HUKUNCIN ALLAH BY GARKUWA

HUKUNCIN ALLAH HAUSA NOVEL BY GARKUWA

Bismillahirahamanirahim

*1:48 pm Monday 10 February*

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.

 

We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors

 

We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.

 

AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ?auke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.

 

Mun samar da littattafan hausa na nau’uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.

*”Alhamdulillah na godewa Allah daya bani rai da Lafiya da nitsuwa da konciyar hankali da damar fara wannan littafin nawa Lafiya, ya Allah ina tawassali da kyawawan sunayenka Allah ka bani ikon rubuta alkhairi da abinda zai amfanar da al’ummar musulmi Allah ka tsaremin Al’k’alami na da rubuta sherri, Allah ka kawarmin da Yatsuna da tunani na da idona akan rubuta abinda zai zamo guba ga Al’umar Annabi, ya Allah ka tsareni daga sharrin mutun da Aljani Amin Amin Ameeeeeeeeen ya rabbil izzati.”*

 

*K’warai-K’warai na gane duniya mai sonka shikeyi maka hiddima, tabbas wannan haka yake masoya na naga zahiri ashe dai nidin ce kuke so ni Aysha Aliyu Garkuwar kuke so ba novels na ba, domin da novels nane a zaman da nayi ina hutawar nan da kun mance dani sai gashi wallahi abun mamaki kunfi nunamin kulawa a yanzu fiye da in ina typing Ana kyawun tare masoya na dan nida ku ba mugun tare akeba a,a kyawun tare muke shiyasa gani gareku da wani sabon salon tukuicin ku, sai dai fa ga shawara gareku Reeders duk mai son karanta littafin nan to ta/ya Tarawa kanta/kanshi dan in nayi koda 5 page ba wacce zan Turawa ta Prvt chart*

 

 

 

*Z*ahra! Zahara!, sauri ya k’arayi ganin duk kiran da yake mata bata jinshi, dan ta daddage sai rawa takeyi d’an guntun siket d’in dake k’ugunta sai bud’uwa yake, wanda yafi dacewa da a kirashi da sunan tayani tsalle sai ‘yar rigarta wacce tayi cib da jikinta kanta a kitse an tubke cukun a tsakiyar kanta amman duk kitson ya tuttujare dan tsufa da yayi.

Sai sautin wak’ar nan mai taken,
Zahra-Zahra kece tauraruwa zahra-zahra kekkyawa kina da kyawu,
na sura,
dake tashi da kind’in daya cika illahirin unk’uwar,
Matasan kuma da ke zaune a bakin d’an Shagon charging sai dariya suke ganin yadda Zahra keta rawa sunata mik’a mata sweet tare dayi mata tafi.

Sauri sosai Yusuf ya keyi har kamar zaiyi tuntub’e yana isa wurin,
ita kuwa tana juyowa ganin yadda ya nufota haik’an k’adaran yasa ta faraja da baya-baya tare da rumtse idanun ta tana sauraron ta ina mari zai sauk’a a fuskarta,
shiko yana isa gareta yatsunshi biyu yasa ya kamo kunnenta ya matse da k’arfi sannan ya juya ya nufi bakin get d’in shiga gidan su da ita,
itako tuni ta saki k’ara tare da yarfa hannu tana kiran.
“Aunty na! Aunty na! Hamma Yucuf a cire min kunne na”.
shiko janta yakeyi da iya k’arfin shi dan yana jin zafin yadda k’arfi da yaji ake sake Zahra take abunda ranta keso yarin k’arama amman duk wata rawa ta iya ga bibiko ita ko yaushe tana cikin maza sannan in an gayawa Aunty bata daukan abun da mahimmanci.

A haka suka shiga cikin gidan kai tsaye parlour Auntyn ya nufa da ita,
yayinda Mama kuma ke binsu a baya tana.
“Kai Yusuf sake mata kunne zaka jawo mata ciwon kunne fa.”
Shiru yayi har suka shiga parlour inda Aunty take zaune tana jinsu,
suna shiga tace kai.
“wallahi kai dai Yusuf ka sawa Zahra ido,
ai yarinta ce kowa da irin tasa,
ka bar ‘yarinya ta huta, in ta girma ai zata bari.”

Turata yayi kan kujera sannan ya wuce bedroom yana zuwa durowa ya bud’e wurin kayan ta yasa hannu ya jawo d’an hijabinta, sannan ya fito parlour yana zuwa ya zura mata hijabin sannan ya kalleta cikin tsuke fuska da zaro ido yace.
“Maza b’acemin da gani yanzu d’auki Allonki ki tafi bappa jangird’e in kuma na fito na sameki a wurin Idi mai charge kina rawa sai na karya miki k’afa inga dame zakiyi rawan.”
Simi-simi ta fice tana ruggume da Allon nata,
tana fita kamar kullum yadda ta saba in zata tsallaka titin k’ofar gidan nasu sai ta jawo rigarta ta rufe fuskarta sannan ta tsalla ka,
ita in ana duba hanya kafin a tsallaka to ita sai ta rufe fuskarta kuma hon d’in mota ko keke napep baya sata ta bud’e ido bare ta kauce musu,
a hakan cikin sa’a ta samu ta tsallaka ta wuce makarantar Allon nasu.

Tana zuwa ta shiga cikin taron yaran ta zauna sannan ta fara juye-juye tana wani kakkane ido alamar neman rigima aiko tayi tozaki da Amira yar malamin allon nasu
ido ta tsura mata tare da yamutsa fuska ta kuma kalli k’afar Amiran dake da gyambo ga k’udaje sun cika kan ciwon,
yawu ta tsirtar cikin harara da tsiwa tace.
“ke Amira ki rufe ciwonki ni bana son gani.”
itama Amira a tsiwace tace.
“bazan rufeba ciwonki ko ciwona.”
ganin suna surutu ne yasa bappa jangirden yayi musu tsawa tare da cewa.
“NJange-NJange, be! sini! mimarra! alifi! lallamu! hasakeri!”.
sannan ya d’ago bulalan hannunshi tare da juyata kan taron d’aliban nashi,
lokaci d’aya wurin rud’e da karatun yara da ‘yan mata da ‘yan samarin,
rud’eqar wurin yasa Amira ta d’an matso jikin Zahra har ta d’an goga mata gyambon k’afarta a jikin Zahran,
Itako Zahra tana jin ciwon ya gogeta ta kalli Amira cikin tsiwa ta zaro takalmin robar dake k’afarta sannan ta daddage da iya k’arfinta ta zuba mata takalmin a kan gyambon har saida k’udajen dake kan gyambon suka mace tare da narkewa a cikin ciwon,
wani irin sanda rewa Amira tayi tare da mimmik’ewa ta cillara k’ara mai cike da azaba,
cikin tsoro Bappa jangirde yayi kansu dan duba me ya samu d’iyar tasa,
itako Zahra tana ganin yayi kansu ta mik’e tare da cilla allonta gefe ta cire d’aya takalmin dake k’afarta sannan ta arce a saba’in ta nufu gidan su.

A gidan kuwa tana fita Yusuf ya kalli Antyn cikin yin magana Kai tsaye yace.
“Anty sufa yara amanace ga iyayensu kuma abun kiyayewa ne,
fisabilillahi ya za’ayi ace,
komai Zahra tayi ke bata laifi a gareki,
kullum ita tana cikin maza,
sam bakya kula da suwaye take mak’alewa,
in anyi magana sai kice yarinta ce,
to wallahi in bata nitsuba bazan dena sa mata idoba”.
yana fad’in haka ya fice ya haura sama inda d’akinsu yake,
sauri-sauri ya cire uniform nashi dan yaji an fara kiran sallan la’asar a masallacin k’ofar gidan nasu,
A parlour Anty kuwa yana fita,
Mama ta kalli Antyn cikin nitsuwa tace.
“Antyn yara ke kinaga zancen Yusuf shirme ne ko?
to wallahi gaskiya yake gaya miki,
domin kuwa Allah ya kawomu wani zamanin da idan kayi sakaci da lura da yaranka to tun suna k’anana wani gardin banza zai lalata miki ‘ya sannan ya rabata da budurcin ta da nitsuwarta
tabbas iyaye sai an sanya lura a kan yara dole kisan shige da ficen ‘yarki ko d’anki. ”
murmushi tayi tare da cewa.
“Kai Mama insha Allahu ba komai Allah zai tsare mana su.”
Ficewa Mama tayi ganin bazata fahimci abinda ake guje mataba.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected