KANWAR MAZA Book 3 & 4 Complete Hausa Novel
*
*₦500 ne, via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*
“Meyasa baka ɗau maganar mahaifiyarka da muhimmanci ba, har kake yi mini wannan barzanar a bayan idonta? Ko ba komai tana tausayina wataƙila ta san me nake ji game da sabir” ta saka idonta cikin nasa, wanda hakan ya sanya musu faɗuwar gaba a tare, cikin jarumta da ƙarfin hali ta daki motar Adam ta ce “Idan har bayan mutuwar anty aisha an yi umarnin a kashe sabir, na ɗau duk wani riski Allah ya dafa mini na kuɓutar da shi, kana tunanin bayan kuɓutarmu ne wani zai haɗa kai da ni a cutar da yaron da na ɗaukarwa babarsa alƙawarin kula da shi? Wace irin zuciya ce a jikinka?”
Ma’aikatan wurin ne suka tunkarosu, amma adam ya dakatar da su, saboda rumaisa ta faɗi wani abu mai muhimmancin gaske.
“Kai ka san abun da ya haɗani da kai ai tun farko, kuma ban janye abun da nace ba, ba zan taɓa janyewa ba kuma. Sabir idan ka ga dama ka kai shi bangon duniya, ka yi duk abun da kake ganin ya dace. Mara imani ban taɓa tsanar abu a duniya ba kamar kai, ko ƴan bindiga da na zauna a hannunsu wataran suna mutunta ni. saboda furucin da ka yi a kaina, wai a haɗa baki da ni a cutar maka da ɗa, na gode daga yau ba zan sake zuwar muku gida ba in sha Allah, in dai ni ƴat halak ce mama ce ta haifeni su yaya usman ne yayyena ba zan sake zuwa gidan nan ba” ta ɗauko maganar tiryan-tiryan ta ƙarasa da shirme, tana kuka ta juya ta nufi gate ɗin.
Jikin Adam yayi sanyi, tabbas a abubuwan da ya faɗa sun ɗan yi tsauri.
Da sauri ta fice tana kuka, ta bi hanya, dan ko za a kasheta ba zata hau motarsa ba, wata irin wutar ƙiyayyarsa ke cigaba da azalzalar zuciyarta, duk wanda zai yi yinƙurin rabata da sabir, to babban maƙiyinta ne.
Sashin Mummy ya shiga yana ɗan tunani, lokaci-lokaci kuma yana murmushi.
Mummy ta kalleshi ta ce “Bani labarin wannan murmushin, dawowar nan ta yi maka daɗi kenan?”.
Ya sake yin murmushi ya ce “Wata yarinya na haɗu da ita da zan shigo, na fita yanzu na kuma ganinta, gaba ɗaya zubinta da character ta abun dariya”.
Mummy ta kalleshi cikin nutsuwa ta ce “Ko ka fara soyayya ne?”
Ya ce “Soyayya kuma? Yarinya ce ƴar ƙarama fa, amma abubuwan da ta faɗa ya bani mamaki, wai ita ce ta dawo da jaririn nan da ake ta surutu a kai, na aisha turaki, wai ta zo ta ga ɗan ta, ya ce idan ta zo kar a sake bari ta shigo. Yarinyar mugun ƙarfin hali ne da ita, maganganunta sam ba irin na shekarunta bane, akwai shirme a maganganunta, amma akwai hikima a cikin shirmen na ta. Ba abun da ya bani mamaki kamar yadda ta iya riƙe rigata cike da ƙwarin gwiwa take tuhumata a zaton ta wancan gayen ne”.
Cikin rashin fahimta Mummy ta ce “Wai kana nufin wadda ta zo da jaririn aisha a gidan nan? Ka ce yarinya ce ƙarama?”.
“Eh, wannan ai sai kun fi ni sani ku da kuke cikin gidan, ni ban san komai a kan zancen ba, kawai dai na san yarinya ce dan ta yi wutar duniya, ba za ta fi shekara sha uku ba, a nawa tunanin”
“What! Kana nufin ƴar shekara sha uku ce ta zo da jaririn da ake cewa na adam ne? Amma rainin hankalin mutanen nan yayi yawa, ta yaya ƴar shekara sha uku za ta kuɓuto da jariri daga hannun’yan bindiga”.
Mahmud ya ɗage kafaɗa ya ce “I don’t know”.
“Amma tsaya, yarinyar tana nan haryanzu ne, ina buƙatar in ganta”
“Mummy ki ganta ki yi mata me? No need dan Allah ki daina shiga sabgoginsu da bin diddigin sai kin san abun da suke ciki, shiyasa suke raina ki, ki ƙyalesu su ji da matsalar su” yayi maganar yana miƙewa.
Bin sa da ido mummy ta yi, amma da ta iya cewa komai ba. Sai mamaki da sake jinjina lamarin giwa da ɗanta saboda zallar goge hadda, wai ƴar shekara goma sha uku ce ta kuɓuto da jariri.
Rumaisa kuwa tafiya kawai take yi tana kuka, dan ta ji zafin maganganun takawa matuƙa. Ta kusa titi kawai ta ji an danƙi hannunta, a fusace ta ɗaga kai, amma kan ta yi wani yinƙuri ya fara janta, a fusace ta fara kokowar ƙwace cikin tsiwa take cewa “Ka cikani me na yi maka?”.
Ba zata manta fuskar sidi ba, wanda suka taɓa kamota suka kaiwa takawa.
Bai saurare ta ba, ya buɗe bayan motar takawa ya jefata, ya rufe motar, Adam ya sauke glass ɗin motarsa ya jinjinawa Sidi kai, sannan ya rufe glass ɗin motar ya fara ja.
“Malam ka tsaya in sauka daga motar nan, bana son ka kaini gidan ka sauke ni bana so” banza yayi mata ya cigaba da tuƙinsa.
“Na ce maka ka sauke ni, wai kai meyasa ka ke mini haka ne? Ka sauke ni”
Ganin bashi da niyyar kulata, ya sanya ta fara kiciniyar buɗe motar, amma ta ji ƙofar motar a rufe gam.
Adam a zuciyarsa yake jinjinawa masifa da taurin kan rumaisa, da a buɗe motar take haka za ta buɗe ta ce za ta fita.
Ganin ba za ta iya buɗewa ba, ta zauna ta cigaba da kuka tana ƙanan maganganu.
Bai tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su, mamaki take yi a ina ya san gidansu?.
Ko da yayi parking bai fita daga motar ba, sannan kuma bai buɗe motar ba, rumaisa ta hau kiciniyar buɗe ƙofar motar, amma ta ji a rufe.
“Ka buɗe mini in fita” ta kai masa duka dan takaici.
Danna wayarsa ya hau yi, na wani ɗan lokaci sannan ya buɗe motar ya fita.
Sai dai ya kulle rumaisa a ciki, bai buɗeta ba, bubbugawa tayi ta yi, amma ya fita ya tsaya ya ƙi saurarar ta.
Aliyu ne ya fito daga cikin gida, yana ganin Adam ya faɗaɗa Murmushin sa, ya ƙaraso suka gaisa, rumaisa ba ta iya jin mai suke cewa, amma sun ɗan jima suna tattaunawa sannan ya buɗeta ta fito tana wani basarwa.
Wani mugun kallo Aliyu ya yi mata, sannan ya ce “Sai ki wuce ki shiga” ko a jikinta, ta yi gaba dan ita yau ko za’ayi mandaƙo da ita tun da buƙatar ta ta biya shikenan.
Wani wawan burki ta yi, da ta ga mai sunan Baba a ƙofar ɗakin mama, yana gyara botirin hannun rigarsa.
Wani irin mugun yawu ta haɗiye, ta fara takawa a hankali kamar hawainiya.
Fuskarta ƙarara ta bayyanar da tsantsar tsoro da razanin da take ciki.
Aliyu ne ya yi sallama da shi da Adam, mai sunan Baba ya amsa ba tare da ya ɗago ya kallesu ba, sai ma ja da yayi da baya ya basu hanyar shiga falon mama.
Bai kula Adam ba, shi ma bai kula shi ba, suka shiga ɗakin mama da sallama, da gudu rumaisa ta bi su tana waiwayen mai sunan baba.
Mama ta faɗaɗa murmushinta tana yi wa Adam barka da zuwa.
Ya ce “Tuba nake mama, tun da aka bar asibiti ban samu na zo na gaisheki ba, abubuwa ne sun yi mini yawa ƙwarai da gaske”
Mama ta ce “Babu komai, ya gida ya hajiyar take? Ya kuma mai gidana”.
“Duk suna nan lafiya, ta ce a gaishe ki”
Rumaisa ta kalleshi a ranta ta ce “Kalleshi, kamar ba yanzu ya gama wulaƙanta ni ba, har da shigo mana gida ya zauna, yana washe baki dan ace masa mutumin kirki”.
Mama ta ce “Rumaisa duba kitchen, ki kawo masa ruwa” sai da ruma ta ji kamar ta yi fitsari, saboda kar ta fita mai sunan baba ya kamata.
Sai da ta leƙa ta ga baya nan, sannan ta shiga kitchen da gudu, ta ɗauko pure water ɗaya, ta dawo ta tsaya a kan Adam ta miƙa masa.
Kallon da mama ta yi mata ne ya sanya ta rasa in da za ta sanya kanta, dan gaskiya a tsorace take sosai.
Da ƙyar ta sake komawa, ta zubo ruwan a wani ƙaton baho, kusan guda goma sha biyu, ta ɗauko ta zo ta dire masa.
Aliyu ya ce “Wai ke wace irin taɓaɓɓiya ce ne? Ya zai yi da wannan ruwan babu plate a kitchen ki ɗoro masa ko huɗu ne, sai ki yi wannan shirmen?”