daddyn ba tsira yay ba da sauran ?annen Yazeed mata. Dan tace tako ina sai ta bama ?arta garkuwa. Tako bayar ?in gwagwargwadon abinda take ganin ya wadaceta. Ga maganin mata ana ?irkama Nazeefa kamar babu gobe, gefe kuma fetsararrun ?awayen uwarta su Hajiya Malika na koya mata kissa da kisisina harda salon kwanciya da miji.
A tacan ?angaren Mahaifinta kuwa yana nasa shirin ne akan Daddy. Dan a wannan karon yaci alwashin samawa kansa nasara akan Daddyn. Sai kuma shirin biki na ?ar gata da sukeyi da ga shi har Aunty Sabuwa ?in.

Ata nan ?angaren Hajiya Yaya shirin suma suke na garari, dan a satin nan zata wuce Dubai ita da Baraka da Asalamiyya su ha?o lefe da nasu kayan cin bikin. Da farko Daddy ya hana tafiyar, saboda ya fahimci ana komai ne dan ?untatama Ammie. Amma sai Ammien ta dinga masa roko da magiya dan tasan hanawar wata sabuwar rigima ce, kuma dai laifin a kanta da baya so zai ?are. Dan tuni Hajiya Basariyya tayi uwa tayi ma?aukiya a bikin shiyyasa ita ake kiranta ?ar ba?in ciki. Haka dai dole Daddy ya bari dan yana matu?ar jin kunyar Ammie ta ro?esa abu ya kasa mata saboda dattakonta itama, sai dai da shara?in karsu wuce sati ?aya, idan kuma hakan ta faru zasu sha mamakinsa. To a hakan ma dai Ammie bata tsira ba dan sai da tasha zagi da habaice-habaice. Ita dai bata kulasu ba kamar yanda ta saba. Sai ma ta maida hankali akan shirin Daddy da shima yake yi dan wannan shine karo na biyu da zai aurar. Na farko ya aurar da su Shahidah da Asalamiyya a rana ?aya, duk da dai an kwashi matu?ar rikici a wannan aure dan Hajiya Yaya cewa tai baza’a ha?a mata auren ?a da agololi ba. Shiko yace tayi ka?an tayi tsororo ma.  Bayan dai an sha fama dole ta ha?ura akayi yanda ya tsara ?in. Sai dai ita Asalamiyya ma nata auren bamai jimawa bane. Dan a gida ma ta haifi ?arta. To yanzu ko Yazeed ka?ai za’a aurar. Babban ?ansa kuma namiji, sannan ?a mafi soyuwa a garesa da Hajiya Yaya. Damma ALLAH ya ragewa aya za?inta auren ba wanda yake so bane ba. Saboda har yanzu sam Daddy baya son wannan ha?in kawai dai babu yanda zai yi ne ya ha?ura. Amma yaci alwashin sai ya bama kowa mamaki a auren Maanal da Yazeed in sha ALLAHU.

To daga can gidan Alhaji Mamman ma dai shirin suke. Dan jikokin duka biyu nasu ne, dan haka dole suma su taka tasu rawar da aljihunsu da kuma matsayinsu. Dan haka suka kasance cikin irin nasu shirin su da sauran ?a?ansu da dangi. Dan ko tafiya Dubai ta zama kamar za’ayi ta a tare ne bisa ?angarori biyu. Ba Hajiya Yaya da Asalamiyya da Baraka bane kawai a tafiyar harda mahaifiyar su Hajiya Yaya ?in da kuma wasu ?annensu Hajiya Yayan su biyu, da harda Aunty Sabuwa amma ta zamewa tafiyar dan akwai binne-binnen da suke son zuwa suyi a inda za’a saka amarya duk da ma Daddy ya ?ata musu tafiyar da buri wai anan gidan su Yazeed ?in zasu fara zama a tare da su. A yanzu hakama ana kan gyara sashen samarin gidan da dama shine dai zaune a ciki kasancewarsa namiji tilo a baya sai yanzu da Ammie ta haifi Waleed da Hameed. Suma acan ?in suke amma yanzu Daddy yasa ana musu nasu ginin ata can bayan na Yazeed ?in kasancewar akwai fili sosai. Sai suka dawo sashen Ammie yanzu tunda ita ka?aice. A wannan gini ma dai sai da akai ?an rikici, ?an daga Hajiya Yaya har Hajiya Basariyya nunawa sukai basu yarda ba. Sai da Daddyn yay musu kaca-kaca yace idan akwai wadda ta haifesa a cikinsu kota saya masa gidan ko suka ha?a ku?i suka saya to tazo ta hanashi yima yaransa wajen zama sannan suka kama kansu. Amma hakan bai hanasu komawa gefe suna zagin Ammie ba da aibantata.

___________?

Shine ya fara fita a elevator ?in, hakan yasa AS da driver rufa masa baya cikin hanzari. Cikin takaici da ?unar zuciya Maanal ta raka bayansu da harara kafin itama ta fito tana jan tsaki. Maimakon tabi bayansu sai kawai ta samu waje ta zauna anan wajen elevator ?in. Tsahon mintuna goma sai ga AS ya dawo wajen. Da mamaki yake fa?in, “Ina can inata tunanin inda kika ma?ale ashe kina nan.”
?an ?agowa tai kawai ta kallesa batare da tace dashi komai ba. Shima sai ya kama kansa dan ya fahimci Maanal irin mutanen nan ne masu masifar miskilanci da kame kai. Har office ?in Directors Mustapha ya kaita, sai dai sun samu baya ciki da alama ya ?an fita. Wajen zama ya nuna mata yana fa?in, “Ki jirasa anan duk inda yake nasan baiyi nisa ba”.
Kanta kawai ta iya jinjina masa. Shima sai ya juya ya fita abinsa. Bayan futarsa ajiyar zuciya ta ?an sauke da numfashi mai ?arfi. Dai-dai lokacin idanunta suka sauka akan hotuna hu?u da aka saka daga can saman saitin inda kujerar mai office ?in take. Hoton farko shugaban ?asa ne a jiki, sai Ministan Abuja. Hoto na biyu AA Darma ne da yay wani kalar masifar ?yau, sanye yake cikin wasu shegun suit ba?a?e da adon gold a jikinsu mai matu?ar ?yalli, ya?an zauna a saman kujera mai tsaho ?in nan, sai ya kasance kamar ya zauna a karkace ?afarsa ?aya ya sakko ?asa sosai ?ayar na daga jikin ?arfen da akaima kujerar kwalliya. Takalminsa ba?i da kwalliyar gold shima. Bai saka rigar suit ?in ba, yana ri?e da ita ne kawai da hannunsa na dama dake sanye da agogo kalar gold a saman kafa?arsa, sai farar long sleeve shirt ?in data sauna ?aran a jikinsa ta fiddo da girman jikin dake a bu?e. Ya saki wani mayataccen murmushi daya sakata ?urama cikakkiyar fuskarsa mai kwarjini da adon gashi ido. Idanunsa sanye da farin gilashi da tun ?uruciya tasan yana sakawa. Sun wani haska oily idanun nasa da suke farare tas kamar an watsa musu madara tsabar yanda suke ?yalli da ?aukar idanu….
Ka?an Director Mustapha ya ?an bubbuga desk ?in, dan sai sallama yake amma babu alamar tasan da shigowarsa. Numfashi ta ?an ja ta fesar cike da kame kanta da vasarwa ta dawo hayyacinta. Murmushi ya ?an yi a ?asan ransa yace (Boss Sarkin sa’a. Akoda yaushe cikin kama zuciyar ?ammata yake).
Ita kam kicin-kicin ta sake yi da fuska sannan ta shiga gaishe da Director ?in. Ya amsa mata da kulawa tare da mata barka da zuwa. Kanta kawai ta jinjina masa shi kuma yakai zaune yana ?aukar file ?inta ya shiga dubawa. Sai lokacin ta sake bin office ?in da kallo daki-daki, idonta ta ?arasa saukewa akan hoton AA ?in, sai kuma ya janye ta maida kan ?ayan hoton dake kusa da nasa da bata kalla ba. Mace ce sanye cikin ba?in hijjab da ni?ab, hatta idanun nata ana iya ganinsu ne kawai ta cikin sirrin farin gilashin data sanya. Hakan yasa baka isa tantance wacece a hoton ba duk iya kallon ?urullarka da bin ?wa?wa?wafi, dan hoton yasha editing ta yanda aka ?adda kamanin komai.
A hankali ta ta?e baki da sake kauda kanta zuciyarta na ayyana ma maybe matarsa ce. Tunku?e tunanin tayi gefe ta maida hankalinta ga Director Mustapha dake mata magana. Umarnin biyosa ya bata, babu musu ta mi?e tare da ?aukar hand bag ?inta tabi bayansa. Wani office dake kusa da nashi suka shiga. Nan ma sun sami mai office ?in daya kasance ba bahaushe ba. Bayan sun gaisa ya amshi file ?in hannun Director Mustapha ya saka hannu. Daga haka suka fito. A ?ofa suka ha?u da wani matashin saurayi, cike da girmamawa ya shiga gaida Director. Shima ya amsa masa da kulawa yana nuna masa Maanal.
“Itama Watch Designer ce, kaje da ita department naku, sit ?in da aka shirya jiya nata ne”.
Fuskar saurayin da murmushi yana kallon Maanal ya amsa ma Director da girmamawa. Ita ko sai wani basarwa take. Bai damu ba ya fara gaidata, sai ta amsa kamar wadda taji kunya. Shi dai director kallonsu kawai yake yana sake jinjina miskilancin yarinyar.
Saurayin daya kira sunansa da Yaqub tun’a cikin Elevator ?in ya gabatar mata da kansa matsayin Watch Designer shima. ?an murmushi kawai Maanal ta masa. Dan ta fahimci yana da nutsuwa. Koda suka fito anata kallonsu, bata damu ba dan ita babu wanda take kallo har suka iso rukunin su daya kasance matsayin office. Su takwas ne, kuma duk artists ne suma ?in, sai dai abin damuwar ita ka?ai ce mace a cikinsu. Amma sai ta dake, dan tasan zata iya zama da kowa. Ta gaishesu tana sake ?aure fuska ganin yanda suke kallonta. Yayinda Yaqub ya gabatar da ita a wajensu shi dai. Suma ya shiga gabatar da su da sunayensu ?aya bayan ?aya. Kafin ya nuna mata wajen zamanta dake a farko. Sun mata maraba da zuwa cikin farin ciki, itama sai ta ?an musu murmushi ka?an. Daga haka takai zaune tana dudduba komai nata dake a wajen. Batare data damu dasu ba kuma wayarta ta ?auka ta shiga ?aukar komai na iya wajenta hoto, Ammie ta turamawa, alamar wayar a hannun Ammie take mintuna biyu ba’a ?ullaba sai ga video call ?in Ammien ya shigo. Murmushi mai sanyi Maanal ta saki tana mai gaggawar amsa kiran sai ga Ammie tar-tar ta fito. Cikin murmushin farin ciki Maanal tace, “Uhm kaga amaryar Daddy”.
Da?uwa Ammie tai mata itama tana murmushin ta ce, “Ungo naki nan ja’ira yau kuma nice bar tsokanrki”.
Karo na farko Maanal ta sanya dariya, abinda kakan da?e a yanzu baka gani ba a tare da ita. Duk ko sai samarin suka shagala suna kallonta duk da su basa ganin Ammie sabo a desk ta ?aura wayar. Ita ko cikin rashin damuwa da wanzuwar su a wajen tace da Ammie, “Tom yi ha?uri Hajiya Ammie na. Ina fatan kin tashi cikin aminci da ?oshin lafiya tare da farin ciki a wannan rana ta laraba ranar samu inji Nene”.
Sosai murmushin Ammie ya sake ?awatuwa. Da kulawa ta ce, “Alhamdullah Auta. Ya ?arfin jikinki? Ya kuma sabon office?”.
“Alhamdullahi Ammie na warke abuna. Sabon office kuma gashi ki sanya masa albarka daga bakinki mai tsarki”. Tai maganar tana mi?ewa da wayar a hannu ta maida back camara tana haska mata ko’ina na office ?in, sai dai koda wasa bata yarda ta hasko samarin nan ba. Sosai Ammie ta shiga yabawa da sanya albarka. Ta kumayi addu’oi sosai ga autar tata. Sannan suka ?an yi hira sukai sallama tace ta fara aikinta. Fuskarta da murmushi ta ajiye wayar, ita ka?ai tasan irin tari-tarin ?aunar da takema wannan baiwar ALLAH. Mahaifiyarsu dabance a cikin daban ?in da bazai ?ididdigu a zukatansu ba. Fatansu dai ALLAH ya ?ara mata lafiya da nisan kwana masu albarka. (Tare da iyayenmu baki ?aya. Ka gafartama wanda muka rasa ka yafe musu KURAKURANSU???? damu da muke raye baki ?aya).
Jan kujerar tata tai har zuwa gaban kantar da aka ajiye musu a office ?in dan kusan da ita ma aka zagaye wajen. Komai na kayan zane-zanen da zasu iya bu?ata akwai a wajen. A haka ta zazza?o duk abinda take bu?ata a lokacin ta sake burko tayoyin kujerar ta dawo da ita mazauninta. Sosai ta ringa ?o?arin ture komai a ranta ta maida hankalinta ga fara abinda ya kawota duk da tana ji a jikinta sauran abokan aikinta hankalinsu na a kanta ta wani sharesu tamkar ita ?aya ce a wajen.
Wani zanen Designs na agoguna data ?ir?ira yanzun nan a kanta ta fara cike da ?warewa. Cikin ?an?anin lokaci ya ha?a su tsaf su biyu kamar ka saka hannu ka ?auka daga takardan. Bayan ta gama zana su a dun?ule sai kuma ta koma zana ?angare-?angare ?in jikinsu kowanne tana saka masa suna da amfanin da zai yi a cikin agogon. Hakanne ya ja mata lokaci sosai dan har ?arfe ?ayan rana. Jin ana kiran sallar zuhur daga masallacin cikin companyn ya sata sauke ajiyar zuciya da ajiye kayan aikin nata ta mi?ar da hannunta da ya ?an sage da ambaton sunan ALLAH.
Mi?ewa tai zuwa window ?in office ?in ta le?a batare data ma kowa magana ba, dan daga wajen ana hango masallacin. Hango ma’aikata tayi nata fita zuwa ?atuwar harabar companyn. Ganin mazansu da matansu ne yasa ta fahimci masallacin harda mata kenan. Dan wasu ma na ?o?arin shigane yayinda wasu suka kasance rukuni-rukini suna hirarsu. Sai wasu dake alwala ta can ?arshen katangar inda aka tanada domin hakan. Huci ta?an furzar daga bakinta tare da barin wajen, dai-dai suma su Yaqub na mi?ewa. Sauran fita sukai gulma fal bakinsu, yayinda shi kuma Yaqub yazo inda take.
Shine ya sanar mata tazo suje salla. Kanta kawai ta jinjina masa ta baro wajen ALLAH ya sota ta taho da hijjab kasancewar yau ma shigar Abaya ce a jikinta ?irar Dubai ruwan ?asa. Hijjab ?in ta bu?e ta saka bayan ta zame hularta da ?an kwalin abayar data na?o a kanta ta ajiye saboda hijjabin ya rufe mata gashinta sosai. Hankalinta kwance kuma kanta tsaye ta fito a office ?in daga ita sai wayarta kawai a hannu. Kusan duk an fice ma, dan wajen yayi tsitt, dan haka a gaggauce ta nufi elevator jin za’a tada sallar kasancewar su suna a 4th floor ne. Bata gama dai-daita tsaiwarta ba kawai taji shigowar mutum babu ko sallama. Dan haka ta ?ago manyan idanunta domin ganin wane sallamemmen ne haka……..??

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected