interstitial
KANWAR MAZA Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

KANWAR MAZA Book 1 & 2 Complete Hausa Novel

[16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA: KANWAR MAZA Complete Hausa Novel

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

 

 

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.

*Ina fatan yadda na fara lafiya, Allah ya sanya na gama lafiya. Ƙirƙirarren labari ne, idan akwai abin da ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne*

Page1

Bismillahirahmanirrahim

 

Daji Ajiyar Allah! La’asar sakaliya, a lokacin da hasken rana ya fara disashewa, ta doshi yamma za ta faɗi, duhun magariba na ƙoƙarin shigowa ya maye ragowar hasken da ranar ta bari kan ta ƙarasa faɗuwa.
Gamayyar bishiyoyi ne, dogaye da da madaidaita, haɗe da ciyayi da ga mabanbantan tushe, suka haɗu suka yiwa dajin ƙawanya. Zai iya kasancewa abin sha’awa ga wanda ya zo yawon buɗe ido, idan har bai san mai dajin ya ƙunsa ba.
Ga wanda ya san abin da ya ƙunsa kuwa, zai kasance wuri mafi razani, firgici da kuma tashin hankali.
Gudu take yi a tsakanin rayuwa da mutuwa, tana rungume da wani zani a ƙirjinta, babu yadda za ayi daga nesa ka gane me ta rungumo haka take wannan uban gudun.
Ƙafafuwanta babu takalmi, jikinta babu mayafi, duk da yanayin garin babu zafi, amma laɓɓanta sun bushe tamkar dutsen da ya shekara ruwa bai zuba a kansa ba, babu alamar tana gane in da take jefa ƙafarta. Duk da wannan mawuyacin hali da take ciki, ta bawa abin da take rungume da shi muhimmanci sosai da sosai.
Cikin rashin sani, tayi karo da wani abu da ita kanta ba ta kai ga tantance ko meye ba, sai dai ƙarfi da nauyin abun ya sanya ta faɗi ƙasa, take ta saki wani marayan kuka, a lokacin da jini ya fara zuba daga ƙeyarta.
Sai a lokacin abin da take rungume da shi ya tsala kuka, saboda firgitar da ya yi shima.
Jariri ne ɗanyen goyo, cibinsa ko faɗuwa bai yi ba, jikinsa duk busashshen ƙazantar haihuwa da alama yaron ya kwan biyu, amma ko ruwa bai taɓa gani ba balle a wanke wannan ƙazantar!.

**************

 

Cikin garin Kano, unguwar ɗorayi tinga, misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar Alhamis, wani matsakaicin gida ne, cikin rukunin gidajen dake ɗan ƙaramin layin, kallo ɗaya zaka yi wa gidajen, ka san na masu ƙaramin ƙarfi ne, duba da yanayin kwatoci da kuma kasancewar gidajen awon igiya, ba magudanan ruwa, babu layuka masu kyau, kowa da in da fuskar gidansa ta kalla, haka zalika kowa in da ya ga dama yake sako kwatar gidansa, wasu da gyara wasu babu, ga gidajen ‘yan ƙanana tamkar wani zai hau kan wani.

“Wai ba zaki fito ki je mini aiken ba, har sai gawayin ya ƙare tukuna?” Cewar wata matashiyar dattijuwa, da take zaune a gaban kurfoti, hannunta riƙe da mafici tana firfitawa, gefe ga farantin silba ɗauke da garin tuwon masara a kai.

Wata yarinya ce ta fito daga wani ɗakin da yake bayan matar, hannunta ɗaya riƙe da hijjabinta, ɗaya kuma sai matsar hawaye take yi.

Matar ta kalleta ta ce “Kukan me ki ke yi?”

Aikuwa kamar mai jiran ƙiris, cikin sangarta yarinyar ta ce “Ba Huzaifa bane ba ya….

“Ni yi mini shiru, haka dai kuka iya faɗa kamar kuna ganin hanjin junanku, idan na hana ki zuwa in da yake ai ba zaki hanu ba, maza ki ɗau kuɗin nan ki je mini gidan Laure, ta baki kuka ta sittin, daddawa ta arba’in sai manja na naira ɗari ki kawo mini canjin, na yi maza in kaɗa miyar nan kan magariba”.

Kwaɓe fuska yarinyar ta yi ta ce “Wai yau ma miyar kuka za ayi Innalillahi wa innalillahi raji’un”

Baki buɗe ta bi Yarinyar da kallo, cikin hasala ta ce “Idan na kaɗa kukar kar ki sha, zaki ɗau kuɗin ki fita ko sai na yi fatali da kanki a wurin?”

Ta durƙusa ta ɗau kuɗin, ta zura hijjabinta ta nufi hanyar fita, a ranta tana jin gara ace yau babu abin da zasu ci, da wannan tuwon kamar na ibada.

Cike da kashedi matar ta ce “Idan kin ga dama kuma ki je ki zauna, kar ki yi sauri kiga yadda zan yi da ke, ko ki biyewa yara ki tsaya shashanci a hanya”

Ba to ko waiwayo ba, ta yi gaba abinta tana kalle-kalle.

Gidansu ƙawarta Habiba ta fara biyawa, ta tarar da maman Habiba a tsakar gida ana yi mata kitso, ta durƙusa ta gaida Maman Habiba, sannan ta ce mata wurin Habiba ta zo.
Habiba ta fito daga ɗakinsu tana kallonta tana murmushi, ta ƙaraso in da take tsaye ta ce “Ruma ina zuwa ne?”

Cikin muryar Raɗa Ruma ta ce “Dan Allah Habiba aron tayar Sani zaki bani, Mama ce ta aikeni so nake nayi sauri na je na dawo”.

Habiba ta ce “Kaii, Ruma kin san Sani yafi kashi ɗoyi, kar na baki ki je ki salwantar da ita, daga ni har ke mu shiga uku”.

Ruma cikin ƙwarin gwiwa ta ce “Wallahi ba zata salwanta ba, ke dai ki aramini, so nake na yi gudu na ne na dawo”.

Habiba ta ja Ruma soron gidansu, ta duba saman kejin kajin da ke cikin ɗan tsukakken zauren gidan, ta ɗaukowa Ruma tayar Sani ta bata ta ce “Dan Allah Ruma ki kula, kar wani abu ya samu tayar nan, ki yi maza mi garata ki je ki dawo”

Ruma tayi murmushi ta ce “Kar ki damu, yanzu zan fyalla naje na dawo, ina son tayar nan ta sani dama ya bar mini, ‘yar dandaɓasa da ita, yanzu zaki ga naje na dawo”.

Habiba tayi murmushi ta ce “To shikenan, yi sauri kafin ya dawo”.

Ruma ta dafe kan taya, ta garata ta dinga zura gudu ta lunguna kamar wata namiji ba mace, ba ta tsaya da gara tayar ba har sai da ta isa gidan Laure.
Ta yo sayayyarta ta gama, ta fito ta kuma garo taya zata tafi gida, can ta hango wasu ‘yan makarantar allonsu, a ƙofar gidan Hanne mai markaɗe suna ‘yanta, ba tare da ta tuna da kashedin Mama ba, ta ajiye kayan aiken da canjin haɗi da tayar da ta aro, ta shiga aka hau ‘yanta da ita.

Kasancewar ƙwararriya ce a harkar shagala da iya rinto, nan da nan wasa ya ɗau zafi, ganin tana ta cinyesu a ‘yantar ta hanyar rinto, sai wasa ya koma faɗa, daga nan aka hau dambe, a wurin Ruma ta kifar wa da wata markaɗenta ga ta da ƙarfi kamar doki. Da ƙyar wani mutum ya raba faɗan, Ruma ta haɗa yaran mutane ta zane musu jiki, sai da mutumin yayi mata barazanar zai gayawa yayanta, sannan ta haƙura da damben.

Yarinyar da suka yi damben, ganin an musu asarar markaɗe, an kifar ga duka, ya sanya ita da ƙannenta suka fasawa Ruma Manjan da ta sayo wa Mama, suka kwashe canjin aiken, suka farke ledar aiken suka gudu, daddawar ma sai da ƙyar ta tsinto wasu, an fasa ledar kuka duk ta watse.

Ta kwashi sauran kayan, ta tafi gida, tana tafe tana tunanin wace ƙaryar za ta jirgawa Mama, dan ta kaucewa faɗanta, dan a duniya ba ta son faɗan Mama, gefe guda kuma tana tunanin irin dukan da zata naɗawa Safiya idan suka haɗu a makaranta allo, saboda abin da suka yi mta.
Lokacin da Ruma ta isa gida tuni an fara kiraye-kirayen sallar magariba, domin wasu masallatan har sun tayar, sai a lokacin ta sake shan jinin jikinta, tsoro ya ziyarce ta.

A soro ta rakuɓe tana leƙa cikin gidan, ta hango Mama a gindin rariya tana alwala, Mama ta ɗaga ido tayi mata kallo ɗaya, ta mayar da kai ta cigaba da alwalarta.

Cikin sanɗa Ruma ta shiga tana satar kallon Mama, ta ji mai Maman za tace mata, amma ta ji ba tace mata komai ba.
Ta lallaɓa ta ajiye abin da yayi saura na aiken, ita ma ta faɗa banɗaki tayi alwala.
Ta lallaɓo falo, ta tsaya a bayan Mama ta tayar da sallar ita ma.
Mama ta idar, ta tashi ta fita tsakar gida, ta duba abin da Ruma ta kawo mata na aiken, taga irin aika aikar da Ruman ta yo.
Ta dawo falon tana jiran Ruma ta idar da salla ta dirar amata, amma Ruma ta ƙi idarwa, ta hau nafifilin babu gaira babu dalili, matar da wataran sallar ma sai Mama ta haɗa .mata da duka take yi, amma yau sai gashi har da nafila.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected