Acikin Gidana 20
Kitchen taje ta dafa musu tea ,ta bude fridge ta dauko wani cake da best friend dinta ta kawo mata as gift ,friend din nata dakanta ta kawo mata sanda aka kowata ta saka mata a fridge ,cake din ta dauko tayi slicing ta hada musu tea a dinning da wani bread data gani da butter sai sardine ,kamal yana mamakin yanda take hardworking,gashi tayi kyau har ta fara sakin jikinta ,gaisheshi tayi har kasa ,bata iya hada ido dashi ,da Kansa ya rike mata hannu suka zauna kan dinning ,bayan yaci cake dinne yake ta wani daga cake din trying to figure out dadin ta Ina yake fitowa ,princess wannan cake din inajin ban taba cin cake me dadinsa bh gaskia ,yayi dadi ,murmushi tayi ,yaya kamal Farah ce takeyin cake din ai ta iya cake sosia ,ai kam dole mu dinga siyo cake dinnnan ,yi mana placing order Yau ma ,number dinta ta shiga dubawa +234 704 040 4884 ,Yawwah ga number din nan tayi dailing ta kirata tayi musu placing order ,suna cikin cin abinci call ya shigo,dauka yayi yaga Amrah Ke kiransa ,saida gabansa ya fadi , danshi har ya Saba da Amrah Tana sakashi faduwan gaba ,kuma ya dade baiga call din Amrah na kiransa bh ,”Salam Aliakum “,cikin muryar me kaman kuka yaji ance ,”Wa’alaikum sallam ,Ina kwana “ “saida ya sake kallon phone din Jin Amrah na gaisheshi ,can kuma ya Amsa “lafiya kalau Amrah ya kk ,Ina baby Muhammad?” “Yana lafiya ,dama nace sai kuma ta fashe da kuka ,tashi yayi daga inda yake Ina zuwa yacewa Yusrah ,”Dama nace dan Allah ka yafemin duk abun danayi maka ,Ina sonka kamal ,sai ta fashe da wani kuka me cin rai “” Babu komai ya wuce ,Allah ya shirya min Ke Amrah ,Allah ya hada kanmu ,Allah ya miki Albarka,zanzo gidanku anjima kinji Ko ,ki daina kukan “, A’a ai na dawo gida mh dazu da sassafe “saida kamal yayi wani murmushi Sannan yace “Thom shkkn Allah ya Mika Albarka “,bayan sun gama breakfast ne yace mah yusrah ta masa listing abubuwan da takeso komai da komai ,Sannan ta shirya zasu fita ,bayan sun gama shiryawa ne suka wuce gidan Amrah a kofar ya tsaya ya mata text ,”Ganinan zamu shigo nida kanwarki “,kallon yusrah yayi bafa gidanku zamu bh naga kina wani murna murmushi tayi ,gun sister dinki zamuje mu gaisa a wuce gurin ko ,bata musa masa bah ,dan yusrah ta kaddarawa ranta duk abun da kamal yace bazata musu masa bh ,duk yanda ya Dama haka zasu sha ,gidan suka shiga Kai tsaye ,Muhammad ya dauko daya gansa a parlour yana wasa shi kadai ,Ina zuwa yace,daki ya shiga ,ganin Amrah yayi anci kwalliya Kama itace Amaryar ,har kasa kuwa ta tsugunna ta gaidashi ,saida yace tashi sanann ta tashi ,abun ya basa mamaki Amman dai kawai ya basar , zo nan ,ya bude hannayensa ta shige ciki harda kwallarta,kukan na mene? ya tambayeta ,babu komai tace masa ,Thom muje ?,eh tace gaba yayi tana binsa a baya ,suna zuwa parlour Amrah saida kirjinta ya buga ganin kyakyawar yarinya ,kwalla taji Zata fito haka ta daure ta hadiye ,tuno fadan mama talatu tayi haka ta daure ta dinga yake ,bata zake ba dai dan an gaya mata karta zagewa kishiya ,safa safa dai tayi mutunci Amman taja class dinta ,haka kuwa akayi dama yusrah ba gwanar magana ba ,kowa yana dan Jan class dinsa ,kamal ya hadasu ya musu fada ,dame magana? Kowa shiru yayi to Allah ya muku Albarka ,haka suka tashi suka tafi ,sai bayan sun tafi ne ta fashe da kukanta ,tayi kuka sosai da regretting rashin rike mijinta ,ta barshi sakaka,professional husband kaman kamal , caring loving and respectful Man ,babu komia tace haka Allah ya kaddara ,itama ta shirya zaman aurenta me kyau ,ta koma ga Allah hardasu sauka su sadaka ,ladabi biyyaya babu Kama kafar yaro ,kamal har mamaki yakeyi ,he was like Allah ya kaddara zai Aure yusrah ,kuma matar mutum kabarinsa ,Amman Amrah abun da take masa yanzu da tun can baya haka take masa da rufe masa ido zatayi ya kasa ganin Ko wace mace ,danshi bamashida time na kula mace but haka yayi squeezing ya Nemo ,Rayuwarsa ta canza ya zama namiji sosai
A joint dinsu suka hadu sunata hira cikin Farin ciki dajin dadi ,Aliyu ne yace gaskia mu dinga sadaka muna godewa Ubangijimu daya bamu mata nagari ,nidai Astagfurillah bansan me nayi Alllah yayi blessing Dina da mata ta gari bh Alhamdulillah Allah yabarmu da matan mu ,Mubarak ne yace wlh kuwa Aliyu we’re blessed ,Allah mun gode maka da kasa muka gane wannan Rahama dakayi mana ,Alhamdulillah ya Allahu ,kamal ne yayi gyaran murya ,wato Ashe haka kukejin dadi ko ? to Nima naji abun da kukeji ,dariya sukayi masa ai munga Alama ,ga wani kumatu daka tara anan ,toh Alhmdl mungode Allah ,babu abun godiya sai Allah ,Allah kabarmu da matanmu har A Aljannah Ameen Sukace
****Safiyya kuwa bayan ta farfado Akan gado asibiti taci kukanta ta koshi ,hakan nan ta koma gidan Jabir jiki babu kwari ,Dagewa tayita yi da Addua sadaka da saukar Alqurani ,Tana Addua tanawa mijinta Addua ,Tana cikin Jin radio ne taji wani Malami ya gama waazi yace idan dame tambaya ya Kira ,Anan ne ta dauka number dinsa ta masa waya ta gaya masa duk abun dayake faruwa ,tambayar ta yayi a baya babu Wanda kika cuta babu Wanda kika zalunta? babu wani Hali da kikayi Mara kyau Wanda Allah ya hana? Tuna Rayuwarta da Aliyu tayi bata boye bh ta gaya masa ,Amman mallam ai na tuba kuma nayi istibra’i,kuma wlh tunda na tuba ban sake bh ,Malam ne yace hakane kuma Allah ya miki Albarka tuban da kikayi, Amman kinsan hakkin wani Akan wani ? dole Allah zai bi ma kowa hakkinsa ,kaman yanda kikace yanada mata dinann ,toh bakisan hakkinta da kika dauka bh ,ki godewa Allah mah sakayar tun a nan duniya ne Alamun da sauki ,dan kaji tsoron Laifin da zakayiwa Allah ya Bari sai ranar gobe kiyama ya kamaka ,A lokacin da za’a Baka zabi ,zaka gwammace da tun a duniya anyi punishing Dinka ka tashi free,and kuma kisani fadar manzon Allah ne (S A W)”Duk abun da kayi sai anyi maka,watakila mah naka yafi abun da kayi ,Ai gaba da gabanta ,Ki cigaba da istigfari komai zai wuce insha Allahu ,Allah ya yafe mana gabaki daya ,ameen tace ,haka dai taci gaba da Addua da fadawa Allah ,kullum cikin istigfari,A kwana a tashi shima Jabir ya dawo hanya ,ta samo kan mijinta soyayya suka sake zubbawa me Rai da lafiya Amman dai Tasha wahala ba karya ,agabanta zaiyi waya tayi magana kuma ya daketa ,wataran mah baya kwana a gida ,kota kirasa mace ta dauka Suna moaning ,Akwia sanda mh ta sake ganinsu a boysquatters ,Ashe mh yarinyar daya kawo ta dade a gidan sai ranar ita ta ganta ,yaje ya cita itama yaje ya kwanta da ita ,Amman cikin ikon Allah ta tashi tsaye da Addua shima ya tuba ya dawo kan hanya ,Soyayya sabuwa sukeyi kaman zasu cinye kansu
****
Haka kowa ya cigaba da Rayuwarsa cikin soyayya kulawa ,kwanar juna da biyayya ,basa mantawa da Addua ,sadaka ,sallatin Annabi ,Istigafari ,saukar Alqurani,Sallar dare ,da tsoron Allah
Toh yan uwana mata ,Allah yasa mun ilimantu ,mun nishadantu ,kuma mun Amfana ,inda mukayi kuskure Allah ya yafe mana ,we’re not perfect
Matan Aure mu tashi mu gyara ,mu dinga gyara ,mu duba inda mukeda laifi mu gyara ,idan abun da mukeyi karawa zamuyi Akan Wanda muke mu Kara,Aure ba Abun wasa bane ,And marriage is not an easy task but marriage is sweet ,Sex is sweet too,Allah yasa mu dace



