interstitial
GABA DA GABANTA Complete Hausa Novel

GABA DA GABANTA Complete Hausa Novel

GABA DA GABANTA Complete Hausa Novel

Page1

Cool ce!

Free book ne, Comment kawai nake buƙata please, if not zanyi abunda bakwa so
Typing ba kullum ba, sai an ganni kawai.

Ƙirƙirarraren labari ne, ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba.

Wannan rubutun mallakina ne, ban yadda a juya shi ta kowacce siga ba sai da izinina, kuma ban yarda a sɗora mini shi a kowane website ba sai da izinina.

 

BISMILLAHIRAHMANNIRAHIM

 

 

 

Dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekaru hamsin, zaune akan benci hannunsa riƙe da ‘yar ƙaramar radio, yana saurara.

Wata Haɗaɗɗiyar mota ce ƙirar Annoconda, aka kwararo dogon layin da Ita, wanda gudun da motar take ta haddasa tashin wata ‘yar ƙaramar guguwa.

A ƙofar wani makeken gate motar tayi birki, aka fara wani irin horn, sai kace yaƙi.

A gigice ya yasar da radiyon da ke hannunsa, ya miƙe a zabure ya nufi gate ɗin, yana gaganiyar buɗe shi.

Yana buɗe gate ɗin, aka turo hancin motar, zuwa wani sashi na gidan.

Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga Motar, gata nan dai kamar bata cin abinci, ban da yanayin jikin ta da kuma kayan da suke sanye jikinta, ba ka ce mace bace, saboda tsabar rama, sai dai fatar jikinta za ka kalla ka gane ‘yar hutu ce, da ga ita sai doguwar rigar material, da hula a kanta tana sanye da wani uban takalmi me shegen tsini.

Ta nufo gurin da dattijon nan yake kokawar maida gate ɗin ya rufe tsigil- tsigil, tana zuwa ta ƙare masa kallo sannan tace “wai kai dan Allah wani irin mutum ne? Kai ta abu kamar mara jini a jiki ko wanda baya cin Abinci? Duk Abincin da kake ci kamar gara amma ba ka da wani Amfani iye?, wallahi daga yau na kuma dawowa, ka barni a waje ina horn sai na tatala maka rashin mutunci, aikin banza ni ban ga amfanin ajiye ka a gate ɗin gidan nan ba, Daddy ya nace lallai sai kai za kai gadi”

Shiru dattijon ya yi, ya sunkuyar da kai, yana jin yadda Yarinyar ke surfa masa fitsara, ‘yar da ba ta fi ‘yar cikin sa ba.

Ta buɗe jakarta ta ɗakko dubu uku ta zubar da ita a ƙasa, ta ce “gashi nan ka ɗauka ka siyo mini Irish, za’a dafa mini, na store ya ƙare”

Cikin girmamawa ya duƙa ya ɗau kuɗin yace “ranki ya daɗe sai dai ban gane me ki ka ce in siyo ba”

Ta kalleshi a wulaƙance sannan ta ce “Kai abun naka ma ya yi maka yawa, to dankali nake nufi, kai Allah ya rabamu da rayuwar ƙauye rayuwar jahilci”

Bace mata uffan ba, ya juya ya fara tafiya, ita ma ta nufi hanyar shiga cikin gidan.

Wani ɗaki ta shiga cikin muryarta ta iyayi take faɗin “Mummy, Mummy”

“Na’am har kin dawo?”

“Eh na dawo, ina wannan yaran suke?”

“Suwa kenan?”

“Maids ɗin nan mana”

“Suna sashin su”

“To na bawa wannan tsohon kuɗi ya siyo mini Irish, dan na gidan nan ya ƙare, ni kuma shi nake son ayi min fatensa da dafaffen ƙwai in yi lunch da shi”

Mummy ta ce “shikenan, Allah sa kar ya yi miki shirme”

“Wallahi kuwa, ni wallahi da za’a bi ta tawa kawai a sallami mutumin nan, shekara da shekaru ya ci abun da ya ci ai, Amma Daddy ya dage lallai sai shi ze din ga gadin nan, dan Allah Mummy ki ba shi shawara a canza tsohon nan”

Zare ido Mummy tai tace “ke Fadila rufa mini Asiri ina zaman zamana, ba ruwana”

Ɗan tura baki ta yi, sannan ta ce “Any way, bari in je in kwanta dan na gaji sosai, idan ya kawo sa karɓa, ayi mini fatensa a saka yaji sosai, sai a dafa mini ƙwai guda uku a ɗora a kai “.

Mummy ta ce “Ina fatan kin gaya musu da kan ki?”.

Fadila tace “Ai ni ƙarasawa kitchen ɗin ma wahala zai bani, ni dai kya gaya musu”. Ta ƙarasa Maganar tare da juyawa, ta bar ɗakin.

Tana zuwa nata ɗakin, ta jefar da takalmanta a tsakar ɗakin, ga gurin ajiye jakunkuna, amma ta yi jifa da ita wani gurin, ta cire hular kanta ta yar a ƙasa, ta haye kan ɗan matsakaicin gadonta tana hamma, tare da yin miƙa”.

*******
Zaune take a gaban murhu, tana tura busassun kararen tafasa, sai uban hayaƙi ne yake tashi, sai fifita wutar take da wani ɗan ƙaramin murfin bokiti, tana jan majina, ga idanunta sun yi jawur saboda yajin hayaƙi.
Can da ƙyar wutar ta kama, a hankali ta furta “Alhamdilillah” ta sake gyara zaman tukunyar da ke kan murhun.

Sai da ta tabbatar wutar ta kama sosai, sannan ta miƙe ta tattare duk tarkacen da ta tara a gurin, ta gyara gurin, ta bar iya murhu da kararen da ke cikinsa.

Ta koma ta ɗakko garin masara a cikin buhu, da ƙwarya da rariya, ta samu guri ta zauna akan tabarmar kabar da ke shimfiɗe a ɗan ƙaramin tsakar gidan, ta fara tankaɗe.

Wata farar mata ce ta fito daga wani ɗaki, hannunta riƙe da carbi, take faɗin “Masha Allah, yarinyar kirki wutar ta kama kenan?”.

Shiru tayi ba ta amsa ba.

“Ke Amina magana fa nake miki”.

Firgigit ta dawo daga tunanin da take, ta fara kokawar kwance buhun garin masarar nan.

Matar tace “Amina, wai tunanin me kike yi haka ne?”.

Wadda aka kira da Amina, ta yi ajiyar zuciya tace “Inno, Wallahi tunanin jarrabawar placement ɗin mu nake yi”.

Inno ta taɓe baki tace “Ai sai ki yi tayi, wannan bokon ko ita ce karatun shiga aljanna yaci ace kin haƙura haka”.

“Inno, dan Allah ki fahimce ni, ina matuƙar son karatun nan ne, dan Allah ko rance ne, ki aro kuɗin nan, in biya jarabawar nan, kafin Baba ya turo kuɗi”.

Inno ta ce “ba abunda zan aro Wallahi, shegiyar boko da bata da wani amfani, kin yi abun da ki ka yi, sai ki haƙura haka, ki dawo ki yi Aure, amma ana ta ƙananun maganganu akan ki a garin nan, saboda baban ki ya ɗaure miki gindin wani wai sai kin yi boko, har yanzu banda tarkacen takardu, ba uban da ki ka ajiye a bokon, shekara da shekaru kina galmashura a titi yawon boko, kullum sa dai ki kawo takaddun banza ki ajiye. Ni na kusa ɗakko buhun takardun ma, in yi makamashi da shegu kowa ma ya huta”.

Ba tare da gazawa ba, Amina ta kuma cewa “to dan Allah Inno, ni ki bari in rubuta wasiƙa a kaiwa Baba, ya taimaka mini, ya aikon da kuɗin in biya jarrabawar, tun da ba zaki biya mini ba”.

Inno tace “Ke Yanzu ya turo da kuɗi ai muna da tarin buƙatun da suka fi na wannan bokon banzar ta ki amfani, ba wani kuɗi da zan bari ki kai wata makarantar boko”.

Amina ta ɗan tura baki tace “Inno dan Allah ki dena cewa bokon banza, Wallahi ilimi yana da matuƙar mahimmanci ga rayuwar ‘ya mace”.

“Dalla rufe mini baki, mahimmancin me? Mu da ba muyi bokon ba mutuwa mu kayi? Ko kuwa wani abu ya same mu? Ni yi sauri ki yi ki gama mini aikina, kije wancan tijararren ƙanin uban naki, yace kije ki kaiwa matarsa Niƙa”.

Take Amina ta tsuke fuska tace “ba in da zani, ‘ya’ya nawa ne a gidansa, amma ni aka mayar kamar jaka, in yi aikin gidanmu, na gidansa sai naje na yi musu, Wallahi ba zani ba, idan na gama girki ruwa zan ɗebo mana”.

Inno ta ce “Ni dai ba ruwana, kin san halinsa, kar ya zo yana mana ihu a cikin gida”.

“Yayi da wata ba dai da ni ba” Amina tai maganar tana hura hanci.

***********

“Ke! Meye sunan naki ma? Ina Abincina da nace ku girka mini?”.

Wadda aka yiwa kiran wulaƙancin, ta ɗan risuna tace “Anty ai ba’a kawo dankalin ba”

“What? Kamar yaya?”

“Eh, Hajiya tace Baba Hassan zai kawo dankali, mu karɓa mu girka miki, amma be kawo ba”.

“Yanzu duk wannan yunwar da nake ji, ba’a kawo dankalin bama, balle in saka ran a dafa a bani, wato yunwa ta kasheni ba shi da asara ko? Lallai wannan an yi tsohon kawai”.

“Kaiii, Fadila ya ne? Tun daga ɗakina ina jiyo muryarki kina faɗa, ke da waye ne haka?” Tai maganar tana ƙarasowa cikin falon.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected