AƘIDA TA COMPLETE HAUSA NORMAL
Asslam Alaikum warahmatullah, A madadina, ƙungiya ta da kuma ‘yan uwa na da abokan arziki, ina taya Ɗaukacin Al’ ummar Musulmi barka da salla, tare da fatan anyi salla lafiya, ina fatan ubangiji Allah ya karɓi ibadunmu da mukayi a watan Ramadan, sannan ina Fatan Allah yasa mu ɗore da ibadun da mukayi a watan Ramadan, Taku har Kullum
AISHA HUMAIRA (Daddy’s girl) ko kuma ince Ayshercool kaman yadda wasu suka fi sani.
TALLA! TALLA!! TALLA!!!
Ina masoya wanda suka bibiye ni a littafina na ABDUL JALAL, da kuma WATA KISSAR yanzu ma na shirya tsaf domin kawo muku wani ƙasaitaccen littafin me ɗauke da sabon salo da kuma sarƙaƙiya,
ga ɗanɗano daga cikin littafin
_*AƘIDA TA*_ *PART1*
_Page 1_
*written and edited by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy’s girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
Bismillahir rahmanirrahim, da sunan Allah me Rahama me jin ƙai, Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko cin fuska ga wani ko wata ko wata ƙabila ba, idan har wani ko wata yaga wani abu daya yi kaman ceceniya da rayuwar sa ko ƙabilar sa Amin Afuwa banyi dan cin zarafin wani ko wata ba.
Wannan littafin mallaka tane, ban yadda a juyamin labari ta kowane fanni ba ba tare da izinina ba.
Katafaren ɗakin Bacci ne me ɗauke da kayan alatu na more Rayuwa da jin daɗi, idan ka ƙarewa ɗakin kallo zaka tabattar da ma’abocin wannan ɗakin Allah yayi masa Ni’imar Dukiya dan ya ƙawatu da dukkan wasu kayan more rayuwa, kallo ɗaya zakayiwa ɗakin kasan mamalakin ɗakin mace ce, saboda kan madubin dake ɗakin shaƙe yake da kayan kwalliya da gyaran jiki, ga wani show glass ɗauke da takalma da jakunkuna na adon mata kamar wani kantin saida kayan ado, kai da ganin takalma da jakunkunan nan kasan bana talaka bane, Makeken Gadon dake ɗakin ne ɗauke da wata kyakywar matashiyar budurwa ta baje gashin kanta tana bacci cikin nutsuwa.
Hasken ranar da ya ratso ta tagar ɗakin ne yake dukan fuskarta wanda hakan yasa ta motsa a hankali, ta buɗe idanuwanta.
Ɗan ya mutsa fuska tayi, ta miƙe zaune ta kalli Agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe tara da rabi na Safiya, a hankali ta zuro ƙafafuwanta ƙasa ta miƙe ta nufi banɗakin dake cikin ɗakin nata.
Aljannar Duniya shi kansa ba ɗaya nata ya isa a tsaya a kalla.
Wanka matashiyar tayi ta fito daga ita se towel, abun mamaki har an gyara mata inda ta tashi, ta zauna a gaban mudubi, ta shafa wannan ta goga wancan, gashi komai nata a hankali cikin nutsuwa take aiwatar dashi, riga da skirt na blouse ta ɗakko ta saka da ɗan guntun mayafi, ta ɗora akanta tasaka takalmin ta me matuƙar tsini da jakarsa, seda ta kalli agogon hannun ta ƙarfe goma da rabi dai dai sannaan ta buɗe ɗakin ta fito.
Wani irin taku take na ƙasaita, takalmin ta na bada sauti ƙwas, ƙwas, ta fito wani irin ƙaton falo ta zauna, ba ta daɗe da zama ba, me aiki ta kawo fruit gabanta ta ajiye, bata kalli inda fruits ɗin suke ba, se kallon tsintsyar hannun ta da ta ɗaurawa Agogo take yi.
“wato Isa rayuwar ƙauye akwai daɗi akwai wahala”
Wanda aka kira Isa yace
“Haba ɗan uwa wani irin daɗi a ƙauye? Kai ka taɓa ganin wanda yake birni ya koma ƙauye banda zunzurutun wahala mene ne a ƙauyen?”
“to ai Rayuwar ƙauye tafi ta birni kwanciyar hankali, ba tashin hankali ba fargaba, amma kaga birni a nan rashin gaskiya ya ƙare”
“tabdijan lallai ma sani, ai tunda Allah ya kawoni birni na samu aikin gadin nan, idan naje ƙauye to ziyara na kai Amma bani babu zaman ƙauye ina daf da dawo da iyalina nan ma”
“kai gidan nan zaka dawo da iyalin naka, kaifa kace min zaman fargaba kake a kowane lokaci za’a iya sallamar ka fa”
Isa yace “rufamin Asiri in kawo iyalina gidan nan Haya zan kama”
Suka ci gaba da hirar su tare da yin taɗi akan rayuwar birni da ta ƙauye
Sake kallon Agogon ta tayi har sha biyu saura minti goma sha biyar, miƙewa tayi cikin takunta na isa ta fito harabar gidan, kai tsaye ta nufi bakin gate, inda me gadi ke zaune yana hira da abokin sa sani suna cin gyaɗa.
Isa Yana hangota ya miƙe jiki na rawa yace “Allah ya temake ki, barka da fitowa” bata amsa masa ba tace
“har yanzu Sabo driver bezo bane?”
Cikin girmamawa yace “Eh ranki ya daɗe be ƙaraso ba”
Haɗe rai tayi ta jinjina kai ta koma cikin gidan
Sani yace “Isa ita kuma wannan wacece naga jikin ka se rawa yake dan tazo” sani ya tambaye shi
Isa yace
“kai bari kawai, itace ‘yar masu gida bata da wa, bata da ƙani shalelen Alhaji kenan, watan ta uku da dawowa daga ƙasashen Turai, yarinyar nan sam bata taɓuwa, gaba ɗaya halin turawa shi take yi, yau kam kashin sabo ya bushe wallahi ”
Sani yace “kamar ya kashin Sabo ya bushe meze faru?”
Be ƙarasa maganar ba aka fara bubbuga gate ɗin gidan, da sauri Isa yaje ya buɗe, wani mutum ne a ƙalla ze shekara Arba’in ya shigo kaman an koro shi.
Isa ya kalle shi yace “Taɓɗijan sabo yau kashin ka ya bushe, yanzu ta fito gurin nan neman ka”
Wanda aka kira da Sabo ya shiga rafka salati “na shiga uku yanzu ya zanyi, wallahi yarona ne babu lafiya na kaishi chemist”
Isa yace “ai bani za kayi wa bayani ba, seka je ka same ta”
Suna cikin maganar ta kuma fitowa, Fuskarta a haɗe babu annuri ta kalli sabo tace
“ƙarfe nawa nace maka zan fita?”
Jiki na rawa yace “ƙarfe sha ɗaya ranki ya daɗe”
“yanzu ƙarfe nawa ne?”
“shabiyu da minti goma”
“good, bani mukullayen motocina”
Sabo yace
“dan girman Allah kiyi hakuri ranki ya daɗe, wallahi yarona ne ba lafiya na kaishi chemist”
Cikin tsawa tace “shut up, did I ask you? Kabani keys ɗina”
Durƙusawa yake ƙoƙarin yi amma ta dakatar dashi “kai motocin na ubanka ne ko nawa?”
“naki ne Hajiya”
“idan har nawa ne, ka kawomin makullayena, na sallameka za’a bawa me gadi kuɗinka ya baka, daga yau se ya zama izina a gare ka, Alƙawari yana da mahimmanci cika shi alamace ta amana, lokacin aiki dana ɗauke ka mallakina ne ba mallakin ka ba tunda biyan ka nake, dan haka seda izinina za kayi duk wani abu komai girmansa in ba ibada ba tunda biyan ka nake”
tana gama maganar ta juya ta koma cikin gidan.
guri sabo ya nema ya zauna ya dafe kansa yana salati.
Isa yace “Sabo se dai haƙuri, Allah ya baka aikin da yafi wannan”
Cike da damuwa Sabo yace “Ameen Isa, Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, idan ta bada sauran haƙƙin nawa nazo in karɓa”
Sukayi sallama Sabo ya fice daga cikin gidan zuciyar sa a cunkushe babu daɗi.
Bayan tafiyar Sabo,
Sani cikin damuwa yace “wai Bala in tambaye ka mana, ita bata da mafaɗi bata san dai dai ba, bata san Afuwa da uzuri ba?”
Bala yace “Taɓɗijan kai kasan su amma ita kam bata sansu ba, wannan da kake gani tana da wata irin muguwar AƘIDA da ta tashi akai saboda rayuwa da turawa, zuciyar ta kaman Arniya gaba ɗaya Aƙidun turawa ne da ita bana musulunci ba, babu wanda ze iya raɓarta su zauna lafiya, Akwai matar mahaifin ta dake gidan nan ita da ‘ya’yan ta, seta yi sati biyu seta ga dama za su ganta balle maganar fatar baki ta haɗa su, ta maida su tamkar bayin ta, idan kaga dariyar ta to da Mahaifin ta ne, da wani babban Aminin sa, ko wasu ƙalilan daga ƙawayen ta, bata da yadda sam, gani take duk wanda ya fiye raɓarta ba shi da gaskiya, Sabo shine driver na huɗu da tayi bayan dawowar ta Nigeria, ga Albashi me kyau ga mahaifinta da kyauta, amma kowanne ma’aikaci da ƙafarsa yake guduwa saboda izza da bala’in ta, ‘yan aiki kuwa koni na kawo shida daga garin mu amma da ƙafarsu suke guduwa, yanzu kalli duk haƙuri da ƙoƙari irin na Sabo kaga yau yadda ta wulaƙanta shi ta kore shi”