Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 95
????9??5??
______________
………Zaman wannan meeting na Kano ya matu?ar saka Mamy a farin ciki. Yayinda Oum da Babban Yaya ke cikin damuwa da zaman neman mafita. Abah da Yaya Fawzan kuwa sun mugun ?ullatar AA. Shiko tunda suka dawo Abuja yay bala’in maida kansa busy. Sam baya zaman gida, yakan fita da safe sosai, sai ya kai goma kuma bai koma gidan ba. Sam ya?i bada wani space da Oum zatai zaman yin magana da shi balle su Babban Yaya. A kamfani ma ya toshe duk wata hanya da zata ha?a shi da Maanal. Itama kuma a nata ?angaren haka ne. Duk hanyar da zata ha?ata da AA ta toshe ta. A wannan halin aka shiga shirin bikin ?addamar da agogonsu. Taro na farko kuma kenan da kamfani zai yi Maanal na nan. Ita da RK normal ne, dan tuni shima ya dawo Abujan, amma ya ?auke ?afarsa da zuwa gidan su AA gaba ?aya. Hasali ma tunda ya dawo babu wanda zaice ya ganshi a cikinsu. Ga Abah ya kafama Oum takunkumi akan cewa RK ?in komai. Dan shi yana bayansa ?ari bisa ?ari.
A haka aka shiga satin bikin kamfani, wanda ke nuni da daura sati biyu kacal gagarumin bikin auren da familyn Darma ke shirin yi na ?a?a biyar cif. Ana cikin wannan shirye-shirye Ammie tazo Abuja tare da Daddy. Zai ?an yi wani aiki na kwana biyu anan tace zata biyoshi dan ta ?an huta da hayaniyar gidan su, daga nan su ?anyi shawara da Shahidah. Sai dare Shahidah da Manaal suka je gaishesu dan da rana suna wajen aiki. Sai kawai Maanal ta ma?ale anan zata kwana wajen Ammie. Dan haka su Shahidah suka wuce suka barta. Washe gari Daddy ya cema Ammie ta shirya ya kaita ta gaida Oum gaskiya. Dan bai kamata ta shigo Abuja ta fita bataje ba tunda komai ya wuce. Tayi farin ciki da hakan sosai kuwa. Bayan sallar juma’a Maanal ta taso aiki sai kawai suka tafi tunda ita ta san gidan.
Sanye take cikin Abaya fara tas da tai mata ?yau sosai. Sai ?an kwalliyar golden ka?an a jikinta. Kasancewar zuwan na surprise ne sun matu?ar saka Oum a farin ciki. Nan fa ta shiga kai-kawon musu hidima. Sunfi mintuna goma da zuwa sai ga Yaya Fawzan da Babban Yaya da su Naufal sun dawo massallaci. Suma sunyi farin cikin ganin su Ammie ?in. Cike da girmamawa suka shiga gaida Ammie, dan shi Daddy yana ajiyesu ya wuce akan sai an jima in ya dawo ?aukarsu ya zai shigo. Gaishesu Maanal tayi itama. Fawzan ya tasata da tsokanar daya saba mata Babban ya na tare mata. Ita dai yau murmushi kawai take ta kasa maida masa. Suna cikin haka AA ya shigo shima. Yana sanye cikin mayan kaya da suka masa ?yau. Sai dai a kallo ?aya zaka fahimci irin ramar da yayi, ga ?asumbar daya tara sosai yanzu baya gyarawa. Yana yin sallama idonsa akan Maanal ?in ya fara sauka. ?an turus yayi kamar yanda itama tayi duru-duru, sai kuma ya janye idanun nasa cike da basarwa ya ?arasa shigowa. Itama natan ta janye tana mai danne komai. Oum dake kallonsu ta cije lips, hakama Yaya Fawzan sai da ya ta?e baki. Ammie kam kallonsa take fuska ?awace da murmushi. A mamakin kowa sai sukaga shima ya saki murmushin, tare da cigaba da takowa a hankali cikin nutsuwarsa ya nufi kujerar da Ammien take Oum a gefenta. Saman carpet ?in ya zauna a gaban Ammie gab, sam ya kasa ha?a idanunsa da Ammien, wani irin kunyarta mai girma da bai ta?a ji ba a shekarun baya yake ji a yanzu duk da kuwa ko randa suka ha?u a Kaduna ma yaji hakan, amma sai yaji na yau yafi na waccan ranar girma kodan daga su sau su ne oho. Sai da ?yar ya iya dai-daita nutsuwarsa ya shiga gaisheta. Kasare Oum da su Babban sukai suna kallonsu…
Gaisheta ya farayi cike da nutsuwa da girmamawa. Murmushi mai sanyi Ammie ta saki, cikin danne komai cike da kulawa ta amsa tare da fa?in, “Ikon ALLAH Ajwaad baka da lafiya ne? Irin wannan zabgewa haka lokaci ?aya?”.
Idanunsa ya ?an lumshe tare da sakin murmushi mai sanyi. Yanzun ma kansa a ?asa ya bata amsa da, “Lafiya Lau nake Ammie. Kai kawo ne kawai na yau da kullum kin san muna shirin fitar da project ?in mu da Maanal tai aikin sa”.
“To, to ALLAH sarki ai ban sani ba. Kasan ?ar uwar taka ta koya miskilanci yanzu ko labari bata bani ba. ALLAH ya sanya albarka yasa a fitar a sa’a”.
Da Amin duk suka amsa, yayinda AA ya ?ago ya ?an kalla Maanal. Suna ha?a ido ta hararesa da ta?e baki ta ?auke kanta. Karan farko ya saki wani ?an murmushi shima ya ?auke nasa idon, sai suka sake ha?a ido da Fawzan alamar yana kallonsu shima kenan. Harararsa shima AA ?in yayi. Fawzan yay dariya yana ?auke kansa da fa?in, “Gulma ajali”. A fili. Dan haka kowa ya kallesa. Ganin duk sun watso masa idanu sai ya nuna AA, ya ce, “Dafa wancan yaron nake”.
Sake harararsa AA yayi, Ammie dake murmushi ta ce, “Fawzan har yanzu dai baka canja ba ashe”.
Dariya yayi shima, ya ce, “Kai Ammie ALLAH na canja sosai, ?anki ne dai yana nan da ba?in halinsa.” ya ?an kashema AA ido.
“A’a Fawzan Ajwaad mutumin kirki ne. Shi dai ba mai yawan magana bane kawai”.
Murmushi sosai AA yayi saboda jin furucin Ammie, matar da yakema kallon uwa bayan iyaye biyu daya mallaka a duniya. Wato Oum da Mamy. Hakama Oum da Babban Yaya duk murmushi sukayi. Babban Yaya ya kalla Fawzan tare da fa?in, “Kasan shi Auta ?an gatan iyayensa ne, basa ta?a yarda da laifinsa in dai Ammie ce da Oum”.
Dariya Ammie tayi da fa?in, “Kaima harda kai Fadeel. Shike nan munji ?in”.
Haka sukaita hirarsu cikin nisha?i gwannin sha’awa. Yayinda Maanal ta ?ir?irarma kanta barcin ?arya, aiko Oum tace ta tashi taje ?aki ta kwanta. Babu yanda ta iya ta mi?e, duk da koba komai ta gujema idanun AA ai….
Bayan sallar la’asar Oum ta tafi raka Ammie sashin Mamy, a ranta tana mamakin rashin shigowar Mamy ?in su gaisa da Ammien. Dan Saheeba da Nibras sun shigo. To ko basu fa?ama Mamy ?in bane?. Tunanin hakan yasata kauda zancen a ranta suka fice. Sun bar Maanal tana salla, itama bayan ta idar sai ta fito da nufin bin bayansu kamar yanda Ammie tace mata.. Harga ALLAH ita ba sanin sashin Mamy ?in tayi ba tunda wancan karon da duka zo bata ma gidan. Dan haka ta fara canki canka a tsakanin sassan gidan.
“Mi kike nema?”.
Muryarsa mai sanyi ta fa?a a bayanta. Da sauri ta juyo dai-dai da shigewar ?amshin turarensa cikin hancinta. Yitai kamar ta daburce, ta dai samu ta saita kanta, idannunta ta janye daga kallonsa tare da furta, “Sashen Mamy”.
Sashen Mamy ?in ya ?an kalla. Sai kuma ya janye idanun nasa ya sake maidosu a kanta. Yatsunta da taketa faman matse gefen veil ?in abayarta ya zubama idanu kafin ya kauda yana ?an cizar gefen lips ?insa.
“Idan babu damuwa ina son muyi magana”.
“Magana? Tami kuma?”. Ta fa?a a sanyaye. Idanunsa dake ?yalli kamar ruwa na taruwa a cikinsu ya janye daga kanta. Shima cikin sanyin ya ce, “Plesse”.
“Okay ina jinka”.
“Ba’a nan ba”.
Ya bata amsa yana barin wajen. Bayansa tabi, sai da suka ?an zagaya can baya ya bu?e wata ?ofa sai ta gansu a wani kyakkyawan waje, ga ?aton swimming pool da kujerun gefen ruwa. Daga can gefe furanni ne da ?amshinsu ya sake ni’imta wajen matu?a. Baka jin komai a wajen sai kukan tsuntsaye masu ?yau farare tas daketa kai-kawo. Matu?a wajen ya ?ayatar da ita, sai faman kalle-kalle take. Wajen zama ya nuna mata a wasu rukunin fararen kujeru bayan yaja kujera ?aya baya. Sai da ta zauna sannan shima ya zauna. Tsawon sakanni baiyi magana ba itama kanta a ?asa, kafin a hankali ya furzar da iska ya ?an gyara zamansa.
“Maanal!”.
Ya kirayi sunanta abinda bai cika yi ba. Sai ko da taji tsigar jikinta ta tashi, amma sai ta dake ta amsa masa da, “Na’am” batare data ?ago ba.
“Kin tabbatar kina son Rafeeq?”.
Harga ALLAH sai da hanjin cikinta suka yamutsa, kanta yay mata wani irin nauyi amma dai ta dake ta jinjina masa kanta. Sai da ya lumshe idanunsa ya sake bu?esu a kanta. Yayinda ma?oshinsa keta faman kai-kawo a cikin wuyansa, sun jima shiru yana kokawa da kansa kafin yay murmushi irin na takaici mai sauti, ya ce, “Shike nan Alhamdullahi. ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri’a masu albarka. Ki ri?e min shi amana. Rafeeq mutumin kirki ne, yanda kikaga halayen Oum shima haka yake, yana da sau?in kai da da?in zama. In har kika zama mai biyayya a gareshi zaki ci ribar zama da shi matu?a. Kema na sanki da ?yawawan halaye tuni, dan ALLAH kada ki canja, ki zama mai yin koyi da Ammie azaman ha?uri da miji. Ina miki wa?an nan nasihihin ne kasancewata yayanki, zakuma ta iya yiwuwa shine zama na ?arshe da zan yi da ke. Dan zanyi tafiya mai nisa ne….”
Yanzu kam Maanal ta kasa ri?e hawayenta, shaaaaa haka suke zubowa suna sauka. Muryarta na rawa ta ce, “Ina zakaje?”.
Murmushi ya yi ka?an, yana mai kauda idanunsa da suka gama ka?ewa jazur a kanta. “Zanje wani wajene mai nisa”. Ya sake fa?a a dun?ule. Batare da ya jira amsarta ba ya cigaba da fa?in, “Akwai sa?o zan bama Rafeeq zai baki daga baya, abu na ?arshe zan dam?a amanar MAWAAD a hannunki…..”
A firgice ta ?ago tana kallonsa jikinta na tsuma ga hawaye. Harshenta har har?ewa yake wajen ambaton, “Mawaad? Kana nufin kamfani? Saboda mi?”.
Kansa ya jinjina batare daya kalleta ba. Sai kuma ya mi?e dan yakai ma?urar da bazai iya cigaba ma da mata bayanin ba, sannan baya son taga abinda ke ?o?arin fito masa ta hanci. Sai da ya juya mata baya yasa handkacheff ?insa da sauri ya tare hancinsa. Tsawon sakan biyu ya goge tsaf sannan ya juyo. Ganin kallon da take masa ya sashi sakin murmushi. “Duk kin maida kanki raguwa yanzu. Komai kuka. Shike nan na fasa yin bayanin zan ajiye miki komai a rubuce. Ina fatan dai kin gama shiryama bikin nan na gobe? Dan kin san kece tauraruwar taron”.
Hannu tasa ta share hawayenta, batare data masa magana ba ta mi?e zata bar wajen. Sai da tai taku biyu sannan ta ce, “Ni bazan zo ba”.
Da sauri yasha gabanta. Cike da kwantar da murya ya ce, “Ashe baki so nima naje kenan Besty?”.
Da matu?ar mamaki take kallon, hawaye na cika mata ido. Ya jinjina mata kansa. “Tabbas idan baki je ba nima bazanje ba”.
Wani kalar kuka ta sakar masa, sai kuma ta zagayesa da gudu ta fice a wajen gaba ?aya. Idanunsa kawai ya lumshe ya cigaba da tsaiwa a wajen, kafin ya kai hanky ?insa saman hanci jin abun zai zubo…..
