Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 25

25

Duk wannan shirun da Ababa yayi sudai hankalinsu bai kwantaba sbd sunsan ba shirun lafiyane ba,

Sumayyahn Kuma yanayin jikinta kaman kada a San da cikin sai ciwonta yayi sauki sbd Daman kullum harda qarin fargaba da tsananin tashin hankalin tsoron ranar bayyanar cikin Amma yanzu Tinda ta faru ta qare Ababa yasan da cikin sai zuciyoyinsu suka Dan dawo hayyacinsu kadan duk da Basu San makomarsu dashi cikin Kansa har lokacin ba Amma dai suna jiran tsammani daga shirun Ababan.

Hande kuwa duk motsin da zasuyi yanzu ta Saka musu Ido kullum fada da hantara sbd ita har lokacin takasa saukowa daga fushi da bacin ran samun cikin gashi Ababan ta rasa gane Kansa yaqi fadan komai har lokacin.

Shikuwa Sam baimasan handen nayi a Dan kuwa kusan kaman zaucewa yake Neman Yi duk Daren Allah har gari ya kusa wayewa lissafi yake na dukiyar kaantes da tsaban arzikin da Allah yayi musu,

Ya kasa yarda da jinin kaantes ne a gidansa Dan haka ya yariga ya yanke shawarar sai an haife cikin Ras da yardar Allah.

Anne ba yanda ta iya itama bayan taya ‘yarta rainan cikin tinda dai kaddara ta rigayi fata,

Kulawa sukeyi da sumayyah sosai ita da Benazir,

Gaba daya aikin gidan sun dauke mata sune sukeyi duk da kusan Benazir Ce kawai me aikin Annen tafara sanyi Bata wani iya aikin sosai.

Kwanaki da satika suka shude a hakan sunata fama har hutunsu ya qare Benazir Ce kawai ta koma makaranta Banda sumayyah sbd ita kam nata karatun da alama ya tsaya Kuma ga ciki daya Dan fito ana ganinsa.

Da aka koma hutun Benazir komai Ababa Bai fada mata ba akan kula Maza bayan kalma daya

“Idan kuka kawo min wani cikin gidan Nan wlh ko na bill gates saina binne ki da Rai,

Ki kula namiji harya dirko Miki ciki kigani idan bazan iyaba”.

Bata buqatan qarin bayani sbd tasan Babu abinda ya fada Wanda bazai iya aikatawa ba,

Kuma ko da Bai fada din ba tinda ciki ya bayyana jikin sumayyah wani irin sabon tsoron Maza Mai tsanani ya shigeta sam Bata ko iya gaisawa dasu tayi nesa nesa dasu,

Nasir ma tini hankalinta yake mummunan tashi idan ta gansa bare ya kusantota Yana son Yi mata magana.

Ms Aysha dai Bata dawoba da alama tabar Nan din Kila ba lallai ta dawoba kwata kwata Dan haka jikinsu yayi sanyi sbd Basu cire ran samun mafita ba daga gareta Amma yanzu da suke da tabbacin Kila ba dawowan zatayi ba sai jikinsu ya mutu tareda fidda Rai daga ganin Alh Bilal Shima.

Dayake Kuma wannan Karan ba sumayyah a makaranta sai Benazir ta Sami nutsuwar tsayar da tinaninta da hankalinta guri daya sosai tana fuskantar karatun nata.

Wannan Karan Kai tsaye cikin tsoro da gudun sabuwar masifa tacewa sulaiman Mai napep dinsu ya dena zuwa kwata kwata ita dai zata ringa zuwa a mashin din dasuka saba.

*****Ahankali lokacin yaketa sake Dan tafiya sunata sake zubawa sarautar Allah Ido suna jiran Ababa da har lokacin baice komai ba,

Abinda Basu sani ba Yana sane da Alh Bilal baya qasar sbd binciken tsaf Da sirrin daya yiwa zuriar kaantes yasan har boyayyan sirrinsu da duniya Bata sani ba sbd har abada bazasu taba bari a sani ba,shi kuwa kudin gaske ya barar masu yawa kusan fiye da Rabin tattalin arzikinsa sai daya qare gurin bincikensu sbd su din bana wasa bane yama Yi arziki da ba duka dukiyarsa tashige ta qare gurin binciken nasu ba Dan haka gabaki daya lissafinsa akan cikin da sumayyah da komaima daya shafi cikin ya sauya kwata kwata Kai tsaye magana Ce ta dalolin gaske kawai kokuma wlh duniya tasan abinda basa son a sani.

Satin benazir uku da komawa makaranta cikin sumayyah ya fita wata hudu ya shiga na biyar a lokacin Kuma sai lafiyar tafara gagararta sbd rashin kula da rashin abinci Harma da rashin magani irin Wanda masu ciki suke buqata,

Jini isashe ma Sam da alama Babu a jikinta Dan haka hankalin Anne Dana Benazir yafara tashi.

Tin yanayin jikinta kadan kadan ne har jikin yafara tsanani ruwa ma Bata iya Sha tana Sha zata amayar dasu ga zazzabi da kullum dashi take kwana dashi take tashi.

Babban tashin hankalinsu da tsoronsa kada wani Abu ya sameta har ita har cikin sbd yanzu Kuma akan cikin sunsan Ababa da wani abin ya samu cikin ya fison sumayyahn ta rasa komai Amma dai ta haife cikin.

Hande tana gani yanda kwana biyun suketa fama da sumayyahn data fara rikicewa gabaki daya Amma tai musu biris sbd ba itace ta aikesu dauko abin kunyar da takaicin ba kokuma taje ta ta shiga lamarin Nasu cikin ya samu matsala Ababa ya haukace musu a cikin gidan Dan ita yanzu ta rasa masifar data samesa ya Hana su bari komai ya samu cikin.

Cikin dare sosai jikin sumayyah ya rikice wani irin ciwon mara da zazzabi Mai qarfin gaske da rashin gani suka taso mata haiqan,

Rawa da kakkarwa dukkanin jikinta keyi hakama numfashinta na Neman daukewa,

Benazir da Anne idanuwansu wani irin ja yai kukan ma ya kasa zuwar musu sbd tashin hankalinsu yafi qarfin kukan,

Rungume suke da ita a jikin Benazir

Anne taje ta debo ruwa takawo suka Ringa goge mata zufan dayake jiqata da tsananin ciwo.

Basuda mafita basuda yanda zasuyi

Tsoro biyu ne fal cikeda ransu dayake gigita ruhi da gangar jikinsu,

Tsoron rasa sumayyahnsu da tsoron rasa cikin na Ababa Dan yanzu ya zama tamkar nasa ne gurin Iko.

Idan wani Abu ya samu cikin ba lallai ya barsu da sumayyahn tasu ba Idan ita ta tsira kenan bayan rasa cikin.

Cikin karyewar zuciya benazir ta kalli Anne da jajayen idanuwanta tace

“Anne mu fadawa Ababa sbd kada wani Abu yafaru Yace mune muka kashe cikin nan tinda Yana zargin munason cire cikin ne.”

Cikin sauri Anne ta gyada Kai Bata hayyacinta sbd mafita take nema kada ta rasa yarta.

Miqewa tayi da sauri cikin duhun dare ko gabanta Bata gani Amma dayake sun saba da duhu su basuda hasken rayuwa Basu a hasken fitila

Ta nufi hanyar dakin Ababan tana Isa Saida tayita rawar hannuwa data qafafu sbd kada ta buga Yace ta buga masa kofa da karfi ta tayar masa da hankali cikin baccinsa.

Ahankali kaman mara laka a jiki ta Dan fara buga kofar da qaramin sautin da bazai razana baccinsa ba.

Jin shiru ya sata sake bugawa sbd kowane second Jin zuciyarta takeyi kaman zata fito kirjinta sbd tsananin tashin hankalin ciwon sumayyah.

Mintina kusan biyar ta share tana buga masa kofar kafin ya taso ya Bude Yana kallanta idanuwansa cike da bacci sbd idanuwansa dasuka kumbura a yan kwanakin sbd rashin bacci akan lissafin yanda rayuwa cikin ahalin kaantes zata kasance masa.

Ganin Anne tsaye tana hada uban zufan duk ta jiqe idanuwanta duka a waje yasa gabansa faduwa ya murxa qananun idanuwansa cikin saurin da Bai san yana shi ba yace

“Lafiya? Me akayi ne?

Rawa muryanta ya sake dauka zuciyarta na karyewa tace

“Sumayyah Ce ba……” Bata qarasa ba ya tureta gefe Yana nufar dakin da sauri sbd idan aka samu matsala wlh kariyar arzikinsa yazo Dan komai baida yanzu na kirki duk ya barar kudin bin diddiqinsa.

‘daruruwan kudi masu nauyi ke binciko sirrikan irin su kaantes

Su ya zubar ya samu lagwansu daya idan ya rasa cikin nan ai sunansa ya tashi daga Ababa yakoma Nobaba.

Yana Isa dakin ya tadda sumayyahn ta sume a jikin Benazir

Benazir na wani irin kuka mai hade da radadin zuciya.

Kafar benazir ya take Yana taba kirjin sumayyahn yaji idan ta mutu ne.

Anne data dauka sumayyahn ta mutu zubewa tayi bakin kofa tana Neman rasa nata numfashin itama hannuwanta da qafafunta na wani irin rawa.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected