interstitial
Ajiya a Duhu Book 2 Na Billyn Abdul

Ajiya a Duhu Book 2 Na Billyn Abdul

[5/21, 10:48 PM] Zainab Muhamma: *_Typing_*

 

*_AJIYA A DUHU…._*

 

*_Bilyn Abdull ce _*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama_

BOOK 2
️➖1️⃣

______________

*_Assalamualaikum. Barkanku da wannan lokaci, fatan ansha ruwa lafiya? Anyi salla lafiya?. UBANGIJI ya karɓi ibadunmu, ya yafe mana kurakuranmu, yasa muna a cikin ƴantattun bayi. Ina mana Barka da dawowa filin daga, ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda bazai cutar dani da ku ba. Ka tsarkake min alƙalamina domin rahamarka. Ka gafarta ma iyayenmu da malamamu damu baki ɗaya. Ka ɗauramu a bisa tafarki madaidaici da bazamuyi dana sani ba. ALLAH ka hanamu cutar da junanmu koda da kalma mara daɗi ce._*

_Ayi mana afuwa da jinkirinmu yau da gobe sai ALLAH ❤️._

*Ƴan ƙungiyar Bati ku matso nan munada meeting . Kun san dai AZUMI aka gama ko, goman ƙarshen nan hummmm karki yarda ki zama a cikin wanda na ɗaga hannu nace ya ALLAH gasu nan….*
_Bazan dai ƙarasa ba amma gaskiya kada ki yarda sister dan in dai an amsa akwai cakwakiya gaskiya _ 500 kacal ne

_____________

……..Sosai ciwon kai yay ma Maanal rijib a wannan yinin isowarsu Abuja, shima kuma AA ɗin zuwa yamma dole aka saka masa drip ma, dan sam baya jin wani ƙarfin jikinsa. Har cikin dare ba’a gama saka masa ruwan ba dan kusan leda uku ne. Dole Fawzan ya kwana tare da shi bisa umarnin Abah. Oum taso yin magana amma tai shiru, dan ita so tai ta kawo Maanal a daren sashen AA ɗin, amma ta fahimci take-taken Abah so yake ya kawo wani sharaɗin hora AA ɗin, dan dama shine ya bata umarnin wucewa da Maanal sashenta sanda suka iso.
Bayan sun baro sashen AA bin bayan Abah tai nasa sashen ta masa magana, amma sai ya nuna mata shi barci yake ji ta barsa dan ALLAH. Haushi ne sosai ya kamata, dan haka fuuu ta baro sashen. Da kallo ya bita ganin yanda ta wuce, sai kuma ya shiga girgiza kansa a fili ya furta, “Fateema son yaranki yayi miki yawa, in dai fushi ne ƙyama sakko dan sai na hora Ajwaad a gidan nan”. Daga haka ya shige toilet yana murmushi…

___________★

Zuciyar Babban Yaya cike da wasi-wasi ya nufi sashen Oum ganin har goma saura na dare yau ma Maanal bata koma sashenta ba, ga AA ɗin kuma ma jikin nasa ya dawo dan yanzu haka wani ƙarin ruwa aka cire masa. Ganin bata a falo ya nufi bedroom ɗinta. Sai da yay sallama ta amsa tare da bashi izinin shiga sannan ya shigan. Yanayin yanda take a zaune da fiskarta dake cike da damuwa yasa gabansa faɗuwa, duk da yasan akwai damuwar yanayin da Auta ke ciki dai.
“Oum baƙya jin daɗi ne?”.
Ya faɗa cike da damuwa matuƙa yana kaiwa kusa da ita zaune. Idanu ta zuba masa kawai, dan duk yanda taso yin murmushi ko sassauta damuwar tata hakan ya gagara sam. Sai ma ƙwalla kaɗan da suka taru mata a idon. Ai sai babban Yaya ya sake rikicewa matuƙa.
Hannunsa ta riƙo tana girgiza masa kai, “Kaga kwantar da hankalinka bafa wani abu bane ba.”
“Haba Oum yazan yarda da hakan, kalla fa yanda damuwa ta bayyana a fuskarki sosai. Dan ALLAH in ma dan ciwon Auta ne ki daina tada hankalinki komai zai wuce kamar ba’ayi ba in sha ALLAHU. Dan yanzu hakama barci yake yi na cire masa drip ɗin dan ya ƙare. Jikinsa sam kuma babu zafi da ganin yanda yake barci ma kasan Alhamdullah babu wani damuwa ba kamar jiya da yinin yau ba. Yanzu haka ma nazo ne akan batun Maanal, nazata zata kwana a can ne yau ai tunda jikin da sauƙin itama?”.
Sosai ɓacin ran Oum ya ƙara bayyana akan fuskarta, ta ce, “Akan hakanne ai Abanku ya ɓata min rai Fadeel, yace wai bazata koma can ba yanzu sai bayan salla ya koyama Ajwaad hankali. Wane hankali kuma ake buƙatar koyama yaron nan bayan wanda ya koya. Kama ajiye batun wahalar ciwo da yasha a shekarun baya, a kwanakin nan kawai kaga hanlin daya shiga fa da wanda yake a ciki yanzu. Kowa fa a rayuwa da irin yanayinsa da kuma ƙaddararsa, amma Abanku ya kasa fahimtar hakan, ya kasa fahimtar Ajwaad nada zurfin ciki ne. Yanda Maanal keda muhimmanci a garesa bana tunanin dole sai ya buɗe baki yace wani abu za’a yarda dashi. Shin so yake na rasa yarona ne saboda wannan tsaurin nasa?”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa kamar zata saki kuka.
Cikin sake rikicewa sosai Babban Yaya ya shiga girgiza mata kai nasa idanun na kaɗawa sosai shima. “Dan ALLAH Oum ki kwantar da hankalinki, ni bara naje na samesa yanzu. Ko kuma ki kira Baba ko Abba ki haɗashi da su…..”
“Saboda ban isa da gidana ba kenan ko mai uwa?”. Atare babban Yaya da Oum suka juya da sauri suna kallonsa, ƙarasa shigowa cikin ɗakin Abah yayi, cikin nuna ɓacin rai sosai ya cigaba da faɗin, “Saboda biyan buƙatar taka uwar ni a kira nawa iyayen a haɗani da su. Lallai Fadeel sannu, nace sannu kaji ko!”.
“Kayi haƙuri Abah ni ba haka nake nufi ba, amma Oum fa……”
“Malam tashi ka wuce sai da safe.”
Abah ya sake katseshi cikin sake nuna ɓacin rai. Kallon Oum Babban yaya yayi idanunsa na sake kaɗewa, kanta ta jinjina masa alamar yaje ɗin. Dan haka ya miƙe kawai ya nufi ƙofa. Da kallo Abah ya bisa, sai kuma ya girgiza kai a zuciyarsa yana ayyana (su dai akan uwarsu kowa ma ya mutu har liman babu ruwansu). A fili kam dubansa ya maida kan Oum data ɗauke kanta gefe tamkar ma bata san da shi ba a ɗakin. Sai kuma ta yunƙura zata miƙe. Yasan mi zatayi, dan haka cike da bada umarni ya ce, “Koma ki zauna”.
Komawar tayi ta zauna, kafin ta ɗago idanunta da suka sake kaɗewa a karo na farko ta kallesa, aiko ya sake yin kicin-kicin da fuska harda ɗan willa mata hararar data sakata janye idanun nata a kansa sannan ya furta, “Oh ke yanzu saboda na yanke hukuncin daya dace akan ɗanki shine kika ɗauki fushi da ni kin kira babban ɗanki kina sanar masa kuyi min taron dangi saboda ban isa nace ga yanda za’ai ba”.
Idanu Oum ta ɗan rumtse kaɗan, sai kuma ta buɗe a kansa. Baki ta buɗe kamar zatai magana sai kuma ta fasa saboda ƙwallar da suka cika mata idanu. Ɗauke nasa yay dan yasan yanzu sai ta karya masa zuciya, shi kuma a wannan karon ya ɗauka aniyar tauna tsakuwa dan aya taji tsoro, dolene ya hukunta Ajwaad kodan ya sake sanin muhimmancin Maanal. Bazai yiwu ya samu aurenta a ɓagas ba su kuma bashi ita a ɓagas. Ƙoƙarin barin ɗakin yayi, sai Oum kawai ta saki hawayen da take riƙewa cikin muryar kuka ta ce, “So kuke sai kun kashe min shi hankalinku zai kwanta ko Gadanga, yanzu horon da ƙaninka yay masa kawai bai wadatar a yafe masa ba”.
Murmushi Abah daya tsaya cak tun fara maganarta ya saki a hankali, sai kuma ya maida fuskarsa ya haɗe kafin ya juyo yana kallonta daga inda yake tsayen. “Rafeeq bai hora ɗanki ba, takarar nema sukai yay muku adalci ya sadaukar saboda ƙyaƙyƙyawar zuciyarsa, da kuma nasan zai yi hakan sai na hana masa”.  Ya ƙare maganar yana mai juyawa ya fice abinsa. Wani irin ƙululun abu ne ya sake tokare wuyan Oum, har zuciyarta na tunzurata akan takai Maanal sashen Ajwaad koma miza’ayi ayin mana…….

___________★

Alamun shigowarsa ya sata dakatawa daga kai-kawon da takeyi, zama tai kamar ba ita ba ta nutsu a bakin gadonsa tare da ɗaukar littafin addu’oin sa dake a bed side drawer ta fara karantawa. Da farko Abah daya shigo ransa a ɓace sam bai ganta ba. Sai da ta ɗago ta kallesa cikin tausasa harshe matuƙa ta furta, “Sannu da shigowa”. Sannan ya kalleta. Ciki-ciki ya amsa mata, dan haka ta taso da ƴar sassarfa tana faɗin, “Lafiya kuwa? Naga kamar ranka a ɓace?”. Tsaki yaja mai ƙarfi, sai kuma ya wullar da wayarsa a saman gadon nasa shima yana kaiwa zaune hannunsa akan goshinsa yana murzawa. “Fateema ce ke neman ɓatan rai Kamila”.
Ɓoyayyan murmushi Mamy ta saki, a zahiri kam cike da damuwa ta ce, “A haba kodai baka fahimta bane, amma nasan bazata ɓata maka rai da son ranta ba yallanɓai.”
“Mtsoww!! Bazaki gane ba Kamila, ita dai sam bata gajiya da rikici akan ƴaƴanta, dokar dana kafa jiya akan komawar Maanal sashen Ajwaad shine taketa faman fushi, yanzu naje mata sai da safe na samu ta tasa babban ɗanta gaba tana faɗa masa, shiko yana bada shawarar a haɗani da iyayena.”
Sosai Mamy takai zaune yanzu kam, hannunsa ta kamo cikin nata cike da kulawa. “Kayi haƙuri, zan sameta muyi nagana ta yanda zata fahimta. Dan tabbas Ajwaad ya cancanci a fara horashi kafin a bashi yarinyar nan kodan halaccin iyayenta da basu duba abinda ya faru a baya ba suka sake bashi batare da ko tada magana ba. Taurin kan yaron nan ne yayi yawa, ya kamata ya fahimci ba komai akema taurin kai ba a rayuwa….”
“Abinda nake son ta fahimta kenan ai nima Kamila. Amma tamaƙi ta nutsu ta saurareni, ni kuma so nake mu rabashi da halin kodan bambancin dake a tsakanin jiyansa da yau ɗinsa”.
“Karka damu zata fahimta in sha ALLAHU. Ka bata lokaci ta huce yanzu sai mu haɗu muyi magana. Idan ma ta kama Maanal ɗin ta dawo sashena da zama to, dan in ba hakaba bazai damu ba”
Ɗan jim Abah yayi, sai kuma ya jinjina kansa cike da gamsuwa ya ce, “Kumafa kinzo da shawara Kamila, dan in har Maanal na a sashen Fateema ba’a rabu da bukar bane an haifi habu za’ai. Dan ɗan nata dai can zai koma ya tare abinsa, kinga kuwa bazai damu ba.”
“Tabbas hakan ce zata kasance”. Cewar Mamy wani farin ciki na ratsa mata zuciya na nasara. Abah kuwa da bai san dawan garin ba ya sake furta, “To ai zanyi maganin abun, bari dai ya samu lafiya”.
“ALLAH ya bada iko, ina goyon bayanka kuma ɗari bisa ɗari a wannan gaɓar. Dan in aka biye ta Mamansu haka za’a mika masa ita kaga ya samu damar cigaba da mana abinda yaso tunda ta shagwaɓa shi daga ita har ƴan uwan nasa. Sun nuna masa komai ya nema sai ya samu komai girman sa”.
Sosai kalaman Mamy ke shigar Abah, yana kuma jin gamsuwa da su da tasirinsu ƙwarai da gaske a zuciyarsa fiye da yanda take ma fatan ya fahimta ɗin………✍️

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected