SOLDIERS FAMILY Book 2 Complete Hausa Novel

SOLDIERS FAMILY Book 2 Complete Hausa Novel

 

Yad’auki tsawon lokaci acikin ruwan kamun ya k’walawa maheerah Kira Yana fad’ar yasamu ganin sihirin tashigo da Mama Aiko ko bakinshi be rufeba tarik’e mama suka nutsa aciki can kasan ruwan wani katon ledane aka nannad’e kamar ball ko tarewarda maheer yayiwa abun yakasa tsayi wuri d’aya cikin k’araji yacewa Mahira tanunawa mama tad’auka domin masu tsaronshi gab sukeda k’arasowa wurin…tana nunawa mama tasaka hannu biyu tareda bismillah tad’auko Amma me tana rikonshi aka fara janta kamar igiyar ruwar zata tafida ita ganin hakan yasa sukayi saurin fitowada ita ta gab’ar ruwan suna fitowa maheer yace tadoka abun ak’asa Idan tayi hakan baze k’ara komawa cikin ruwaba Kuma kowa ze iya k’arasa aikin

 

Hakako tayi domin dagewa tayida iya k’arfinta tadokashi k’asa aitana dokashi itama ana wullata cikin ruwan hakan sukaga anjefata kamar walk’iya kamun maheer yayi wani yunk’urin tuni maheerah tabi bayanta Amma se tamaula ruwan keyida ita sunaneman hallakata dak’arfi gaske Mahira tasamu nasarar cabkota kana tafitoda ita Amma tuni tasuma…seda suka B’ata lokaci sosai wurin ganin sun ceci rayuwarta seda ta farfad’o dudda batadawo normal ba kana suka shiga kiciciniyar walwale wannan sihiri wani irin mird’ewane akamasa wani abun cikin wani hakan sukayita banye abubuwa daga karshe suna Kai karshen kullin sekawai sukaga guntun takalmine dawani Kashi se dunkulin jini da babyn roba mekamada wancan dattijon sak…suna gama bud’ewa maheerah tak’ona kayan.

 

 

Aiko zunbur abban mama dake kwance tin bayan tafiyarsu yamik’e tsaye kamar Wanda aka tsikara duk seda suka bishi da kallo arazane Amma Banda gimbiya halila daketa famar murmushi…shiko rik’e kanshi yayi dake juya Mashi sosai kana yayi baya luuuuu ze Fad’i cikin sauri jalaludeen yataroshi yafad’a jikinshi… d’agowa yayi Yana kallon gimbiya halila kamar zeyi kuka se kawai ta girgizamai Kai alamar karyayi…shiru yayi Yana duban abbe nasu yakai kusan minti 5 ahakan kamun gimbiya halila tacewa mero takawo ruwa ba musu kuwa mero takawo mikawa jalaludeen tayi tana fad’ar kayi addu,a tukunnah kashafa masa a fuska…hakanko akayi bayan yakarb’a yayi addu,ar kamar yadda tace kana yashafa masa a fuska atake yasauke ajiyar zuciya me k’arfi kana yafara bud’e idonshi da salati d’auke abakinshi yabud’e su tarr akan fuskar jalaludeen…yunkurawa yayi zetashi jalaludeen yatemaka masa yatashi kana shiga k’arewa wurin kallo cikin sauri jalaludeen yace abbe.

 

“”Na,am jalal inamuke anan mimukeyi anan? Ina alyasat?

 

“Alhmdllh alhmdllh alhmdllh shine kawai abunda kefitowa daga bakin jalaludeen yabud’e baki zeyi magana kenan su bibibo suka bayyana awurin yanad’auka mama…cikin sauri gimbiya halila tamik’e Wanda sukayi atare itada jalaludeen miyasa meta maheer? Cewar gimbiya halila…karkidamu tajigatane sabida matsalar da kasamu Amma komai lpy insha Allah..to alhmdllh tafad’a tareda bashi wuri ya kwantarda ita… maheerah ce tashiga Basu lbrn abunda yafaru acan dakuma yadda sukayida abunda suka d’auko…shidai jalaludeen inbanda tasbihi ga ubangiji ba,abunda yakeyi…yayinda gimbiya halila tayi musu Adda,a sosai dakuma fatan alkhairi taname jinjinawa kannen nata dasuka kasance bayan sallah nagani☺️

 

 

“”Nisawa tayi tana fad’ar aiki yayi kyau sosai maheer domin abban zaraah yasamu lpy.. dukkansu murmushi sukayi hadda jalaludeen shiko abbe biye kawai yakedasu Yana kallo domin Sam besan inda kalamansu suka nufaba Kuma bayajin hausa garama jalal yad’an ji sabida zamanshi Nigeria

 

Ganin irin kallonda yake musune yasa gimbiya halila fad’ar sannu bawan Allah nasandai dukkanmu Nan baka sannumuba bancin wannan

 

 

Tanuna jalaludeen dake zaune kusanshi d’aga Mata Kai yayi domin da larabci take magana shiyasa yafahimceta… cigaba tayida fad’ar to abunda yafaru gaskiya wannan yarinyar itace silar had’uwarmu dakai tanuna mama dake kwance kana tabashi lbrn tin lokacin da mama ta tahad’u dashi har izuwa kawo yanzu da sihirin yabar jikinshi shera 4 kenan..seda takai karshe kana tace kaji yadda akayi muka sameka har zuwan wannan bawan Allah yace Kai abbanshine..

 

Shiru kawai abbe yayi Yana sauraronta idonshi suncika Tabb da k’walla Yama kasace komai se aikin kallon mama yake

 

 

Jalaludeen kuwa se murmushi yakeyi seda gimbiya halila tace kagaya masa yadda kuka rasashi domin hankalinshi yak’ara kwanciya Nan ko jalaludeen yabashi lbr iya abunda yasani na b’atanshi dakuma tashin hankalin da ahalinsu suka shiga Amma ya boye masa cinwon ammy…awannan Karon kuka sosai abbe keyi bawanda yahanashi domin dukkansu sunsan abunda ciwo sosai arabakada ahalinka natsawon shekaru…ana cikin wannan halinne mama tafarka tana turo baki gaba tana Kiran bibibo

 

 

*SOLDIERS FAMILY* complete ne ga duk me buk’atar complete akwai ak’asa

 

 

 

Murmushi sukayi atare kana bibibo tarik’ata tatashi zaune kamun yace uwar gijiyata abbanki fa yasamu lpy…wani irin k’walalo Ido mama tayi kamun tasaka ihun murna tamik’e aguje taje gun abbe dake zaune Yana kallonta sekawai Tafad’a jikinshi tana abbana kawarkeko? Bazaka Kara ciwoba insha Allah yanzu mikakeso abbana naje nasaka Biba takawoma? Jin yayi shiru Kuma biyi Mata yadda yasaba ba seta d’ago tana dubanshi taga shid’in ma ita yake kallo kunya taji takamata atake Kuma jikinta yayi sanyi data tuna yafa samu lpy kardai ace yamantata janye jikinta tayi daga nashi zata Mike sekawai taji yamaidata Yana shafa bayanta hawaye nazuba a idonshi  godiya yakesan yimata Amma yakasa furta komai se aikin shafa bayanta yakeyi Yana hawaye Koda ba,a bashi lbrn ta ba iya yadda tayi yanzu da,akace yasamu lpy ya,Isa yanuna masa tsananin sonda take masa shiko mizeyiwa wannan yarinya yabiyata aduniya…sunjima ahakan sosai kamun yad’agata Yana fad’ar ngd ngd ngd sosai y’ata Allah yayimiki albarka Allah yabaki ingattacciyar rayuwa Allah yabaki Ni,imar duniya data lahira Allah yabaki miji nagari Wanda zekulada rayuwarki cikin amunci… dukkansu da ameen suka amsa kana wurin ya keceda fira kowana bada lbrn abunda yasani kamun haduwarshi da wani..!

 

 

Dubai

 

Suna kan hanyar zuwa d’aukar mlm Abba yakirasu yace suzo yadawo ance suna nemanshi…to kawai sukace tareda K’arasawa suka d’auko mlm pert d’in ammy sukakaishi inda sukace suhaif da alhusain sukaishi inda ammy zasuje suga Abba…hakanko akayi bayan sunje gun Abba sunjima awurinshi suna tattaunawa bayan sungama kana suka fito kowannen ji yakeyi kamar ancire masa k’aya ajiki ahakan suka Isa pert d’in ammy suka samu mlm nazaune shida su Al Hassan domin yaduba ammy har an mayarda ita d’aki wuri suka samu suka zauna..

 

Kana mlm yashiga yimusu bayi “”agaskiya ciwon mahaifiyarku ba komai bane face babbak’un aljanu sune aka izo Mata Kuma akowacce Rana ta duniya tsafi sukeyi ajikinta domin ba,abuk’atar tawarke Kuma Basu tashi kashetaba ba,ba,abunda zance muku anan illa kudage da addu,a Kuma akwai wasu addu,oi dazan Baku zaku Rika yimatasu da maganin dazan,arika yimata wanka ana shafe mata jikinta sedaifa kusani abune me matuk’ar wahala rabatada way’annan hatsabiban alajanun shiyasa nace kudageda addu,a….nisawa suhaif yayi kana yace shikenan mlm mungode sosai Kuma insha Allah zamuyi yadda kace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected