Tsutsar Nama Book 2 page 53
 _
_  _
……Hajiya Mammah na ganin Samraah ta wuce da aikar da tai mata ta wani saki ƙayataccen murmushi. Sai kuma tabar kitchen ɗin da sauri. Fita tayi daga sashen baki ɗaya zuwa na Maash. Cikin sanɗa ta leƙa ta window ɗin falon. Kusan abinda ya faru na farko a idonta ya faru. Sai dai ganin Maash zai fita yasa hankalinta tashi. Da sauri tabar wajen, ɗakinta ta koma, ranta a dagule ta rarumi waya tai kiran Rubayya. Bugu biyu kuwa ta ɗaga…
“Gaskiya na gaji Rubayya. Ni fa shiyyasa kikaga sam babu ruwana da wani tsigunne-tsugunnen malaman nan. Gara na tashi da kaina nayi aiki nasan ni nayi sa”.
“Haba hajjajuna relax mana. Mike faruwa irin wannan ɓaɓatu haka ko shaƙar numfashi bakiyi?”.
“Ba dole nayi ɓaɓatu ba. Yaron nan fa yau ma gashi can ya tsallake abincin can bai ciba. Sai ma shirin barin gidan yake”.
“Ita yarinyar tana ina?”
“Mtsoww, oho ma shegiya, ban dai ga ta fito ba daga bedroom ɗin nasa”.
“Fantastic! Ai muna da sauran hope kenan”.
“Ta yaya muke da wani sauran Hope bayan na faɗa miki yama fita a gidan, shegen kamar wani ɗan fashi yayi shigar baƙaƙen kaya yan koransa biye da shi. Wlhy sai nayi maganin shima wancan shegen ɗan masu aikatau ɗin Hayatu yake koma wa oho mas”.
Dariya Rubayya tayi da ga can, tare da faɗin, “Ai abin naki da yawa Hajiyata. Yanzu dai kwantar min da hankalinki. Zuwa zakiyi ki kafa ki tsare ta ko wane hali kada yarinyar tabar sashen nan. Ina kuma turaren daya baki”.
“Mtsoww ke ni ajiye wani batun turare har yanzu banyi ba. Banda rainin wayo taya za’ace saka turare a wuta zai sa wanda ke nesa da gida dawowa koda ba’a Nigeria yake ba”.
“Humm. Aike kinji matsalata da ke gardama. Ke dai ki gwada mana kiga idan bai yi miki abinda yace ɗin ba sai ki faɗi koma minene yazo ranki. Amma dan ALLAH ki kwantar da hankalinki kiyi komai yanda ya kamata daga nan har zuwa safiya idan komai bai farun ba sai musan matakin ɗauka.”
Badan zancen ya shigi Hajiya Mammah ba tayi duk abinda Rubayyan ta faɗa. Dan sashen Maash taje ta kunna turaren wuta. Yana fara hayaƙi tai kiran sunansa, “Awwab duk rintsi ka kwana a gida yau. Kayima yarinyar nan fyaɗe. Ka mata kaca-kaca, fata-fata, yaga-yaga. Kona minti ɗaya kada kaji tausayinta Awwab, karka raga mata”. Ta ƙare maganar tana kokkora hayaƙin da hannu tako wace kusurwa. Sai da ta tabbatar tayi duk yanda malamin yace sannan tayi murmushi da fatan dacewa ta fice.
Koda ta koma sashen nata ba kwanciyar tayi ba. Dakon zaman jiran dawowar Maash tayi tacan balcony ɗin sashenta na upstairs. Duk yanda take jin barci har gyangyaɗi na ɗibarta bata tashi ba a wajen har sai da su Maash suka dawo wajen 1-30. Jitai kamar ta daka tsalle taita ihu dan daɗi. Tana ganin ya shige ciki shi jaɗai ta ƙara sauke ajiyar zuciya. Da alama ɗan koran nashi y sauka a gida kenan. Cikin sauri ta sauka downstairs. Kai tsaye ta can baya ta zagaya cikin garden. Dan windows ɗin Maash na bedroom duk tacan baya suke. Tako ci Sa’a bai rufe ba. Sai dai gaba ɗaya labulolin a sake suke. Cikin dabara ta ɗan janye tana leƙen bedroom ɗin. Maash ta hango yana lulluɓa ma mace blanket, sai da tayi tsamm da ranta ta tabbatar da Samraah ɗince. Jitai kamar ta kurma ihu dan daɗi, amma sai ta kanne, tadai gyara tsaiwa domin ganin yaya wasan zai kaya..
Komai daya faru tun daga ciwon Maash har zuwa hawansa saman gadon akan idanunta ne. Maash na gab da cimma burinsa taji abu yabi takan ƙafarta, firgitar da tayi da jin kamar motse-motsen mutane da gittawarsu ya sata barin wajen cikin rawar jiki. Wannan shine ya hanata ganin ƙarshen faruwar komai. Amma da tabbas taso komai-da-komai sai ta ɗauka a wayarta dan tana son tayi komai da shaida. Amma ko’a yanzu ɗin ma wanda ta ɗauka ya wadatar da ita…
Hummmm
❤️❤️
Hannunsa dake saman lips ɗina na ture, tare da yunƙurawa zan tashi ina faɗin, “To ka tashi min a jiki mana”
A yanayin ƙara shaƙewar muryar tasa dake seizing ya ɗan sake ƙanƙance min idanunsa cikin tsakkiyar nawa, sai kuma ya shiga hura min iskar bakinsa a hankali, babu shiri na lumshe nawa idanun ina haɗiyar numfashi. Cigaba yay da hura min iskar ta saman wuyana har a cikin kunne na, gaba ɗaya naji kamar numfashina zai ɗauke. Bam ma san na sake ƙanƙamesa ba. Sautin fitar murmushinsa naji, tare da fara min magana cikin raɗa a kunnen nawa. “Ba abinda nake ma ƴan hotels ɗin kike buƙata ba kema?”.
Sosai na waro idanuna da suka gama cika taf da hawaye ina ƙoƙarin ture kansa. Amma ko gezau, cike da shagwaɓar da ban san tazo min ba na ce, “Ni yaushe nace, kada kamun sharri. Dan ALLAH ka matsa Ummie nake dafa ma abu a kitchen fa”.
“Kin san da Ummien ai kika kawo kanki nan”.
“Na kawo kaina fa? Wlhy Hajiya Mammah ce ta aiko ni kai kuma dan mungunta ka ɗaureni, ƙilama cocaine ka shaƙa min dan nayi barci.”
Bai amsa min ba, sai wani lumshe idanunsa da yay yana matse fuska alamar da abinda ke damunsa. Gabana ne ya faɗi, saboda tunawa da zancen Mama Balki akan yanayin ciwon da yake shiga akan Ummie, sai nai tunanin ko dan na ambaci sunanta ne. Cikin suɓutar baki na ce, “Baka da lafiya ne?”. Na faɗa cikin rawar murya hawaye na rige-rigen sakko min a guje.
Maimakon amsa min sai ya wani lumshe idanunsa da matso da fuskarsa kan tawa sosai. Idanuna na runtse da sauri ina ƙanƙame jikina tare da kauda fuskar tawa gefe. Sai kawai naji saukar numfashinsa akan wuyana zuwa ƙasan wuyan nawa da cikin kunnen yana shinshinata ta.
“Na shiga uku, dan ALLAH Awwab ka rufa min asiri, wai minene haka kake yi kamar wani mage”. Na faɗa cikin zaburowa a ɗan sauran ƙarfin daya rage min. Gocewa yay daga rankwafowar da yay ya koma gefena. Da alama tanƙwaɓar hannunsa da nayi ne. A zatona na kuɓuta, sai kawai jinai ya yaye bargon gaba ɗaya ya rungumeni tsam a cikin jikinsa har ina numfashi da ƙyar. Cikin kunne ya raɗa min, “Idan na rufa miki asiri ni wazai rufe nawa Samr!”.
Yanda ya ambaci sunan nawa da wani irin salon cire wasalin kowacce harafi yasa jinina yamutsawa gaba ɗaya. Kuka na sake fashe masa da shi. Ina mai jujjuya kaina dake kwance a ƙirjinsa. “Dan ALLAH Awwab ka bari zan cutu”.
“Zan fiki cutuwa idan nayi hakan”.
“Wai dan ALLAH kai baka da tausayi ne? Baka da…..”
“Nace bana son surutu”. Ya faɗa cikin muryar data sake firgita ni, yana sake ƙanƙameni. Ɗif naga hasken cikin gadon ya koma duhu. Mutsu-mutsu na farayi na son ƙwatar kai amma yamin riƙon da ban isa aikata hakan ba. Sai kawai na buɗe baki na fasa masa ƙara. “Gayyato wani nan bazai hana ni karɓar HALAL ɗina ba, dan ina da taurin kai, idan har nace ZANYI, to sai NAYI Samrh” ya ƙare maganar da rufe min baki da nasa. Daga haka bai sake bani wata dama ba koda ta shaƙar numfashi ne cikin sauƙi. Gaba ɗaya ya canja daga wancan Maash ɗin zuwa wanda ban taɓa gani ba. Tunda nake a rayuwata ban taɓa tunanin akwai makamancin irin wannan tashin hankalin na kana ji kana gani ba sai yau. Sam baya jin roƙo, baya jin magiya. Saima sake tabbatar min da shi ɗin mayuncin zaki ne da in ya ɓalle abinda ya fito nema kawai yake farauta. Tun ina iya banbancewa har komai ya ƙwace min daga gangar jiki zuwa fitar numfashi….
Matsanancin firgicin da muka shiga na ganin wanda yasa aka satomu bazai musaltu ba. Dan kuwa ba kowa bane face Maash. Duk da sau ɗaya na taɓa ganinsa a rayuwata hakan bai hanani gane sa ba. Roƙonsa muka dinga yi da magiya amma ko sau ɗaya bai ɗaga kai ya kallemu ba. Sai da ya mula dan kansa kusan mintuna ashirin sannan ya furta, “Su wanene ku?”.
Kasa fahimtar tambayar tasa mukayi, sai da yaronsa ya daka mana tsawa sannan na bada amsa ina nuna Aunty. Nace wannan Yayata ce ni kuma ƙanwatarta ce”.
Shiru bai sake tanka mana ba. Sai yaronsa ne ya tura mana tab da hoto a jiki, cikin tsawa ya ce, “Miye haɗinku da wannan yarinyar?”.
Hoton muka kalla, ba kowa bace face budurwar Mansoor. Kasa bashi amsa mukayi, sai da Maash ɗin da bai sake tankawa ba ya jawo bindiga ya nuna mu batare da yayi magana ba shima. Atake jikinmu ya fara ɓari, kallan kallo muka fara, kafin tuni bakin Aunty ya buɗe ta shiga zayyano bayani akan alaƙarmu da Samraah. Har takai aya babu wanda ya tanka a cikinsu har tsawon wasu mintuna. Miƙewa Maash dako kallonmu bai sake yi ba yayi, sai da yaje tsakkiyar falon batare da ya juyo ba ya furta, “Ka basu Account details su saka min kuɗina. Ka kuma faɗa musu tun kafin na sakasu nadama su janye abinda suke shirin ƙullawa. Ciki harda auren yarinyar wa ɗansu, idan kuma sukayi taurin kai, su kuka da kansu. Dan sai na sakasu dana sani”.
Da ga haka yay ficewarsa batare daya sake ko waiwayo mu ba. Muna ji muna gani muna hawaye yay kiran waya aka kwashe kuɗaɗensu dake account ɗin aunty da wanda ke hannuna. Sannan ya sake tabbatar mana da musan mi mukeyi kafin lokaci ya ƙure mana. Dan Maash baya magana biyu. Akoda yaushe zamu iya ganin jami’an tsaro da ƴan jarida har gidajenmu…
