AKIDA TA HAUSA NOVEL BOOK 2
46_47
shiru Yusuf yayi yana kallon Widad, yayin da yaji gaba ɗaya hantar cikinsa ta kaɗa jin abunda Widad ɗin ta faɗa, ta kalleshi tace
“Ya naji kayi shiru ne? Akwai matsala ne?”
girgiza mata kai yayi yace
“A’a babu komai” Widad tace
“Shikenan, ga Abinci can, kaci seka sha magungunanka ka kwanta”
Kasa motsawa yayi daga inda yake, balle ya aikata ɗaya daga cikin abunda tace, sake kallonsa tayi tace “wai ko dai jikin ne?”
Girgiza mata kai yayi yace “A’a jikina ai na warke”
” to ai gani nai duk ka wani koma so silent, shiyasa nayi zaton ko jikin ne, ka tashi zan kwanta ”
Yusuf ya miƙe, ya bata guri ta gyara shimfiɗar ta ta kwanta, yayin da ya koma gefe yayi jugum kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa.
A ƙoƙarinsa na kaucewa zargi daga Widad, ya miƙe ya ɗakko Abincin da niyyar ya fara ci, Amma gaba ɗaya ya ya kasa, tunani burjik a zuciyar sa, ga labarin da Saleh ya gaya masa, ga kuma itama abunda ta faɗa masa yanzu, ashe dai da daru a gaba, ko wane irin hukunci zata yi masa idan ta gano shi jami’in sirrine? Gashi zuciyarsa ta riga ta gama kamuwa da tsananin ƙaunar Widad, yana matuƙar jin sonta a ransa, a yanzu haka dama yana ɗar ɗar, saboda yasan bashi da tabbacin idan suka koma gida Widad ta cigaba da zama da Auren sa, dukda a yanzu yana ƙoƙarinya jarraba Widad yaga ko tana son shi, a ƙaddara ma ta yadda da Auren, su cigaba da zama tare, waye yasan Aure suka yi, Saleh ne kawai sheda ta yaya zasu fuskanci mutane suyi musu bayanin wannan rikita rikita?.
Nan da nan wani irin gumi ya shiga tsasttsafowa Yusuf, lallai akwai ƙura a gaba, kasa cin Abincin yayi, dama gashi bakinsa babu ɗanɗano saboda zazzaɓi, dan haka ya ajiye Abincin a gefe ya nemi guri ya kwanta, sedai kamar yadda beyi tsammani ba, bacci ya ƙauracewa idonsa se tunani, yanzu meye mafita? Ta ina ze tunkari Widad yayi mata bayanin waye shi, dan kamata yayi ace shi ya gaya mata ba wani ba.
Haka nan jiki a sanyaye ya cigaba da tunani, ya daɗe a zaune ba tare da ya kwanta ba, yana ta saƙawa yana warwarewa.
Muryar Widad yaji tace “Tunanin Meka ke hakane wai?”
Da sauri ya dawo daga tunanin da yake yace “Babu komai karki damu”
“Ko kana tunanin gidane, da Ummanka?”
Murmushin dole ya ƙaƙalo yace “A’a”
“Nasani dole zakayi tunanin gida, nasan baka jin daɗin zaman garin nan, ko baka faɗa ba zaman garin nan ba daɗi, Amma ni ta wani ɓangaren rahama ne a gare ni, bana fargaba ko tashin hankali saboda maƙiyana, ina matuƙar jin daɗin karamcin da mutanen gidan nan suke min, dukda yadda zaman garin ke bani wahala, amma karamcin su da goyon bayanka na ƙara bani ƙwarin gwiwa, tabbas duk wani motsi da zanyi ina tunanin Daddy, ina tunanin wani hali yake ciki, me yake yi? Nasan ina ransa, sedai ina masa Addu’a zuwa lokacin da Allah ze kawo ƙarshen wannan abun in koma gida, kaima kayi haƙuri nasan duk nice silar shigar ka wannan halin”
Ta ƙarasa maganar cikin damuwa. Yusuf yace “bana dana sanin kasancewa ta dake anan, saboda karamcin mahaifinki da yadda da yayi dani beci ace na bar ‘yarsa ɗaya tilo ta shiga wani hali in kasa temaka mata ba, sedai dole inyi kewar Ummana, bata da kowa seni, mahaifina ya rasu, gata marainiya ni kaɗai ne a kusa da ita muke rayuwar mu tare, Allah kaɗai yasan irin damuwar da take ciki, dan tunda na tashi ban taɓa nesa da ita ba, nasan tana cikin damuwa ”
Cikin tausayawa Widad tace
“Allah sarki, dole zukatan makusantan mu su shiga damuwa, har gara kai wataƙila bayan mamanka akwai wanda zasu damu da halin da kake ciki na ɓatan da kayi, nikam daga Daddy na se Bulama nasan sukaɗai zasu damu, duk wanda yake tare dani, yana tare dani ne dan wannan dukiyar, nasan da babu ita da bazasu nunamin so ba, kuma nasan zagina suke a bayan idona, shiyasa nake wa mutane wani kallo na daban, a da na zata duk mutane miyagu ne, kuma talakawa zasu iya komai akan kuɗi basu da kirki, sedai wani darasi da nayi shine, shi rashin kirki ba’a talaka ne ko me kuɗi ba, a mutum ne kawai, na samu misali akanka da kuma mutanen ƙauyen nan, basu san koni wace ba, amma suna ta kyautatamin”
Yusuf yace “hakane kam, naga kin sake dasu sosai kamar bake ba, kamar ba kece me wannan AƘIDAR ta ƙin mutane ba, me yiwa mutane kallon miyagu ba”
“Hmm ina da dalilin yin hakan, ka kwanta dare ya fara yi, kaga baka da lafiya akwai buƙatar ka samu isashen bacci”
Yusuf yace “Hakane, kema ki kwanta my queen”
‘ba zaka dena faɗar wannan sunan bako? ”
“Dama bakya son sunan ne? ”
“ban sani ba, ai kasan nace maka bana so”
Yusuf yace “ni gaskiya daɗin sunan nake ji, My Queen, My life, I love you so much My dearest Queen”
Tsaki tayi, ta canza position ɗin da take kwance ta toshe kunne ta, wai danma karta cigaba da jin meze ce”
Yusuf yayi murmushi, ya kwanta sedai fa bacci yaƙi yuwuwa, saboda saƙawa da warwarewa da yayi tayi, akan ya sanar da Widad gaskiya waye shi, kokuma karya gaya mata?
“Barrister Hafiz, kuyi duba a cikin lamarin nan da kyau, ku tsananta tunani kafin yanke hukunci, akwai gwagwaɓar riba da zaku samu idan akayi wannan harƙallar daku, zaku samu alheri fiye da tunaninku, zaku samu arziƙin da baku samu a harkar aiki bama”
Barrister Hafiz ya gyara zama yace “Abunda nake so ku fahimta anan shine, wannan aikin fa hatsari ne dashi, mu sa hannu a siyar da kadarorin Daula, karkuyi mamaki akwai masu bibiyar al’amuran dukiyarsa bamu sani ba, idan abu yazo ya tonu sunanmu ze ɓaci, kuma mu rasa aikin mu, sannan mu fuskanci fushin hukuma”
Alhaji Musa yace “Barrister, sha’anin ƙasar nan tamu yanzu kowa mafita yake nemawa kansa, da kayi ƙaramin laifi a kaika prison a banza, gara kayi gagarumi wanda zaka samu mafita a al’amuranka, kuɗi zaka samu manya ba ƙanana ba, wanda baku taɓa zaton samu ba, kuma a yanzu waye yasan inda Daula yake? Idan abubuwan nan suka samu zaku iya barin ƙasar ma gaba ɗaya, dan haka ku san dabarun da zakuyi, kuyi mana wata takarda da zata nuna yayi holan wasu daga kadarorinsa, a bisa farashi me sauƙi “.
Ya kice gumi Barrister Hafiz yayi yace” Yallaɓai akwai buƙatar a ɗan bamu lokaci, zamuyi shawara tukuna ”
“Shikenan, amma bama buƙatar a ɓata dogon lokaci, muna sauraren ku”
“Shikenan yallaɓai, sekun jimu”
Hajiya Sarah ce zaune gefen Bulama, yana shan tea yana karanta jarida, tace
“Yallaɓai, dan Allah ka tausayawa Hajiya Halima, kasa baki a sakar mata ɗanta, gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, hankalin ta gaba ɗaya baya jikinta saboda damuwa”
Bulama ya nisa yace “banƙi ta taki ba, amma baki fini son Halima ba, da ina da yadda zanyi da zanyi ƙoƙari in saka a fitar da shi, amma wannan case ɗin ba ƙarami bane, idan na matsa sunana ze iya ɓaci”
“Hakane amma ya kamata kayi wani abu, koda ta ɓangaren kwantar mata da hankali ne, Allah kaɗai yasan halin da take ciki, ba ƙaramin abu bane uwa ta iya jure ɗanta a wani yanayi, idan ka bincika babu lallai ko Abincin kirki tana iya ci”
“Eh to banƙi zancen ki ba, amma Halima mace ce me taurin kai da rashin haƙuri, maimakon tayi haƙuri a bi komai a hankali, amma se azalzala ta take, irin wannan lamarin a hankali ake binsa, amma ita ta fiye garaje, case ɗin nan ba ƙaramin case bane ba, karki manta Daula ne fa aka nema aka rasa, kuma shine yake kula dashi, gaba ɗaya ana saurarar hukuma aji me zasu ce, Amma insha Allah ze fita “