Ajiya A Duhu BOOK 1 Na Billyn Abdul

Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 93

??9??3??

______________

………Washe gari kamar yanda AA ya fa?a ya bar gidan batare da sanin kowa ba. Yayinda Abah ya samu kira daga baba Sardauna akan batun nemawa Rafeeq aure da sukai jiya a Kaduna. Tare da batun hukuncin da suka yanke akan AA da Najeeb suma. Dan haka a weekend ?in da za’a shiga za’ai taron family na gaggawa. Duk da zuciyar Abah ta girgiza matu?a haka ya danne ya amsa da to, yayi kuma ALLAH ya sanya albarka. Baba na yanke kiran ya wani zube a kujera yana ambaton sunan ALLAH. A kuma dai-dai nan Oum ta shigo ta samesa tana hawaye da waya a hannu da alama itama dai ta samu batun kai ku?in Rafeeq ?in gidan su Maanal kenan.
“Gadanga ka gani ko, kaga abinda naketa son ka fahimta game da al’amarin nan ka?i ko. Ni Rafeeq zaima haka ya zagaye yaje yasa a nema masa auren Maanal? Auren Maanal fa, yarinyar da Ajwaad ke matu?ar so…..”
“So?!!”..
Abah ya katseta a fusace yana mata wani irin kallo. Cikin zafin rai ta cigaba da fa?in, “So kike magana Fateema? To wane irin so Ajwaad kema Maanal? Lokaci yayi da zaki daina son kanki da yawa saboda soyayyar ?anki ta rufe miki idanu. Shin idan Rafeeq baisa an nema masa auren Maanal ba yaya kuke son yay muku? Ki gaya min shi Ajwaad ?in bai san akwai ala?a tsakanin Maanal da Rafeeq bane? Tun a farko miyyasa bai ?auki matakin nuna masa yana sonta ba? Girman kai! Ko tsabar ya rainama mutane wayau ne? Ko kuwa ita Maanal ?in bata san ciwon kanta bane? To wlhy bari kiji, kodai ku kama kanku ke da ?anki, kokuma ku ha?u da fushina. Kuma wannan ya zama garga?i na ?arshe da zaki sake zuwa min da wannan zancen. Kuma shima na bashi kwana uku kacal ya sanar da wadda yake so dan cikin weekend za’ai family meeting, idan ba hakaba duk Wadda aka za?a masa wlhy, wlhy dole ya aura. Na gaji da case ?in Ajwaad a gidan nan tunda bai san ciwon kansa ba, shi ka?ai bazai cigaba da bani ciwon kan da ?an uwansa dake manya basa bani ba. Ke kuma kina biye masa saboda sonsa ya rufe miki ido.”
Ya tashi fuuu ya fice daga falon ma gaba ?aya. Wasu irin hawaye masu ra?a?i da zafi ne suka shiga sakkoma Oum da gudu, ga jiri na neman zubar da ita a ?asa. Babu shiri takai zaune. Hayaniya take jiyowa kamar a gidan, jiki na rawa ta mi?e ko ganin gabanta batayi ma da ?yau ta fito tana faman ha?a hanya….
“Naga dai ya fito da jakka har ya saka a mota tun bayan dawowarku sallar asuba. Sai kuma ya sake cirewa ya ?auka yazo ya fita da ?afa. Amma wlhy ban yi tunanin akwai matsala ba duk da na fahimci ransa a ?ace yake dan ko gaisuwata ma bai amsa ba.”
Wannan furucin kawai Oum ta iya ji daga bakin maigadi sanda ta fito daga haka ta silale a wajen. Sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti su Fawzan zagaye da ita. Ganin ta bu?e idanu duk sukai kanta, Babban Yaya da Fawzan na gefe da gefenta, a kallo ?aya zakai musu ka fahimci sunyi kuka, dan idanun ?an maza duk ya ka?e. Hannayenta dake cikin nasu ta ?ara dam?ewa, sai hawaye sharrr, muryarta na rawa ta ce, “Fadeel Ajwaad, da gaske Ajwaad yabar gida?”.
Kai kawai babban yaya ya du?ar, hawaye na ciko masa idanu dan bai san amsar da zai bata ba. Sai ta juya ga Fawzan, shiko bashi da ?arfin zuciya irin tasu, sai hawaye sharrr, ?o?arin cire hannunsa yay daga cikin nata amma ta sake dam?esa. “Fawzan kuka kake kaima. Kodai na rasa Ajwaad ne, dan ALLAH ku gaya min.” sai kuma ta shiga yun?urin tashi zaune. Da sauri suka maidata suka kwantar. Abah dake ta ?o?arin danne nashi tashin hankalin ya matso kusa da ita sosai ya zauna, cikin muryar lallashi ya ce, “Fateema ki kwantar da hankalinki dan ALLAH. Ajwaad fa ba ?aramin yaron da kike goyawa bane har yanzu. Karki manta shekara ?ai-?ai har talatin ne da shi da ?oriya. Duk ma inda yaje zai dawo….”
Kuka Oum ta sake fashewa da shi tana faman girgiza kai. “Dan ALLAH kada kaimin haka Gadanga, ka dawo min da yarona. Kuma kun san Ajwaad nada lalura kada yaje wani waje ya shiga matsala. Wlhy bazan yafe muku ba bazan kuma yafema kaina ba….”
Kallo ?aya yay mata ya kauda kansa gefe. Fin minti ?aya sannan ya sake kallonta, “Nace ki kwantar da hankalinki, in sha ALLAHU a yau zai dawo gida, dan na saka a binciko min duk ma inda yake ko ?asar nan bai isa bari ba a yanzu dan na saka an dakatar da komai nasa daga aiki, hatta account ?insa”.
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya Oum ta sauke. Yayinda Mamy da takaici ya cika ta ta?e baki a kaikaice. Ita har mamakin ?arfin halin Oum nan take a ranta, mtsoww wai su za’aima pretending. A zahiri kuwa itama matsawa tai kusa da gadon Oum ?in ta fara lallashinta….

__________?

A Kaduna kuwa bayan wucewar ba?i Daddy ya kira Ammie a waya, dai-dai nan itama Nene ta iso. A tare suka nufi sashen Daddy, inda yake tare da ?a?an Nene uku. Sosai Ammie tayi mamakin taron, amma sai ta danne suka gaisa. Babu wani ?oye-?oye ko jan zance babban ?an Nene Yaya Nuhu ya mata bayanin komai. Duk da jin al’amarin kamar daga sama taji sanyi a ranta, har bata san sanda ta saki ajiyar zuciya ba. Sai dai ?asan ranta wani kalar abu mai nauyi take ji. Godiya ta dingama Daddy saboda fahimtarta da yayi ya janye batun Yazeed cikin sau?i haka. Gefe kuma tanama Maanal addu’a da fatan ALLAH yasa Rafeeq ya zama sanadin kwaranyewar damuwarta. Yasa kuma iyakar wahalarta kenan. Sun tattauna sosai game da tsaida bikin sati uku kawai da akayi, dan hatta da sadaki sun ajiye abinsu. Dan haka dai babu zama shiri kawai ya kamata a fara…
A waya Daddy ya kira Maanal da Shahidah da Amaal suma. Shi da yaran Nene sukai musu bayani. Da ?arfi Maanal ta rumtse idanunta, cikin jarumta ta shiga kokawa da zuciyarta, yayinda take ambaton sunayen ALLAH har ta samu nutsuwar da take bu?ata. Ta kuma tunatar da kanta hakan shine dai-dai, shine kuma zai bata masalaha da kwanciyar hankali a wannan ga?ar. Batace komai ba dai a gabansu, hakan kuma na nufin nuna alkunya da kowa yay zato. Sai dai hankalin Shahidah da Amaal harma da Ammie na kanta. Koda suka dawo sashen duk motsinta na a idonsu, amma a mamakinsu bata nuna wani reaction ba sam. Saima a mamakinsu yanda ta ?an warware daga kwanciya ciwon kwana biyun nan da take ciki tayi. Sai duk suka cigaba da mata addu’a a zukatansu, duk da ?asan ransu na jin tausayinta saboda sanin har yanzu tana son Ajwaad. To amma tunda shi bai nuna yanayi ba har yanzu basu da wani dalilin damuwa da son ganin sai ta aureshi ai…
Washe gari suka shirya suka koma Abuja, suka bar Nene da Ammie da fara tsara shirin biki. Koda suka iso Abuja ma duk motsin Maanal a idon Shahidah ne, sai dai har suka kwanta bataga wani damuwa a tattare da ita ba. Washe gari kuma safiyar litinin, sukai shirin office yara makaranta suka wuce. Shahidahn da kanta ta ajiye Maanal a kamfani, ita kuma ta wuce nata aikin. Yau kam a kallo ?aya su Zaharadeen suka fahimci Maanal ?in a Manaal ?inta take. Dan tun daga gaisuwa ko Yaqub bata sake kulawa ba ta shiga ayyukanta. Lokacin tashi kuma nayi tana a ?an farko na barin kamfanin. Washe gari ma haka tai musu, bata shiga sabgar kowa da komai, aikinta kawai ke kawota. Ko’a zaman meeting da sukai sau biyu dan kamfani na shirin fitar da agogon data zana ga ?an kasuwa a dakenta take. Sai kuma a meeting ?in taji cewar CEO yayi tafiya, dan AS ne yay dukkan zaman a madadinsa. Batabi takan zancen ba balle ta nuna ya dame ta…

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected