Ajiya A Duhu BOOK 1 Na Billyn Abdul

Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 17

????1??7??

…….Sai da suka gama gaisawa da Shahidah sannan ta ?an kallesa ta ce, “Yaya Yazeed ina yini”.
Sai da yaja kusan minti ?aya kafin ya amsa da, “Lafiya lau. Yaya jikin naki?”.
“Alhamdullahi”.
“Masha ALLAH”. Ya fa?a yana maida kallonsa ga Shahidah. “Shine aka sallameku Shahidah ban sani ba. Sai da naje asibitin yanzu akace kuna gida”.
“Kayi ha?uri Yaya Yazeed anyi kuskure kam. Amma banyi tunanin zaka dawo yau bane, azatona kuma kasan da sallamar ne ma wlhy. Tunda muma munje kai musu breakfast Nene ke sanar mana ai doctor yace zai sallemeta yau, da daddare yake sanar musu.”
“ALLAH ya ?ara lafiya to, ya kuma kiyaye gaba. Ina su Nenen?”.
“Nene ai yanzu na tabbata suna gab da shiga Kaduna. Mijin Amal ne ya wuce dasu gaba ?aya”.
“Kai da sauri haka?. Ita Nene ko ?an hutawa bazatayi ba”.
“Aikam bazata zauna ba. A hakama dan zaman asibiti ne. Yau kam muna dawowa tace bafa zata sake kwana a garin nan ba”.
Murmushi kawai yay da fa?in, “Shike nan zan sameta har gida ai. To kema sai ki shirya mu wuce da safe ko, tunda yanzu yamma dai tayi kam”. Ya ?are maganar idonsa akan Maanal.
“Ni Ammie tace ai na zauna anan”.
“Anan kuma? To saboda mi?”.
Shahidah ce ta bashi amsa da, “Bana zaton wani abune gaskiya. Inaga dai tana son ta ?an ?ara murmurewa ne dan suma likitocin sunyi garga?i sosai akan ta huta a waje mai ?arancin jama’a da hayaniya. Amma tana ?ara murmurewa zata dawo Yaya Yazeed”.
Badan ya gamsu da bayanin Shahidahn ba ya ce, “Okay shike nan ALLAH yasa kaffara ne. Nima dai ina nan Abujan har zuwa jibi in sha ALLAHU, dan akwai abinda zanyi”.
“ALLAH ya taimaka ya bada nasara”. Shahidah ta fa?a cike da girmamawa. Dan suna matu?ar giramam yazeed, koba komai suma yana girmama musu Ammien su. Su kansu yana mutuntasu, dan bazasuce ya ta?a musu wani abu na ashsha ba tun daga zamansu gidansu har zuwa aurensu. Hasalima a auren nasu ya zame musu tamkar babban yaya ne a komai. Tashi tai ta bar musu falon. Hakan yasa shi tashi ya koma kujerar kusa da Maanal shima. Cike da kulawa murya can ?asa ya ce, “Baki jin komai dai zuwa yanzu?”.
Kanta ta jinjina masa alamar eh.
“Alhamdullahi haka ake so ai. Nasan kece kikacema Ammie baki son komawa KD ko?”.
Cikin marairaice fuska kamar zatai kuka ta ce, “Ni ALLAH babu ruwana.”
Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya ?an murmusa tare da du?o da kansa ka?an murya ?asa-?asa ya furta, “Adana shagwa?ar nan ba yanzu ba”.
Kanta ta du?ar ziciyarta na gudu da sauri-sauri a ?irjinta kamar zata fito waje. Sai kuma ta yun?ura zata tashi. Cikin bada umarni ya ce, “Koma ki zauna”. Babu yanda ta iya dole ta koma ta zauna ?in tana ?ata fuska….

_______________?

“Da alama wannan karon mijinki yana son nai matu?ar cin mutuncinsa Sadiyya. Ki taho gida tsahon kwanaki goma amma bai biyo bayanki ba saboda yana son nuna min iyakata. Ban san yaushe Usman ya fara maida kansa sakarai a gidansa ba. Ace mace ke juyaka yarinya ?arama”.
Hawaye Hajiya Yaya ta sake matsowa tare da du?ar da kai kamar ta ALLAH. Muryarta na rawa ta ce, “Baba wlhy yamafi yanda kake zatonsa a yanzu. Ni shiyyasa ma nace kawai kasashi ya sakeni na gaji da wannan zaman ?uncin, ai ba haka mukai da shi ba. Shi da kansa yace min duk macen da zai kawo gidan nan sai dai ta kasance a ?ar?ashin ikona da umarnina. Amma duk ya manta da wannan al?awuran da girmana agaban ?a?ana da matansa yake tozartani. Wai har yake iya gaya min sai dai matarsa idan ta juya naga bayanta amma ba’a zaman gidansa ba, wai ni Usman ke tarema mace fa?a a gabana Baba”. Ta fashe da kuka.
“Kinga ya isa kukan haka kinji, barni da shi ai nasan maganinsa. Shi kuma Yazeedu daketa kai kawon ki koma saboda baida kishin uwarsa shima zan gyara masa zama. Share hawayenki abinki zakiga matakin dazan ?auka jeki kwanta”.
Kai Hajiya Yaya ta jinjina tana mi?ewa hannunta a saman ido tana share hawaye kamar wadda akacema baban ne ya mutu. Sai da ta gama ficewa mahaifiyarta dake zaune a falon bata tofa ko a ba a maganar tasu ta nisa a hankali. Tsohuwar kirki mara yawan son hayaniya kenan. Idanunta akan Baba ta ce, “Nikam da zakaji shawarata dattijo da baka goya bayan Sadiyya ba a wannan karon. Kai kanka kasan halin yarinyar nan sarai da abinda zata iya. Tunda kaga kuma Usman ya watsar da ita a wannan karon wlhy ba banza ba. Dan haka ka kirashi cikin dattako ka zaunar dasu su duka kaji bakin kowa. Idan ta kama ma can gidan nasa zakaje ka tasata gaba ka ha?asu har abokan zaman nata. Karfa dan ka raini Usman ya zama kana tauye masa hakki akan ?ar da ka haifa.”
“Ai ke kinji matsalarki, idan har abu zai taso akan yaran nan sai kin nuna ban iya ba ke sarkin tawakkali da gaskiya ko”.
“Ba haka bane Dattijo. Masu iya maganafa sunce kaso naka duniya ta ?isa, ka ?isa duniya ta soshi. Usman na maka matu?ar biyyar da kosu ?a?an da ka haifa ba kowa ke maka irinta ba. To bai kamata a cigaba da ?as?antar da shi ba akan abinda ya isa da shi. Wannan fa rayuwar aurensu ce. Kuma shine shugaba a gidan, yin kutse a al’amarin kamar ?as?antar da shi ne. Dan ALLAH kada ka biyema yaran nan ana ganin ka da kima da mutunci irin na uba kuma shugaba”.
Shiru yay na kusan minti biyu, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya. “Hakane kuma Adama nagode da tunatarwa. In sha ALLAHU gobe zan tasata gaba muje gidan. Sai dai ance min shi Usman ?in baya ?asar, amma dai inada tabbacin kamar yau ne da dare zai dawo”.
“To Alhmdllh gobe idan ALLAH ya kaimu ?in sai kuje, ALLAH ya ta?aita al’amarin kuma ya daidaita su”.
“To Amin ya rabbi. Yarane sai addu’a kawai yanzu, sun maida aure wasan yara”……

__________?

Isowar dare Daddy da Hajiya Basariyya sukai ma gidan. Tafiyar kwana goma har sunyi fresh abinsu. Babu wanda yasan da dawowar tasu, dan ita Ammie ma harta kwanta abinta. Cikin barci taji wayarta na ?ara. Da ?yar ta bu?e ido ta jawota dan ta manta ne ma bata kashe ba. ?agawa tai takai kunne tare da sallama. Sai dai Muryar wanda ya amsa mata da umarnin daya bata ya sata watsakkewa sai kuma ta tashi zaune. Jin abin tai kamar mafarki, amma dai ta mi?e ta ?auka dogon hijjab ta saka sannan ta nufi kitchen. Tea ?in daya bu?ata ta ha?a masa. Sai ta ha?a da ?an snacks da fruits da bata rabo da su. Haka ta fito gidan shiru alamar kowa ya kwanta ta nufi sashen maigidan. Takai hannu zatai knocking ta tsaya cak sakamakon jin muryar Hajiya Basariyya na tashi a sama cikin fa?a…
“To amma dare yayi ai, ?arfe nawa yanzu da zaka ?aga waya ka kirata wai ta kawo maka abu. Ni banda hannune ko abinda zata kawo makan banda shi a sashena? Randa kuka dawo Abuja wayasan kun dawo ba sai tashi mukai muka ganku a gidan nan ba. Sai ni daka raina. Wai mi Asiya tafimu dashi ne? Mi take dashi na mata da mu bamu da shi da kake son ganin ka fifitata a kammu?!!…….”
“Badariyya wai kina da hankali kuwa. Baki ganin dare yayi zaki zo kina min ihu a kaina. Da kike maganar miyasa zan kirata ta kawo min abu ke da kika dawo daga tafiya mizaki bani? Sannan batun fin sauran mata da kike sai yanzu kika san Asia tafi sauran mata ashe. To lallai kin makaro da kika kasa fahimtar hakan tun tuni. Ita da na saka kika bini a ranar girkinta kinji tayi wani ?orafi ne. Kuma randa muka dawo Abuja ni Asia bata kwana a sashen nan ba, idan ma ta kwana ai matatace. Dan haka ki fice min anan shasha kawai tana girma bata san ta girma ?in ba”.
“Ni ce shashashar Daddy Huznah?”.
Banza yay mata bai tanka ba. Sai maida hankalinsa yay a kiran Ammie. Da sauri ta danne wayar gudun kartai ?ara. Sai kuma ta daure tai knocking ?ofar. Umarnin shiga ya bata. Koda ta shigo kai tsaye a Centre table ta ajiye tray ?in, sai kuma ta shiga gaishesu su duka a tare da yimusu barka da dawowa. Daddy ne kawai ya amsa mata. Zata juya tabar falon ya katse hanzarin ta. “Ina zaki kuma”.
Juyowa tai ta kallesa. “Zanje na kwanta ne, kuma ku samu ku ?an rintsa ku huta gajiya ko”.
“Dawo ai anan zaki kwana”.
“Anan kuma Daddyn Hameed amma ai….”
Cikin katseta ya ?aga mata hannu. Dole ta ha?iye abinda take son fa?ar. Cikin ?acin rai Hajiya Basariyya taja akwatinta da hand bag ta fice a sashen tana jan tsaki. Da kallo Ammie ta bita harta gama ficewa. Tai wani kalar masifar bugo ?ofar har sai da Ammie ta zabura. Cikin sanyin jiki ta maida dubanta ga Daddy dake ?o?arin fara shan shayinsa hankali kwance. “Daddyn Hameed dan ALLAH….”
“Asia! Kin san bana son jan zance ko!”.
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke kawai, badan taso ba tabi umarninsa a yanda yake bu?ata…….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected