Ajiya A Duhu BOOK 1 Na Billyn Abdul

Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 75

????7??5??

______________

Assalamu alaekum,Yan uwa barka da wannan lokaci, inde Kaya kikeso unigue Wanda bazakigannsu ajikin kowaba se yangayu toh kishiga group din mom safwan Muna turakaya ko Ina cikin amincin Allah Muna seda lace, atampa,shadda,voil,beil,sarka,kayan yara,takalmi ,jaka ,kayan yara, kayan kitchen,Kae mufa komae daruwankane Allah y bamu kasuwa me albarka nagode

Ga inda zamu iya samun mu .

09064820534.

Ga kuma link na group ?in mu.

https://chat.whatsapp.com/CuYcnxM1Z7VCYL5tqnyuL7

_____________

………Daddy shine ya lalla?a Maanal da su Shahidah fitowa wajen ba?in Giro. Gwaggo kakarsu, sai Babu mahaifinsu, sai Malam A?ilu ?ani ga Baba Haruna. Wanda bayan barowar su Ammie Giro ya aure gwaggo.
Zama kawai su Maanal sukai batare da sun kalla kowa ba balle gaishesu. Sai da Daddy yay musu magana sannan suka gaishesu ciki-ciki, dan Maanal ma kam bakin kawai ta motsa. Baabu ne kawai ya amsa cike da zumu?i idanunsa cike da ?walla yana kallon ?a?an nasa, farin cikin rayuwarsa. Ita kanta Ammie ?in satar kallonta yake. Zuciyarsa na matu?ar rawa da ganin ?unbin canjawar da tayi. Canjawar da a yanzu idan yace ya ta?a aurenta wani sai ya gallara masa maruka kafin ya ?aryatashi. Dan shi duk ya rame ya lalace tsufa ya taso masa saboda ciwo. Ga zaman ?auye da canjin rayuwa tamkar bai ta?a zama aji ba a rayuwarsa, ga fitinar yara guda biyu da ALLAH ya bashi tare da Sailu amaryarsa. ?ansa namiji shalele ya zama fitinanne a garin Giro da kewaye, sai mace dake bimasa itama dai marabarta ka?an da namijin..
Daddy ne ya katse shirun da gyaran murya. Kafin ya ?aura da sallama. Duk suka amsa. Cigaba yay da fa?in, “Alhamdullahi da kasancewar mu anan, kafin komai zan fara da nasiha a garemu baki ?aya musamman akan ku yarana. Ina ro?on ku kuyi ha?uri da koma minene zukatanku suke tunawa da suka faru a baya. Ba’a fushi da iyaye, ba kuma a ?in su sai idan akan abinda zai zama sa?on ALLAH ne. Koma minene ya faru ya rigada ya farun ya wuce. To a barsa a ya wuce ?in a tari gaba. Yau ga mahaifinku sunzo garemu da muhimmiyar magana kamar yanda suka fa?a, sai dai dama bamu kai ga tattaunata ba ALLAH ya kawo ku. Dama a nawa shirin shine na bu?aci ganinku a gobe idan ALLAH ya kaimu, sai kuma komai ya sau?a?a.” Sake maida hankalinsa yay ga su Babu, fuskarsa da murmushi ya cigaba da fa?in, “Inaga tunda ALLAH ya sau?a?a gasu sunzo kafin ma mu nemesu ya kamata mu tattauna ko”.
“Hakane”. Cewar Kawu A?ilu yana gyara zama. Sai kuma cikin dakiyar murya ya cigaba da fa?in, “Kamar yanda ka fa?a abinda ya faru ya riga ya wuce hakane Alhaji, dan haka maganar tuna baya da anyi kaza ko anyi kaza babu zancen maimaita shi ko tada shi. Dama munzo nan ne akan batun ita Maanal, wanda yake neman aurenta yaje garemu a satin daya gabata kuma mun bashi. Saboda dalilan ganin shi ?in mutumin kirki ne da muke da tabbacin zai ri?eta da mutunci kamar yanda muka samu sauran ?an uwanta a mutuncinsu…….”
Cikin mamaki da ru?ani Ammie da Nene da su Maanal duk suka kallesa. Yayinda Daddy ya kasa jurewa shima dan shi zatonsa ha?uri suka zo basu da neman yafiyar su Ammien akan abinda suka aikata musu a baya, ashe wata fitinar ce suka zo da ita kuma. “Me neman aurenta kuma? Wanene shi haka da mu anan bamu sanshi ba?”. Cewar Daddy da mamaki.
Wani irin ?aure fuska gwaggo tayi, Babu zai yi magana ta hararesa. Cike da isa ta ce, “Sunansa Alhaji Bukar. Sanata ne babba a ?asar nan, kuma mun bashi, munzo nan ne ma saboda mu tabbatar muku mun bashin sannan mu wuce da ita can Giro dan nan da sati biyu za’ayi biki kamar yanda ya bu?ata”.
Tuni zufa ta gama wanke Daddy, ya dai daure da ?yar ya maida dubansa ga Maanal da take ma su gwaggo wani irin shegen kallo, sai dai uffan batace ba. “Manaal” Daddy ya kirayi sunanta a hankali. Juyawa tai tana amsa masa.
“Waye kuma Alhaji Bukar?”.
“Daddy ban sanshi ba nikam, bana kuma bu?atar saninsa. Sai dai ina ro?onka cike da girmamawa ka fa?ama wa?an nan mutanen su bar mana gida su koma inda suka fito. Idan ba hakaba wlhy wlhy wlhy sai na kawo musu human right.” sai kuma ta mi?e a hankali tana duban gwaggo da wani irin ?as?antaccen kallo. “Ke kuma idan kina bu?atar mutuncin furfurar kanki kiyi gaggawa tarkata komatsanki ku kama gabanku. Ashe kina da baki ko ido da kwallin kwaso wa?an nan ?azaman ?afafun naki zuwa garemu? Kin manta mu ba jininki bane? Kin manta a yawon tazubar uwarmu ta samo mu? Kin manta bazaku ha?a zuri’arku da lallatacciya mai ?auke da cikin shege ba? Kin manta… Kin manta…. Da yawa. To karki yarda ki bari na tuna miki, dan tunawar na nufin shiga ukun ki, tun kina iya banbance su waye a gabanki ki koma inda kuka fito. Inba haka ba kuwa…..” ta saki wani murmushin da jinjina kanta tai wicewarta da karka?a ma gwaggo yatsa na tabbatarwa.
Harga ALLAH gwaggo ta matu?ar tsorata da yanayin Maanal. Eh tasan dama yarinyar tun tana ?aramarta fitsararriya ce, amma bata san rashin kunyar tata har ya kai haka ba. Da ?yar ta iya ?arfafa zuciyarta ta maida dubanta akan Ammie. “Asiya ni ?arki kema wannan ?ibar albarkar a gabanki kina jinta”.
Murmushi sosai Ammie tayi, kafin a karo na farko ta sanya idanunta a cikin na gwaggo. “Mi kuke son nace da ita Talle….”
“Talle?! Asiya ni kike kira da Talle?”. Gwaggo ta fa?a a zabure tana katse Ammie. Murmushin Ammien ta sake sakin mata, sai kuma ta ?an la?e baki, “Shi nasan sunanki, tunda shi na tashi nasan ana fa?a miki. Tabbas kamar yanda Maanal ta fa?a kuyi gaggawar barin gidan nan tunda mutuncinku, dan wlhy bazan hanata ?aukar dukkan matakin datai niyya ba ita da ?an uwanta. Tun farko ma da nasan abinda ya kawoku gidan nan kenan da bazaku ko zauna ba balle shigowa nan. Amma kunci arzi?in mahaifina ya fito ne daga ku, hakama mijin aurena daya ce na saurarenku, dan shi tuwo dai tuwo ne ba’a canja masa suna. Amma wa?an nan yaran baku da wani hurumi akansu, dan da bakinki kin tabbatar ma da duniya ba jinin ?anki bane ba. Shima kuma ya tabbatar da hakan, idan duk kun manta maza kuje ku sake sabon tunani dan tuna hakan zai matu?ar taimaka muku. Idan kuma na sake ganin ?afar ?ayanku a cikin gidan mijina na rantse da ALLAH sai kunyi dana sani da nadamar sani na. Yarinyata kuma nada mijin aure, kai koda bata da shi gara na jerata naita kallo matsayin kayan adon ?aki da ace kune kuka za?a mata mijin aure……..”
“Asia!”.
Daddy ya kirayi sunanta a hankali yana mai ri?o hannunta, ?o?arin fisgewa Ammie tayi idanunta na cikowa da hawaye, dan gaba ?aya neman birkice musu take yi kamar ba Ammie Sarkin ha?uri ba, dole ya mi?e tare da jawota jikinsa kawai ya rungume. Murmushi Nene da ko a bata furta ba ta saki, hakama Shahidah da Amaal sai suka mi?e suna wata ?ar dariyar sha?iyanci. Dan su kam ai ba sai sun ce komai ba, Auta ta gama komai ita da Ammie. Babu kam rawa jikinsa ya fara yi, da sauri ya du?ar da kansa ?asa hawaye na cika masa ido. Yayinda gwaggo ta gama macewa a zaune ita da Kawu A?ilu. Oho ko’a jikin Daddy, dama yayi hakan ne da gayya duk da sai da ya ya?i kansa matu?a saboda kunyar Nene. Kusan minti ?aya tana a jikinsa kafin ya cirota a hankali ya zaunar da ita shima ya zauna a kusa da ita. Kallon su gwaggo yay babu ko kunyarsu ta sisi.
“Ina fatan basai mun cigaba da wata jayayya ba. Amma ni zan baku ha?uri, in sha ALLAHU kuma zamu zo gareku domin auren ita Maanal, dan kamar yanda mahaifiyarta ta sanar muku tana da mijin aurenta a hannu.”
Wani irin mi?ewa Kawu A?ilu yay a fusace yana kallon Daddy, “Alhaji munzo nan ne domin mutuntaka. Dan haka kada ka zubar da wannan darajar, kar kuma ka biyema she?aniyar can Asiya dan zamu iya yin komai a wannan karon kan yaran nan”.
Murmushi kawai Ammie tayi, hakama Daddy. Sai Nene ce a wannan karon ta furta, “To kudai yi a hankali”.
Harararta Kawu A?ilu yayi, hakama gwaggo. Babu kam da har yanzu kansa ke’a ?asa sai ya share hawaye. Cikin sanyin murya ya ce, “Gwaggo dama na ce muku abinda ake shirin yi kuskure ne, sannan mutumin nan wlhy bai dace da Maanal ba. Kada ku?i su rufe muku idanu ku…..”
“Rufe min baki shashasha kawai sallamamme, an?i a bari ?in, mu da su kuma mu zuba ?an halak ka fasa. Dalla tashi mu wuce”.
Komai Babu bai sake cewa ba ya mi?e. Haka suka fice yana waiwayen Ammie data ?auke kanta gefe……

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected