interstitial
Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*

*Shimfiɗa*

*PAID BOOK*

ƊANƊANO

**Assalamu Alaikum warahmatullah, tadaaaa ga Gureenjo da sabon littafi,salo,labari me kama zuciya.. Ba zan ce wadda baku taɓa gani ba sede in ce ya sha bam-bam da wadda kuka saba gani, Mallaki naki tun kan free pages su ƙare ki sha karatu cikin kwanciyar hankali**

Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata, wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta.

“Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali… Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan ɗaurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke ɗin tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faɗa miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba, idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaɗan ki hana wannan aure!”

Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa
“Na yarda baba Alhj….a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina…! Ko yaya yake… Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni..”
Ta karashe da kuka sossai har tana shiɗewa.

Wani mugun kallo ya watsa mata yace
“ko mutuwa zaki yi se an ɗaura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan ɗin ba son auren tantiyar ƴar iska irin ki yake ba..!”

Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta ƴar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su Haɗa ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi.

Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama’ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe

“Ammi! Baba Alhj basa ƙaunata Ammi, Ammi don Allah kiyi wani abu kar su kasheni tun kwanana be ƙare ba! Ammi wallahi na tsane sa Ammi bana sonsa bana ƙaunarsa, ki tausaya min Ammi..!”
Shafa kanta Ammin take cikin baƙin cikin da yake daskare bisa zuciyarta, in akwai wadda ta tsana a rayuwar nan To mahaifiyar Faizan da Mahaifinshi me ze sa komai na rayuwarta da ahalinta se da umarnin su za’a aiwatar?

Allah kaɗai ya san irin zaman da suke yanzu da mai gidanta duk saboda su, me yasa ne ita bata da ƴanci a nata gidan da mijinta? Me suka fi su? Kuɗi ko suna? Me yasa Sulaiman a ko yaushe umarnin Prof shine gaba da na kowa? Ina soyayyar da Jaddah ke ikirarin tana yiwa Fauziyya ɗin?

“Fauziyya kiyi haƙuri, duk yadda zan yi wurin ganin na hana aiwatuwar wannan aure na yi sede babu nasara sakamakon hakan ma aurena rawa yake, ki daure zuciyarki ki bari ayi auren amma ba zan taɓa yi miki dole ki zauna ko kiyi biyayya ba… Wannan karo ma Aisha tayi nasara a kaina”

Sakin Ammi tayi ta sake mikewa ta fice da gudu, idanunta a rufe suke mafita kawai take nema, sashen Jaddah ta shiga a gigice Sam bata lura da mutanen da suke wurin ba, ta fara cewa

“Zan kashe kaina! Wallahi tallahi zan kashe kaina…. Duk ranar da aka yi Adu’ar aurena da Wannan azzalumin ina me rantsuwa zan mutu! Sede a kai gawata ɗakin sa.. Ku gafarceni Jaddah…”

Natsatsiyar muryar da take bayyana fushi da wani irin ciwo ne ta ratsa kunnuwanta, irin muryannan na no nonsense, muryar da ta tsana fiye da na kowa da komai a duniya, sautin da take jinshi kaman saukar aradu a kunnuwanta da ma gangar jikinta…

“Ka ji ba Baba? Ban taɓa yi muku jayayya ba a rayuwata, ban taɓa sauya fari zuwa baƙi ba idan har ku kuka furta Cewar farin ne, sau ɗaya dae ku dubi Allah karku tilastani yin abunda ba zan iya ba, zan iya shiga wuta aka yi min dole wannan aure saboda ba zan iya adalci tsakanin ta da Fatima ba, above all that baba bana fatan Haɗa jini da fasiƙa…! Idan har aka ɗaura wannan aure an cutar da ni da iyalina…”
Sauƙar gigitaccen mari ne ya hana shi ƙarasawa.

Jajayen idanunshi ya ɗago ya zuba mata na mintuna ba tare da ya iya cewa komai ba, karon farko da wayaunshi kenan da mahaifiyarshi ta sa hannu a kanshi duk akan wannan annoban, miƙewa yayi a zuciye ya fice kaman kububuwa…

“Menene hujjar ki na ƙin wannan aure?”
Jaddah ta jefa mata tambayar karon farko tana kallonta.

Shiru tayi tana kuka sossai don Kalmar fasiƙa da ya jefe ta dashi har tsakiyar zuciyarta take jin zafi da raɗaɗin shi.

“Baki da hujja? To fitar min daga ɗaki”
Kallon ban yarda Jaddahta bace a zaune anan take jefa mata kan ta yi baya baya ta fice da sauri tana kuka.

Dafe kai Jaddah tayi cikin jin ciwon wannan abubuwa da suke faruwa a cikin zuri’ar ta, idanunta ta kai kanshi yayi shiru cikin nazari da tunani, chan ya ɗago ya kalli Jaddah cikin girmamawa yace
“kwarai raina a ɓace yake kuma a ƙuntace hajiya! Ban taɓa yin abunda na muzanta ba irin wannan kab tarihina zuwa matsayin da na taka a yanzu, na kan Haɗa auren maƙota ma su karɓa cikin farin ciki bare na ƴaƴan cikina..”

Shiru ya ɗan yi kan ya kalli Mammi yace
“Ki sanar da ɗanki daga yanzu har a ɗaura auren nan idan na saƙe jin muryarsa da sunan mujadala da auren nan na yafesa har Abada!”

A razane duk suke kallon shi, kwarai ranshi ya ɓaci da wannan lamarin tunda har Baba prof ze iya furta kalma irin wannan.

Miƙewa yayi ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, a maimaikon yayi sashensa se ya nufi sashen ƙaninsa Sulaiman, sama sama yake amsa sannu da matan da suke daga farfajiyar har zuwa harabar na gidan Sulaiman suke mishi har ya isa zuwa parlornshi, da sauri Baba Alhaji da yake shirin cin abinci ya miƙe tsaye yana furta

“Yaya! Ai da ko a waya ka ƙirani ba se ka zo da kanka ba!”

Daga tsayen hannayenshi goye a baya yace cikin natsuwarsa na tsantsan ilimin addini
“Ba buƙatar hakan Sulaiman saboda ina so ka san saƙon me muhimmanci ne, ina so ka sanar da Fauziyya idan har kai ka haifeta na sake jin magana makamancin wadda ta zo dashi yanzu sashen hajiya ka yafeta wa duniya har Abada!”

Da sauri ya ɗaga kai ya kalli yayan nashi zuciyarshi na bugawa, dukda maganan yayi mishi tsauri sede zasu iya kaiwa ko wani mataki domin ganin mutuncinsu be zube ba kaman yadda ƴar wajenshi ta so zubarwa, mutuncin da tun kan a auri mahaifiyarta yake wanzuwa a idanun mutane..

“Kayi hakuri yaya in shaa Allah hakan ba ze sake faruwa ba”

“Allah ya sa!”
Baba prof ya faɗa yana Juyawa ya fice a lokaci ɗaya yana amsa saida safen da Baba Alhajin ke yi mai.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected