YA ZA A YI COMPLETE HAUSA NOVEL

YA ZA A YI COMPLETE HAUSA NOVEL

[10/27, 11:35 AM] bintaumarabbale: °°YA ZA A YI❓
*BINTA UMAR ABBALE *
MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION
°°°°°°°

YABO DA GODIYA SU TABBATA GA UBANGIJI MA’DAUKAKIN SARKI.
TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU ‘KARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)

*GARGADI!*
KUSKURE NE MAI GIRMA A ‘DORA MINI LITTAFIN NAN A WATA TASHAR, KO KUMA A KAI FCEBOK KO WATA MANHAJAR BA TARE DA IZININA BA, WANDA YA AIKATA HAKAN NA BAR SHI DA ALLAH MUTUKAR INA DA HAKKI SAI ALLAH YA SAKA MINI.

A TAFIYAR MU TA (GA IRINTA NAN) DA YAWA MAGOYA BAYA BASU SO LABARIN YA ‘KAR’KARE BA TO BA GAJIYA NA YI BA NA TA’KAITA NE DAN GANIN NA ISAR DA SA’KO NA.
AMMA YANZU GA NI NA YI ‘DAMARA NA SHIRYA TSAF DOMIN NA GWANGWAJE KU DA WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA A SAMA.
*YA ZA A YI❓* SUNAN LITTAFIN KAWAI YA ISA YASA MAI KARATU TUNANIN ME ZAI FARU❓ NI MA TAMBAYAR KAINA NAKE WAI SHIN *YA ZA A YI NE❓* ‍♀️ IN SHA ALLAHU NA YI AL’KAWARIN SANAR DAKU YANDA ZA A YI.
KU KASANCE TARE DA NI DOMIN WARWARE MUKU ZARE DA ABAWA.

*ARASHI:*
LITTAFIN YA ZA A YI ‘KIR’KIRARE NE, BA A YI DON A CI ZARAFIN WANI KO WATA BA.
WANDA LABARIN YA YI DAI-DAI RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE.

*GOMBE STATE*
*Area Waziri South Dukku local government*
*MAFARI!*
1&2
Tunda na ji Tokar tana maganar dawowarsa gida na rasa sukuni. Na san kuma shikkenan ni da samun walwala da farinciki har sai ya tafi.
Ban san me yasa muka tsani junan mu ba. kwata-kwata bana ‘kaunarsa duk da kasancewar mu ‘yan uwan juna na jini, amma tsakanin mu kamar Annabi da kafiri! ba ma jituwa kuma duk lokacin da za mu had’u a wani guri sai mun yi rikici! kamar masu ya’ki! Ya zage ni Ya ci mutuncina watarana ya kai hannu ya dake ni duk da ‘karfin ba daya bane amma ina kokarin ramawa domin ba na iya ha’kuri da cizo da yakushi nake kwatar kaina na yi ta kuka ina zaginsa, aikuwa ya sha zubar mini da jinin bakina domin har ha’kora biyu ya fitar mini inda Allah yasa na gefe da gefe ne.
Wannan dalilin yasa na ke bala’in jin haushinsa kuma har yanzu ina kan bakana sai na salwantar masa da wani sashi na jikinsa kamar yanda yasa nayi asarar ha’kora na biyu.

Zaune kawai nake ina tufka da warwara! ta rarrafo tsakar gidan ta fito tana surutai kamar koda yaushe bakinta baya shiru ita kad’ai magana take, idan ba haka ba kuma za ka same ta tana taune-taune! koda kuwa babu komai a bakinta.

Kallonta nayi na ‘bata rai! domin na riga na san irin soyayyar da take tsakaninta dashi, nasan yanzu za ta zo mini da son zuciya to ba zan lamunta ba.

Tasa hannu ta shafa yamulallan gashinta da gabad’aya yake dabaibaye da furfura! ya cukurkud’e! kamar audiga kuma iya tsakiyar kan ne kawai ke da gashi amma gefe da gefe da k’eyar duk sumul kamar ba a ta’ba tsirar gashi a gurin ba, saboda fitina irin tata duk sati sai ta sa ni nayi mata tsifa na wanke mata gashin sa’an nan nayi mata sabon kitso.

Ta kalle ni da za’kin muryarta rad’au kamar ba tsohowa ta ce.” Ma’kiyin ki zai dawo shine ki ka fito tsakar gida ki ka zauna kina k’unci! ko? wai ke Jamila yaushe za ki daina nunawa d’an uwanki kiyy…..Katse ta nayi ta hanyar daga mata hannu da cewa; Kin ga Tokar don Allah ki rabu da ni da maganar wannan d’andaban! ni ina ruwana da dawowarsa, abinda na sani shine yana shiga harkata zan keta masa rashin mutunci, domin wallahi na daina raga masa.”

Ta ja tsaki tare da sa tsinke tana sakace ramuka da kogunan ha’koranta! aikinta kenan sakace! ta ce” To ai gaki gashi nan, tunda kina ganin za ki iya gwada ‘kwanji dashi bisimillah.”

Zuciyata tayi zafi ruwan hawaye ya ciko idona! na ce” Tokar ban san me yasa ki ke fifita Bahago a kaina ba, alhalin duk ke ki ka haifi iyayenmu! a gabanki fa ya zubar mini da hak’ora har biyu, amma baku d’auki mataki ba, babarsa ma har yanzu ba tace komai ba, kodan
mahaifina yana da kawaici da hakuri ya yi muku shiru shiyasa kuke nuna mana wariyar launan fata! Tokar na jima fa da gane ba kya ‘kaunata saboda ba kya son mahaifiyata duk da irin d’awainiya da ‘kaunar Babana yake nuna miki.”
Ina maganar hawaye na gararanba a saman fuskata! na cigaba da cewa” Idan na yi magana ko na nemi k’watar ha’kkina a ce bani da kunya! bani da tarbiya wai shin ya kuke so na yi da rayuwata ne? Tokar ina k’ara fad’a miki wallahi ku ja masa kunne babu ruwansa da ni, ba zan shiga harkasa ba to nima kada ya shiga tawa, idan ya yi mini akuyanci! nima zan nuna masa zara! domin nima na iya ta’addacin sai dai ayi mutuwar kasko tsakanina da shi!

Hankalinta a kwance take kallona tare da cigaba da tsokane! dadashinta da tsinke dake hannunta alhalin duka ha’koran dake bakinta sun zube bai fi biyar suka rage ba, amma kullum cikin sakace! su take! duk sun yi jajawur! da ti’kar! goro!

Ganin ta tsira mini ido tana kallona yasa na yun’kura domin barin gurin zuciyata kamar ta tsage! saboda ‘bacin rai! kafin na kai ga shiga d’akin Kawu Sammani ya shigo gidan dawowarsa kenan daga kasuwa hannunsa rike da leda mai zane! kawai sai ji nayi ta fashe! da kuka! da cewa” Jamila na gaji da wannan rashin arzikin naki kawai kin tasa ni a gaba kina zazzaga mini rashin mutunci! kina so ki kashe ni to ta Allah ba taki ba ehe! ba zan mutu ba sai kwana na ya ‘kare.” Ta kai k’arshen maganar tana goge majinar da ta ziraro mata da hannunta.

Ban damu da maganarta ba domin na san za tayi abinda ya fi haka saboda ganin d’anta ya shigo gidan ta ke wannan maganganun shiyasa kullum gidan yake a rikice! domin ita da kanta take haddasa rigimar ta haifi iyayenmu su uku amma ta ware wad’anda take so a cikinsu kuma tana fifita ‘ya’yansu ciki kuwa har da Bahago wanda take ji dashi kamar ta d’auke shi ta goya.

Kawu Sammani ya san halin mahaifiyarsa sai kawai ya girgiza kansa ya kalle ni a lokacin da nake tsaye a jikin bango ina jiran hukuncin da zai yanke, Cikin lumana ya ce.” Me ki ka yi mata?”
A sanyaye na ce.” Ban yi mata komai ba.”
Ta ce.” Don Ubanki ‘karya nayi miki kenan?”

Shiru nai domin bana so maganar ta yi tsayi!
Ya kalleta a lokacin da take kumfar baki da balolo’ko! duk akan Bahago! Ya ce.” Tokar ya isa haka kiyi hakuri ki bar maganar haka, in sha Allah idan ya dawo zan zaunar dasu nayi musu sulhu.”

Ta ce.” Ai ko ka zaunar dasu wannan mai ‘kirar samudawan ba zata saurareka ba domin bakar zuciya ce da ita kamar kafira! idan ba mugun hali ba, ina ita ina yin gaba da wanda ke fita ruwa! da iska! ya nemo mata abinda zata ci, amma har tana kiransa da d’andaba! wannan kalamar ta yi mini ciwo mutuk’a.” Ta kai k’arshen maganar tana sake goge majinar da take tsiyaya dakalin hancinta, tafi sati biyu tana mura amma ta’ki shan magani! kuma ta’ki daina kwanciya a farin wata. haka ‘ya’yanta suke fama da ita domin muguwar rikitacciya ce, to dukkaninsu lallabata suke domin su rabu lafiya.

Shi dai Kawu Sammani bai ce komai ba ya ajiye mata ledar lemo da ayaba wanda ya siyo mata ya nufi ‘bangaransa yana mamakin rikici irin na mahaifiyarsu, haka suke fama da ita kullum ta Allah, burinsu dai suga sun rabu lafiya.

Kallonta nayi tana ta sosa hancinta nan ta janyo wani tasono mai had’e da majina ta lakace! a jikin bango! sannan ta janyo ledar lemon ta d’auko d’aya da ayaba ta bani. Girgiza kaina nayi tare da yatsine fuskata! can ‘kasan ma’koshi na ce” Tokar ai ni tuntuni nayi sallama da cin abincin hannunki ko wani naga zakiyi wa kyauta mutukar ina gurin sai na hana shi kar’ba! ace mutum kullum hannunsa a cikin hanci! bayan haka kuma idan tayi bayan gida (kashi) sai tace sai tayi tsarki! da kanta gashi ba wani iyawa tayi ba hannunta duk yayi jirwaye! idan nazo zanyi mata tace bata so Allah ya suturta ban isa naga tsaraicinta ba. haka surukanta suke fama da ita da ‘kyar take bari suyi mata wanka! amma kafin hakan akan d’auki sati biyu zuwa uku. sai dai kuma tana da k’ok’arin ibadah! lokacin sallah yanayi zata ja jikinta ta dauro alwala! amma bata bambace! gabas ko’ina kallo take, idan anyi mata magana sai tace ai ko’ina da Allah!
Kallona tayi da fadin.” Me ki ka ce?” Da sauri na girgiza kaina ” Ban ce komai ba kisha kayanki na gode.”
Bakinta ta ta’be da fad’in.”Kinyi wa kanki mai ba’kar zuciyar tsiya” Ba tare da nace mata komai ba na dauki buta na shiga band’aki domin gabatar da uzurin da yake damuna.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected