Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 15
????1??5??
……..“Why kake son mu dinga kasancewa a wannan yanayin ni da kai?. Ina fa ganin girmanka ne matu?a shiyyasa kaga ina barin komai a yanda yake. Please respect your self mana. Kai namiji ne, nima namiji ne kowa ya cigaba da gwada sa’arsa mai rabo sai ya ?auka a cikinmu. Dan har yanzu banga dalilin da zaisa na iya janyewa ?in ba”.
“Haka kace?”.
Murmushi RK ya sakar masa da kashe ido ?aya kawai ya zagayesa ya bar wajen. Hakan ya sake hasala Yazeed matu?a. Tabbas shi ?in mutum ne mai ha?uri da dattako. Amma yana da tsananin kishi akan abinda yake so shiyyasa yake zafafawa akan al’amarin Maanal matu?a. A zuciyarsa yake tunanin dolene ya koyama guy ?in nan hankali, dan haka a daren yau zai wuce Kaduna dan gara ya zauna ayita ta ?are shi da Daddy. Mamma dai ce matsalar zai rumtse ido kawai komai ma ya faru daga baya yasan zata sakko ta yafe masa…..
Kiran daya shigo masa a wayane ya katse tunaninsa. Ganin ?anwarsa Badiyya ce kamar zai share sai kuma dai ya ?aga. Yana kai wayar kunnensa ya janye da sauri saboda abinda ta sanar masa.. Yana sauke wayar daga kunnensa sai kuma ga text massage ?in Ammie itama ya shigo masa. Ai bai tsaya sauraren komai ba yabar asibitin……
_____________
“Wai Daddyn Yazeed mikake nufi da ni ne a gidan nan? Katafi kai da matanka holewarku bance komai ba, ka dawo ranar girkina kace baka bu?atar komai daga gareni. Na zuba maka ido nan ma, washe gari Basariyya tai girki ita jiyama haka. Yau kuma ?ar sonka ta amsa”.
Idan kujerun dake falon sun motsa Alhaji Usman ya motsa kenan. Tamkar ma bai san da zaman Hajiya Yaya a falon ba yake kallon labaransa yana shan fruits da Ammie ta ha?o masa. Hakan ne ya sake sakata fusata, cikin matu?ar ?acin rai ta ja remote ?in dake a Centre table ta kashe tvn gaba ?aya. Karo na farko ya juyo ya kalleta fuskarsa a matu?ar ha?e. Itama kallon nasa take tana huci.
“Sadiyya bar falon nan kafin ranki yafi haka ?aci”. Har cikin ranta taji tsoron fitar kakkausar muryarsa. Amma sai ta dake dan gara dai ayita ta ?are. Itama a fusacen ta ce, “Babu inda zanje wlhy. Dan nifa na gaji da abinda ake min a gidan nan. Ubana ya dasa inuwa wasu banzaye suzo su zagayeta domin sha suna min gadara.”
“Hummm”.
Ya fa?a kawai yana mi?ewa. Bedroom ?insa ya shige tare da rufo ?ofar ya barta a falo tana jidali ita ka?ai. Haka dama yake mata, ita kuma sai take ?auka kamar tsoronta yake ji ko tafi ?arfinsa ne. Bata san yana hakan bane kawai saboda wani dalilinsa daban, amma badan gorin da take masa ba akoda yaushe. Tsautsayi rabon fa?an nan ya koma kan Ammie sai gata ta shigo sashen batare da tasan Hajiya Yaya na nan ba. Aiko ina wuta Hajiya Yaya ta saka Ammie, nanfa ta shiga mata gori da cin mutunci. Ita dai Ammie komai batace da ita ba ta ajiye basket ?in hannunta dake ?auke da kayan abincin maigidan a saman d/table. Rashin tankawar da batai ba itama sai ya sake fusata Hajiya Yaya, a matu?ar zafafe ta nufi d/table ?in da niyyar kifar da kayan abincin Ammie ta tare tana girgiza mata kai.
“Kiyi ha?uri Hajiya kar kiyi haka dan ALLAH. Koba komai shi ?in abincine, yana da darajar da wula?antashi kuskurene takowace irin fuska”.
“To mama Asiya shawara kike bani ko umarni?”
“Babu ko ?aya da nake baki a ciki kiyi ha?uri”.
“An?i ayi ha?urin munafuka kawai, kullum sum-sum ita a dole ta ALLAH amma dafinki yafi na ba?in kumurcin maciji. Kin mallake min miji da bin bokaye, kin cika mana gida da agololi har kina shirin ganin kin mannawa ?ana. Wlhy Asiya sai naga bayanki a gidan nan”.
“Idan ta juya ba…..”
Alhaji Usman daya fito ya fa?a a zafafe. Juyowa sukai su duka suna kallonsa. Fuskarsa a ?aure ya cigaba da fa?in, “Idan ta juya kam zakiga bayanta Sadiyya. Amma kiga bayanta akan zama dani har gaban abada bazakiga hakan ba da iznin UBANGIJI. Asiya ajiye abinci, idan kin isa dan ALLAH ki zubar da shi ni kuma wlhy yau sai na baki mamaki irin wanda baki ta?a zato ko tsammani ba. Ke Sadiyya bafa wai ina tsoronki bane a gidan nan. Karki ?ureni a wannan karon wlhy idan ba hakaba zakiyi matu?ar dana sani.”
“Dana sani na nawa kuma ai nayi dana sani tun daga randa na amince na aureka….” sai kuma ta fashe da kuka “Kai dai burinka kullum ka wula?antani a ?asan ?anwar bayana koma nace sa’ar ?ana ko, shike nan ga gidan nan na bar maka, ka kwa?ata ka cinye dan ALLAH” fuuuu ta fice daga falon. Tsaki yaja kawai tare da juyawa zai koma bedroom ?insa. Hankalin Ammie ne ya tashi, cikin sauri tabi bayansa, kusan a tare suka shigo bedroom. Jin yanda ta fa?o masa ya sashi juyowa yana kallonta.
“Dan ALLAH ka bita karta tafi ?in da gaske, na ro?eka Abban Hameed. Bana fatan kowacce matsala ta kasance tsakaninka da matanka a dalilin…..”
“Asia!”.
Ya fa?a cikin katseta. Kanta ta shiga girgiza masa sai ga hawaye. Zata sake magana kawai ya jawota jikinsa ya rungumeta. Sosai take bashi tausayi, mace ce mai ha?uri da juriya akan komai na rayuwa. Tana da kawaici da saurin sallamawa koda abu zai cutar da itane ko zuri’arta. Duk abinda kaga ta masa musu a kai to ka duba wannan abun kuwa. Komai yace ita mai biyayya ce a gareshi ko bai dace da ita ba. Wannan halayen nata ne suka mamayesa cikin ?an?anin lokaci yake jinta ?ololuwa a saman matan da ya aura tun yana da jajayen sawunsa. Hanata duk wata damar sake magana yayi, ba kuma ta sake yi ?in ba ta ha?ura saboda ita ?in mai biyayyace a garesa. Fitowarsu falo babu jimawa tana zuba masa abinci sai ga Asalamiyya ta shigo tana kuka ita da Basirah.
“Daddy dan ALLAH ka kazo ka hana Mamma tafiya. Gata can ta ha?a kaya zuwa mota zata tafi Daddy”.
A birkice Ammie ke kallonsu, sai kuma ta yun?ura jikinta na rawa zata nufesu. Cikin bada umarni Daddy da tun kallo ?aya da yay ma su Asalamiyyar bai sake ba ya dakatar da ita. “Asia koma ki zauna”.
Kallonsa Ammie tai kamar zata fashe da kuka. “Daddyn Hameed kana fa jin abinda suke fa?a”.
“Cigaba da zuba min abinci nace. Ku kuma ku bar falon nan!!!”. Ya ?are maganar a tsawace. Zabura sukai saboda tsawar ta shigesu. Har rige-rigen fita suke daga fallon. Kallonsa Ammie ta sake yi zatai magana ya ?aga mata hannu. Dole tai shiru ta cigaba da zuba masa abincin hannunta sai rawa yake. Tsaf yake kallon yanda hannun nata ke rawa amma sai bai tanka ba. Tana gama zuba masa abincin yaja ya fara ci hankalinsa kwance.. Abu ya ishi Ammie ta rasa ina zata kama, sai kallon Daddy kawai take. Can dai ta jawo wayarta ta shiga rubutama Yazeed text massage…..
______________?
Yau da wuri Nene ta dawo asibitin. Dan haka ta kora su Amaal gida suma saboda mijinta daya shigo Abuja. Daga nan ma asibiti da yazo ya duba Maanal ?aukar Amal ?in yay suka wuce masaukinsa. Itama Shahidah da mijinta yazo sai suka wuce kawai. Hakan yasa Maanal ta kasance daga ita dai Nene a ?akin. Sai kuma duk ka?aici ya isheta. Dan Nene da zaran tayi sallar isha’i zakaga ta fara gyangya?i abinta. Gashi babu waya a hannun Maanal ?in, tana Kaduna aka barta, bakuma a kawo mataba har yanzu. Shiyyasa ma taima Shahidah maganar a sayo mata kayan zane-zanen ta dan ta iya sosai, shine Yazeed yaji ya hana Shahidah siyowa shi ya sayo mata. Tun ?azun daya kawo mata su ta ajiye bata sake bi takansu ba. Sai yanzu ta jawo ledan ta fiffito da su. Komai da take bu?ata akwai, harma da wanda batace a sayo ba ya sayo. Dan haka sai ta gyara zama kawai ta fara zanenta dan shine hubby nata tun tana yarinya. Maanal ta masifar iya zane ta yanda idan ta zana abu sai ma ka ?auka ba itace ta zana ?in ba. Da farko ?akin jiyyar tata ta fara zanawa harda Nene dake zaune a kujera tana famar gyangya?i, sai ita kanta a yanayin da take zaune. Koda ta gama taga komai ya mata sai ta tsinta kanta kuma da fara zana agogo. Abinda ta jima batayiba a rayuwar zanenta kenan. Ta zana guda biyu tana akan na uku RK da Doctor Ranjet suka shigo ?akin. Firgigit Nene ta farka, yayinda Maanal tai ?o?arin rufe zanen nata amma sai caraf RK ya rikesa.
“Woow!, this is amazing”. Ya fa?a yana kallon zanen cike da matukar mamaki. Sai kuma ya kalleta. “Dan ALLAH da gaske kece kikayi Baby?”.
Kafin ma Maanal ta bada amsa Nene ta cafe cikin ta?e baki. “Yo in dai Manaalu ce ai baka rabata da zanen aljanai Rafeequ. Tun tana yarinya uwar tayi tayi amma ina harma an barta taitayi itace zata ?are da mafarkinsu ai ba wani ba”.
“Nene ai abune mai ?yau wannan ?in…..”
“?an nan a al’adar yahudu da nasara ba. Amma mudai a musulunce banjin cewar abune mai ?yau duk da ni ?in ba malama bace”.
Dariya RK yayi, sai kuma ya mi?ama Nenen zanen yana fa?in, “Amma Nene kinyi fa ?yau a wajen nan kamar wata sarauniya a kujera”.
Ba ?aramin zare ido Nene tayi ba tana kallon kanta an zane ras harda yanayin atamfarta. Duka ta kaima Maanal itako ta kauce tana ?ara ?ata fuska. Aiko ta shiga zazzaga jaraba shi dai RK da Dr Ranjet na dariya abinsu. Manaal dai ta miskile fuska kamar ba ita tai tsiyar ba. Sai da Nene tayi mai isarta sannan ta fice dan idan anzo duba Maanal ?in fita takeyi. Bayan fitar Nene Dr Ranjet na duba Maanal RK daya kasa ajiye zanen ya dubi Maanal cikin serious ya ce, “Amma basirar nan naki bai kamata ya tafi a banza ba kawai, yana da ?yau mutane su amfana da shi”.
“Kamar ya?”.
Ta fa?a a ?asan ma?oshi. Bai damu ba, dan zuwa yanzu ya sake fahimtar miskilancinta mai lasisi ne.
“Akwai Companyn da nasan suna matu?ar bu?atar aiki da mai irin wannan basirar taki”.
A da?ile ta furta, “Ba bu?ata”.
Cikin ?an girgiza kansa ya ce, “Wlhy seriously Baby akwai companyn da zakiyi wannan aikin fa kuma anan Abuja ne, Please kada kice a’a dan ko kina gida zaki iya musu aiki ma”.
Rasama abinda zata cemasa tayi, dan yanda ya wani marairaice fuska ya tsareta da manyan idanunsa sai ta ji ta kasa furta komai. Dr Ranjet ne ya saka baki a zancen nasu, “He is telling you the truth my patient.. Ko game da ciwonki idan kin samu abinda zai dinga maidaki busy zaisa ki rage saka damuwar abubuwa a ranki da har zai dinga yawan tashi akai-akai”.
Shiru kamar bazatace komai ba. Sai zuwa can ta sauke ajiyar zuciya tana ?an girgiza kanta. “Su Ammie bazasu amince ba ne. Kadai ji abinda Nene ta fa?a ai”.
“In dai har kin amince zakiyin ki barni dasu kawai”.
“Mi zakace musu?”.
“Ke dai kawai ki amince zaki ji ai”.
“Zanyi tunani”.
Ta fa?a a ta?aice tana zamewa ta kwanta. Bai sake magana ba shima sai ?aukar hoton zanen da yay a cikin wayarsa kawai. Bayan fitarsu kafin barci yay awon gaba da Maanal tai zurfi matu?a a tunanin zancen RK ?in da Dr Ranjet…..
