VENNETE
DR. SAIF RETURN Complete Hausa Novel

DR. SAIF RETURN Complete Hausa Novel

*DR. SAIF Complete Hausa Novel*
_(return)_

©Ummu Hanan.

Bismillahir Rahmanir Raheem

Haske writer’s associated
(Home of expert & perfect writer’s).

A hankali had’add’iyar motar tayi parking a harabar hospital d’in kusa da jerin gwanon motocin dake parke a wajen.
K’ok’arta ki fito Ayshaa kinji?, Naji wata murya ta fad’a daga cikin motar, “Aunt Salma bazan iyaba fa” wata siririyar muryar mace ta fad’a cikin shagwa6a, “daurewa dai zakiyi meye amfanin zuwa asibitin?.
Mintuna kadan wata matashiyar mace ta fito riqe da wata matashiyar budurwa dabazata haura sha bakwai ba kyakkyawace sosai kamar su d’aya da matar da alamu yayarta ce,
Tarairayota jikinta ta qara yi tana d’an murmushi gamida girgiza kai ganin yadda d’an zazza6i kad’an ta zauna sai shasshake mata take.
Kai tsaye office d’in babban likitan suka nufa bawani layi sosai daga Wanda ke ciki saikuma wasu mutum biyu masu jira, layi sukabi suma gaba d’aya Ayshaa ta kanannad’e Aunt Salma ta hanata motsin kirki sai faman 6ata fuska take kamar mai shirin sakin kuka.

Wad’anda suka shiga d’in basu wani jimaba suka fito sukuma suka shiga.
Had’add’en office ne daya wadatu da kayan zamani da ake qawata ofisoshi dasu sanyin A.C da qamshin air freshener da kuma na mamallakin mai office d’inne suka cakud’a suka bayar da wani irin daddad’an qamshi mai sanyaya rai da yanayi mai dad’i.

Idona ne ya sauka kan mai office d’in, fatabarakallahu ahsanul qaleeqeen, kalmar dana ambata kenan cikin raina saboda had’uwar mutumin tun daga zaunen zaka fahimci cewar giant ne ALLAH ya azurtashi da wani irin sirrin kyau mai d’aukar hankalin jama’a.
Idanunshi a lumshe suke ya dafe kanshi da hannu d’aya d’ayan kuma ya d’orashi kan table d’in gabanshi riqe da pen sosai yayi relaxing kan kujerar dayake zaune, a hasashena dai bazai wuce 31 zuwa 32 ba.
Sallamarsu ce tasa yad’an bud’e ido kad’an ya kallesu ya qara mayarwa ya rufe.

Duk da halin da Ayshaa ke ciki bai hanata ta6e baki ba, da jan k’aramin tsaki a ciki, Tunda suka zauna baice uffan ba haka suma basuce komiba bakajin komi sai sautin karatun Al’qur’ani mai girma daya kunna a wayarshi k’ira’ar khusary cikin k’arshen suratul baqrah kad’an kad’an sautin ke fita ta yadda idan baka kasa kunne sosai ba bata yadda zakaji.
Tuni Ayshaa tafara gunguni tanajan k’ananun tsaki, duk abinda take kuma yana kallonta ta qasan idonshi da tsakin datake masa.

Ganin shirun yana neman yin yawa yasa Aunt Salma ta bud’e baki zata fara magana, sai a lokacin ya d’ago ya zauna sosai kan kujerar tare da ware manyan idanunshi yana d’aga mata hannu alamun tayi shiru.
Shirun tayi kuwa cikeda mamakin irin Dr’n da ALLAH ya had’asu dashi yau, Ayshaa kam tuni ta shaq’a sosai jitake tamkar ta tashi ta shaq’o wuyanshi dan yadda ya raina musu hankali.
Kamar wanda akayiwa dole kokuma mai ciwon baki yace
“Ko zaki iya barina da patient d’in?”
Kamar wata doluwa Aunt Salma ta kad’a kai tana k’ok’arin raba jikinta dana Ayshaa databi ta kanainayeta, kamar zata saki kuka take fad’in
“Haba Aunt Salma bazan iya zama bafa”, k’ok’arta dai little sis” Aunt Salma ta fad’a tana shafa kanta gamida ficewa.
Shirun ne dai ya qara ratsa wajen dan ba wanda ya q’ara ko tari cikinsu saima wani aiki daya tsira a laptop d’insa bayan ya saka suratul Ali imraan dan suratul baqrahn harta q’are.

Yana ganinta ta gefen ido sai faman lallanqwashewa take alamun zaman ya gundureta, Itakam Ayshaa ta d’au alq’awarin indai bashi ya fara tambayar ta abinda yake damunta ba bazata fara masa magana ba tunda shine likita shiya dace ya fara tambayar ta damuwarta.
Shima a nashi b’angaren hakanne indai bata fad’a masa damuwarta ba shikam bazai tambayeta ba dan yaga alamun yarinyar y’ar rainin hankali ce (Saif bakada gaskiya fa).
Wani dogon tsaki taja ta miq’e ta fice daga office d’in bayan ta jefa masa wata muguwar harara.
A hankali ya sauke idanunshi daga kanta bayan ta fice ya tsurawa table d’in gabanshi ido “wai yarinyar nan kuwa tasan wanda takewa tsaki? Kokuwa batasan yadda ya tsani tsaki bane? (Ina zata sani). ALLAH ya q’ara had’ashi da ita kuwa san tayi masa tsaki.

A reception ta samu Aunt Salma tana zaman jiranta, da sauri ta tashi ta tareta tana tambayar ta lafiya? Ganin yanayin yadda ta fito office d’in
“Wlhi Aunt mutumin nan mugun d’an rainin wayone” ta fad’a tare da hararar inda office d’in yake.

“Tunda dai ya dubaki ai shikenan naga alamun shi ai d’an jida kaine” Aunt Salma ta fad’a tare da jan hannunta, baki ta turo tace
“Nifa bai dubani ba, bai tambayeni abinda ke damuna ba nima kuma ban masa bayani ba
“Wato kowa yanaji da kanshi ko? idan shi bazaiyi magana ba ke bazakiyi ba?”
Baki ta tunzuro gaba tace
“Amma Aunt Salma shi….”dallah wuce muje malama”, Aunt Salma ta katseta tana hararar ta.
Gaba tayi bakinta a d’ane tanajin tamkar ta koma ta gaggaya masa magana d’an rainin wayo kawai.
Da hanzari isah direba ya taso yana fad’in
“Kun fito Hajia?”
“Eh amma bata samu ganin Dr ba kaimu wani asibitin”.
Aunt Salma ta bashi amsa tana shigewa motar batare data jira ya bud’e mataba.
Ayshaan ma shigar tayi shima ya zagaya cikin rawar jiki ya shiga ya tada motar suka fice daga cikin hospital d’in.
★★★
Bai q’ara duba kowaba ya had’a nashi ya nashi yabar asibitin yatafi gida.
Sallama yayi cikin wani qaton parlour dayasha q’awa kala kala na ababen more rayuwa.
Matashiyar budurwa ce y’ar kimanin 18yrs a zaune tana game a wayarta, kamarsu d’aya saidai ita tana da d’an duhun fata kad’an kuma yafita dogon hanci.
“Sannu da zuwa Yaya” ta fad’a bayan ta amsa sallamar tana cigaba da game d’inta dan tasan bama lallai ya amsaba.
A ciki ya amsa yana tambayar ta Mamie”
“Yanzu ta haura upstairs” tabashi amsa.
Kan cushion ya zube yana sauke numfashi, har ynxn tsakin da marar kunyar yarinyar nan tayi masa bai bar sukar ransa ba, yayi dana sanin barinta ta tafi batare daya d’au mataki a kanta na jiyake tamkar ya dawo da hannun agogo baya.
“A ah ikon ALLAH tunanin me Saifu yakene haka?”
Ya tsinkayi muryar Mamie tana masa magana, murmushi ya d’anyi yana shafa sumar kanshi mai laushi.
“Gajiya ko?” Ta tambayeshi tana murmushi.
“Gajiyar ma akwaita Mamie ga yunwa tun breakfast fa”
To kaje kayi wanka kafin Imaan takawo maka abincin”.
Car key d’insa ya d’auka da manyan wayoyinshi guda biyu ya miq’e tsaye.
“Kaga daka aje iyali duk wad’annan abubuwan saidai kazo ka tarar da komi ready”
Mamie za’ayine fa ina lalubawa bansamu bane har ynx”
Baki ta ta6e tace
“Uhmm nagaji da gafara sa banga q’aho ba, ALLAH dai ya nunamin ranar da zanga matar Saifu inga wace kalace da tsawon shekaru ake lalubota”
Dariya Imaan tasaka tana toshe bakinta da hannunta, harara ya zabga mata tayi hanzariin daidaita fuskarta.
“Vry soon Mamie insha ALLAH” ya fad’i a hankali yana barin parlourn.

*DR. SAIF*
©Ummu Hanan

Bismillahir Rahmanir Raheem

Haske writer’s associated
(Home of expert & perfect writer’s)

Free page
No 2….

K’arfe 9:15 ya shigo parlourn gidan sanye yake cikin wasu riga da wando marasa nauyi farar riga da red color d’in wando,anja adon dogayen layika a gefe da gefen wandon da farin zare hular sanyi ce a kanshi mai laushi white an rubuta MY MAN agaban hular sai farin slipper dake sanye a k’afarshi mai taushin tsiya sai zuba daddad’an qamshi yake.
Kai tsaye upstairs ya nufa wajen Mamie yana stairs na farko yana shirin taka na biyu ya hango Daddy da Mamie zasu sauko downstairs da alamu rakiya tayo masa, da saurinsa ya juya zai fece kafin Daddyn ya hangoshi saidai ya makara dan daf dazai fice ya tsinkayi muryar Daddyn yana fad’in
“Karka sake ka fita ka makaro nariga na ganka”
Cak ya tsaya tare da runtse idanunshi yana dafe goshinshi q’asa q’asa ya furta
“Oh my gosh, dama bai fitaba?”
A sanyaye ya koma bakin stairs d’in ya tsaya tare da sunkuyar dakai.
“Barka da safia” ya fad’a bayan sun sauko har lokacin bai kallesu ba
“Barka dai uban y’an shiririta”Daddy ya fad’a yana kallonshi a kaikaice,ya d’ora da fad’in
“Wato Saifu idan ka sake ka shiga hannuna wllhy bazakaji da dad’i ba wato wasan b’uya ma ka fara dani ko, nagaji da nanata magana d’aya kusan shekara d’aya muna abu d’aya dakai, to anzo ga6ar da haqurina yazo karshe kaji na fad’a maka”
Kanshi a q’asa a hankali yace
“Ayi haquri insha ALLAH za’a duba”
“Okay bakama fara dubawar ba kenan?, rasa amsar bayarwa yayi still dai kanshi na q’asa sai faman susar k’eya yake.
Kai Daddy ya kad’a yace
“Good hakan yayi maka kyau” ya ka’rasa maganar tare da nufar k’ofar fita.
ALLAH ya kiyaye sukayi masa ya amsa tareda ficewa.
Marairaicewa yayi ya kalli Mamie zaiyi magana, bata kulashi ba ta nufi ainahin cikin parlourn kan cushion ta zauna, bin bayanta yayi ya zauna kusa da k’afafunta tareda kamo hannuwanta ya riq’e cikin nashi
“Dan ALLAH Mamie ku k’ara hakuri insha ALLAH nan bada jimawa ba komi zai zama labari”.
“Ah to gara dai kayiwa kanka fad’a dai fisabilillahi ace kusan shekara d’aya muna magana d’aya dakai nagaji da gafara sa banga q’aho ba, ALLAH ya azurtaka da komi na rayuwa amma ajiye mace ya gagareka ga sadeeq nan da mahfooz (causin brothers d’insa) duk sunyi aure harda albarkar y’ay’a ga kuma Sameer nan k’aninka ne amma har ansa date d’in aurensa kai kana zaune wai ko bakada lafiya ne?”
Fuska ya b’ata sosai kamar zaiyi kuka yace
“Mamie please ki daina wannan maganar dan ALLAH”.
Baki Mamie ta ta6e tace
“Ah ah to aida gaskiya ta, cikin y’an uwa ma ga y’an mata nan dayawa masu sonka ga yaran k’awayena da abokan Daddyn ka amma ka shafawa idonka toka kak’i saurararsu saboda ALLAH fa”.
“Ni Mamie duk basu yimin ba wllhy”.
Rank’washi Mamie ta sakar masa a kanshi tace
“Ai kaji matsalarka Abbana”.
Wajen ya dafe da hannunshi kamar zaiyi kuka yace
” Da zafi fa Mamie”(uhm sai an fita ai tawa mutane muzurai).
Dariya Mamie ta d’anyi tana miq’ewa tsaye tace
“Bari in koma sama dan ALLAH ka daure dai babana a k’ok’arta a samo mana suruka”.
Shima d’in tsayen ya miq’e yana fad’in
“Insha ALLAH Mamienah”.
Daga nan ta haura upstairs shikuma ya shige part d’inshi.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected