YAR ZAMAN WANKA BOOK 1 COMPLETE HAUSA NOVEL
ƳAR ZAMAN WANKA
(KWANA ARBA’IN)
NA
MAMAN AFRAH
FCW
️1️⃣
Gabaɗaya ta jibge kayan cikin wardrobe ɗinta a kan gado, sai zuba wa take a cikin wata babbar bakkon kai da gani tamkar ƙaura za ta yi, sai da ta kwashi son ranta ta maida sauran. Akwatin ƙarfe ta ɗakko irin tasu ta mutanen da, kayanta ne na fita unguwa ƴan atamfofinta sabbi. Sai zuba kayan take tana ta faman murmushi gabaɗaya wani irin daɗi take ji a ranta
“Yau sai kwanan binni” Inna Azimi ta faɗa tana ƙoƙarin zige zip ɗin bakkon nata, hango sallayarta ya sanya ta dakata da zige zip ɗin ta ɗakko abin sallar tana cewa
“Kar in je in ke cewa a bani abin sallah dan ni bana son yin sallah sai a kan sallaya ta bare ma su yara da kunya kake bani-bani in da abinka kwa sai dai a ga ka ɗakko” Ta ce tana sanya sallayar ta dannata daƙer ta samu ta shiga saboda cika da bakkon ta yi.
Wanka ta shiga abin ta, tana ta sauri ta fito, kallon ɗakin kishiyarta ta yi ta yatsina fuska a ranta ta ce
” Humm ba zan faɗa miki ba jikata na naƙuda, ba sai dai ki ganni da kayana zan tafi birni in yaso baƙinciki ya kasheki, tun da ke baki da dangi a birni” Ta faɗa har da wani gatsine kamar wata ƙaramar yarinya.Ɗakinta ta shiga sai da ta shafa mai tsaf, ta sanya kwalli sai wani kallon ƙaramin mudubi take tana wani gyagygyara fuska tamkar wata ƴar budurwa. Sai da ta gama tsaf ta ɗakko atamfarta batik a linke a kan gado daman takanas ta fitar da ita saboda ta sanya idan za ta tafi.
Sanyawa ta yi a jikinta ta ɗakko ɗankwalinta irin na tsaffin nan ɗan kantu mai santsi ta ɗaura har da yi gwaggwaro a gaban goshi, ƙasan gado ta sunkuya ta ɗakko takalminta ɗan madina domin shi ne wanda take sanyawa in za ta gidan biki dan shi ne na ganin sarki, ta fiddo shi ƙofar ɗaki ta ajiye, ta ɗauki silifas ɗinta wanda ta cire duk ya wani tsufa ya katale, ta shiga da shi ɗakin ta sanya a ƙasan gado, madarar turarenta ta ɗakko ta shafa abinta, sai ta kwalbar turaren a ƙaramin aljihun bakkon tana cewa.
“Wannan sai ranar suna kuma zan shaga abuna, yo a kan me zan ke wari ranar suna a raina min hankali ganin daga ƙauye nake” Ta faɗa tana taɓe baki.
Sauran goranta ta ɗauko ta ɓantala tana ci ta ƙulle sauran ta saka a ƙaramar jakarta ƴar pos wacce jikarta Sadiya ta bata.
“Yauwa na gama komai bari in je in tambayo Malam, dan ma kar ya ji ya wai dan wallahi tafiya babu fashi” Ta faɗa tana fitowa ta nufi turakar mijin nasu da ke can wajen hanyar zauren gidan.
Kai da tsaye ta danna kai turakar Malam tana mai cewa
“Gafaranmu dai”
“Allah mana gafara” Cewar Malam yana kallonta mamaki bisa fuskarsa ganinta da shirin fita dan ya san biki ma sai na wanda yake da kusanci da ita take saka atamfofinta na adakar ƙarfe, hakan na nufin biki za ta ko sanar masa bata yi b ya faɗa a ransa.
Inna Azumi kwa sai da ta gama shigowa ɗakin ta lura da Tasalla da ke zaune a ɗakin sai lokacin ma ta tuna Tasallar ce da girki.
Wani kallo ta yiwa Tasallar ta ce
“Umm in ji mai ciwon haƙori” Ta faɗa tana samun wuri ta zauna. Shi dai Malam har lokacin kallonta yake da mamaki, sai da ta zauna ta ce.
“Sannu Malam” Kallonta ya yi tare da gimtse fuska sannan ya ce
“Yawwa sai ina, dan na san dai zancen gizo bai wuce na ƙoƙi tun da na ganki da shirin fita”
“Haba Malam, dama magana ce nake so mu yi” Ta faɗa tana kallon Tasalla dan so take Malam ya ce Tasalla ta fita dan bata so Tasallar ta san da tafiyar tafi so sai ta fiddo jakarta ta mata bazata.
“Ki faɗi abin da ya kawo ki” Cewar Malam yana kallonta har lokacin babu fara’a a fuskarsa.
Washe haƙuranta ta yi wanda har lokacin da ɗan sauran goron da ta tauna a bakin ta ce
“Dama Halima ce ƴar wajen wannan yaro zan je yiwa zaman wanka sai…
“Zaman wanka kuma Yaushe Halimar ta haihu da har za ki tafi zaman wanka ko faɗa min baki yi ba sai da kika shirya? Shin ma me za ki je ki yi da girmanki da komai?” Malam ya faɗa rai ɓace dan abin ya bashi mamaki bai zaci ma garin za ta bari ba duj tunanisa biki ne za ta je a cikin garin ko wani ƙauyen da ke maƙotaka da su.
Tasalla da farko wani haushi ta ji jin kishiyarta za ta tafi birni, dan duk da sun tsufa amma kishin nan yana nan sabo dal a zukatansu. Amma ganin Malam ɗin ya haƙiƙice sai ta faki idonsa ta yiwa Inna Azumi gwalo.
Inna Azumi wani ƙululun baƙinciki ne ya tokareta ganin kishiyarta tana mata gwalo har da ƙunshe dariya.
“In kin san wata baki san wata ba wallahi sai na yi kissar da sai ya barni na tafi, shegiya ƴar baƙimciki da bata da kowa a birni bare tasa rai wataran za ta je ta sha miyar ɗanyen kaya (jar miya).
“Bata haihu ba fa fama…
“Ban gane bata haihu ba wato shi zaman wankan ma tun kan a haihu ake zuwa yinsa?” Malam ya katse ta da tambaya cikin nuna tsantsar mamaki a fuskarsa.
“Yau za ta haihu”
“Ikon Allah wato dai har ɗan adam ya san ranar da wani zai haihu in ce dai wannan ilimin ubangiji ne, ko su turawan da suka fito da yin hoton ciki (Scanning) Dan a san watanninsa da ranar haihuwar ai ko sun faɗi ranar ba a ita ake haihuwa ba ko dai mace ta rage kwanankin ko kuma ta haura ma amma ke har kin ware ranar da za ta haihu, wallahi Azumi ki fita idona ba na son fitina” Malam ya faɗa yana nunata da yatsansa.
Sosai abin ya yiwa Tasalla daɗi, sai ƙunshe dariya taje tana yiwa Azumi kallon ƙasan ido, wannan abu shi ya ƙara ɓatawa Azumi rai sosai take jin kamar ta fashe da kuka.
“Haba Malam ai ka bari na mutu kafin ka binne ni” Cewar Azumi a ɗan fusace.
“To uwata yi min faɗa ko ki haɗa da duka tun da ke ce mai gidan, kuma ma da kin san ke ce mai gidan ai da baki zo nan neman izini ba da sai ki yi tafiyarki” Malam ya faɗa yana gyara zamansa ya lanƙwashe ƙafafunsa wanda suke a miƙe.
Sai sannan Azumi ta gane katoɓarar da ta yi aikuwa da sauri ta ɗan karyar da kai tare da sanyaya murya ta ce
“Haba Malamin Malamai, Malamin da ƙauye da rigagen yankin nan ke ji da shi suna alfahri da shi, ni na isa in ja da Malamin da kowa ke girmama shi saboda ilimi da ɗaukakar da Allah ya masa”
Aikuwa Azumi ta harbo jirgi tuni Malam ya washe jajayen haƙoransa, cikin jin daɗi ya ce
“To ai ke ɗin ce Azumi sai kike abu kamar dai ke ce sama da ni amma ai sai ki yi bayani tin farko”
Tasalla wani irin takaici ne ya mamaye dukkan zuciyarta dan bata so Malam ɗin ya sakko ba ta so ayi ta gumurzu, har ayi faɗan da Malam ɗin zai hana zuwa birnin duk da ta san har yanzu bata ji an yi haihuwar ba, ta san kawai riɗin abincin birni ne ya sa ta zazzoɗin son tafiya.
Wani kallo mai haɗe da hara Inna Azumin ta yiwa Tasalla kafin ta juya wajen Malam ɗin ta yi murmushin jin faɗi ta ce.
“Wallahi dama ɗazu ne na kira lambar Babar Halimar dan in ji ya suke, to shi ne fa na ji tana ta sheshshekar kuka tana cewa “Inna ki taho idan da hali muna asibiti an kawo Sa’adiyya tana naƙuda idan ya so sai ki nemo izini agun Malam ki mata zaman wanka, kin san dai bata da wata kakar da za ta mata zaman wanka sai ke kaɗai a duniya” Inna Azumi ta faɗi maganad tana share ƙwallar ƙaryar da ta mammatso daga idanun nata.
“Wato da gasken dai bata haihun ba?”
“Haba Malam wai ya kake maida hannun agogo baya ne, na faɗa maka naƙudar take amma kaƙi yarda sai wasu tambayoyi kake min mau kamar tuhuma, ko dan ka ga yarinyar ba jikar ka bace, amma tabbas ka zama mai manta alheri lokacin yaron nan na da rai haka zai kwaso goma ta arziƙi ya zo ya gaisheka duk da ba kai ka haifesa ba amma shi ne yanzu dan ƴarsa za ta haihu zan je zaman wanka kake nuna mata wariyar launin fata?” Ka san dai shi kaɗai na haifa a duniya, shi ma su biyu ya haifa daga ita sai ƙanwarta, kuma wannan ne karo na farko da jikata za ta haihu amma kana ta yalbatsani a gaban kishiya salon wataran a min gori” Ta ce tana fashewa da kukan makirci har da su fatar majina ita ala dole ta tuno da ɗan mata da ya mutu.

