Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 35
????3??5??
……..Sosai zuciyar RK ke yin kaikawo a ?irjinsa matu?a akan wannan al’amari. Ba komai ya kawo hakan ba mamakin Maanal da AA da koda wasa basu ta?a nuna masa sun san juna ba. Sannan miyyasa AA ?in bai sanar da Oum fara aikin Maanal a companyn sa ba kusan sati uku kenan. Ko shima dai bai san Maanal ?in bane? Ala?ar iya Oum ?in ce kawai da su Maanal ?in?. Zuciyarsa na ?o?arin gamsuwa da hakan sai ga sallamar yayan AA ?in, da’alama ma yanzu ya shigo gidan daga wajen aiki.
Zama yay a kujera yana sauke numfashi. Oum dake kallonsa cike da tausayawa na jera masa sannu. Amsawa yay fuskarsa da murmushi sai kuma ya ?ora da gaisheta. Sai kuma ya juya ga RK yana fa?in, “Barka da juma’a Uncle”.
Amsa masa RK yay shima yana murmushin. “Wai sai yanzu kake dawowa gida? ?arfe biyar fa?”.
“To ya muka iya Uncle. Bakaga shi Autan Oum da yake ?an shagwa?a ne ya gudo wajenta da wuri ba”. Dariya RK yayi ganin yanda AA ya dallo musu harara su duka ya maida idonsa ga novel ?insa batare da yace komai ba. Sai da suka tsagaita Maanal da kanta ke ?asa ta shiga gaisheshi ita da su Barrah. Kallonta ya ?an yi, sai kuma ya ?auke idonsa ya maida gasu Barrah yana amsa musu da murmushi. Kasancewarsa mutum mai barkwanci idonsa akan RK yake fa?in, “Uncle R kodai Momyn tamu ce ne wai? Dan ?azun Oum ke sanar min zaka kawota yau”.
Kallon Maanal RK yayi yana mai jinjina kansa fuska ?auke da murmushi. “Gatanan ai na kawo muku”.
“Kai kai Masha ALLAH, Momyn mu ai ban san ke bace dana dur?usa har ?asa. Matar Uncle Rafeeq fa. Bara kiga na taso ki saka min albarka ga ?anki yazo gaisheki”.
Dariya Oum da RK sukayi, yayinda Maanal ta ?an ?ago ta kallesa a karo na farko. Dai-dai yana ?o?arin sake yin magana amma sai maganar tasa ta ma?ale a saman harshe saboda saukar idanunsa akan Maanal. ?an wara idanunsa yayi na rikicewa, sai kuma ya maida kallonsa ga Oum dake sakin murmushi itama idonta a kansa. Ai da wani irin sauri ya mi?e ya ?arasa kusa da Oum ?in ya zauna, tare da kai bakinsa saitin kunnenta ya ce, “Oum idona ne kokuwa dai kaina ne ya kwance da gajiyar aiki? Wai kin san wa nake gani kuwa? Little fa, Bestyn Auta?”.
Kai Oum ta jinjina masa fuskarta na ?an komawa damuwa, itama a hankalin ta ce, “Itace Fawzan, Maanal ce. Itace kuma Rafeeq ya kawo mana matsayin wadda zai aura”.
Ai zaram sukaga Fawzan ya mi?e yana fa?in, “What!!” gaba ?aya idanunsa a waje sosai, sai kuma ya juya yana kallon AA daya wani share kowa yana sauraren surutun Haneeff, idanunsa kuma nakan novel da tunda su Maanal suka shigo ya daina fahimtar labarin. Sake ?aukewa yay daga kan AA ?in ya maida ga Maanal daketa ?o?arin saisaita kanta. Murmushi ta sakar masa mai sanyi, cikin muryarta mai zurfi da rashin son hayaniya ta ce, “Yaya F”.
Maimakon amsawa sai yakai zaune jagwab a kujera yana fa?in, “Ya ilahil’alamina da gaske Little ?in ce dai Oum. Ni abin ma sai yake min kamar mafarki wlhy”.
“Bakai ka?ai ba Fawzan, ni kaina kallon komai nake kamar a mafarki, yau Rafeeq ya ha?a zuminci sai dai ALLAH ya saka masa da alkairi. Kalla yaran nan yaran Shahidah ne su duka, macen sunana aka saka mata ma”.
Kallonsa ya maida ga yaran, sai kuma ya kalla Maanal. “Little! Su Shahidah duk sunyi aure kenan?”.
Kan Maanal a ?asa ta ce, “Eh yaya. Itama Didi Amal yaranta biyu”.
Wani murmushi ya saki mai kama dana damuwa, sai kuma ya jinjina kansa, “ALLAH sarki rayuwa komai sai kaga yana faruwa kamar a mafarki. Oum jiba dai Autar ki duk ta canja, komai na Little ya canja kamar ba ita ba. Ji yanda ta zama shiru-shiru, ba surutu yanzu, komai nata ya canja, ta girma ta ?ara tsayi”.
Murmushi sosai Oum tayi itama idonta akan Maanal datai ?asa da kanta kawai tana wasa da yatsun hannunta. “Sosai kam Auta ta canja Fawzan, badan fuskar na nan ba ma sai nace an canja min ita gaba ?aya. Girma yazo”.
“A girma yazo kam Oum, ko’a mafarki akace min little zata koma shiru-shiru haka za’a kwana gardama dani ban yarda ba. Little ina Ammie da Abbah fa?”.
“Lafiya lau Yaya, Ammie na Kaduna itama”.
“Ban gane ba, kun dawo Kaduna ne yanzu?”.
Kai kawai Maanal ta jinjina masa. Cikin mamaki ya ?an juya ya kalla Oum, itama shi take kallo, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru saboda maganar da RK yayi….
“Nifa gaba ?aya sai sake sakani a wani irin dogon tunani mai rikitarwa kuke wlhy Aunty, wacece Maanal a wajenku dan ALLAH? Ya akai kuma ni ban santa ba?”.
“Ai kwantar da hankalinka Uncle kada ka wani ru?ar da kanka. Maanal dai ?iyar Oum ce, mu kuma ?anwa ce. Abinda yasa baka santa ba lokacin da mukai zaman Kano ne, kai kuma sannan kuna Paris”.
Da mamaki RK yace, “Kenan har AA ya santa?”.
Su dukansu juyawa sukai suka kalla AA ?in da furucin RK ?in ya wani daki zuciyarsa, hakan ya sashi tsayawa cak da karatun da yake duk da dama tun ?azun ba fahimta yake ba. Kai Fawzan ya jinjinama RK. Sai kuma ya ce, “Tabbas ya santa”.
Cike da mamaki RK da ke kallon AA ya ce, “Lallai, amma gaskiya na sake yarda kai abin tsoro ne AA. Amma shine koda wasa baka nuna min kasanta ba. Aunty kusan fa 3 weeks da fara aikin Maanal a companynsa shiyyasa kikaga inata ?ara jinjina mamakina ai”.
Kallon juna Oum da Fawzan sukayi, sai kuma suka kalla AA ?in da har yanzu dai yana a yanda yake, sai ka rantse baya falon ko kuma baya jin mima suke fa?a akansa. Fawzan ya girgiza kansa kawai da murmusawa, “Ai autan Oum sai addu’a Uncle. Little kice har an kammala karatu?” ya maida hankalinsa ga Maanal.
Idanunta ta janye daga satar kallon AA ?in itama. Ta amsa ma Fawzan da, “Eh Yaya har sarvese nayi”.
“Kai Masha ALLAH, kinga rigimarki ta saka kin kammala karatu da ?arancin shekarunki, kai Little rigima”.
Hannu Maanal tasa ta rufe fuskarta dan tuna baya. Yayinda Oum keta dariya itama tana tuno abubuwa kamar labarin Film. A mamakin su sai sukaga AA ya mi?e batare da yacema kowa komai ba ya nufi hanyar ficewa daga falon. Da kallo kawai suka bisa…. Sai da ya taka step na farko batare daya jiyo ba ya ce, “Oum na wuce massalaci”. Murmushi Oum tayi da masa addu’a, yayinda RK ya mi?e yana fa?in, “?an rainin hankali shine bazakace mu tashi lokacin salla yayi ba”. Fawzan ma mi?ewa yay yana dariya. Sai kuma ya fara raira wa?ar Hamisu breaker _?ar Arewa_.
“Duk wanda yay gamo da abin ?auna baisan rabewa, in dai ko ya rabe duk nisha?i nai yay tarwatsewa.
Sirrin farin ciki soyayya in ba takurawa, mai so aso shi kanso babu abinda bazai iyaba.
Na durkusa akan gwiwata idan kuskure nai. Kiyafiya gyaran dan kamin har maganai.
Nemanki na kara?e kauye na koma birane, fito na ganki Ni kallon kauna kinji yar arewa…
Sissiran dake cikin raina duka ne zan baiyyanawa. So yayi tsitstsige na takawa yay min illatarwa.
Ni bani fasa yarda domin kin zam rayuwata, manta dake hakan ban san yaushene zan iya ba
Kukan da ni nake da kishirwa bata gushe ba, duk da na sani rabuwa bata zamto mutuwa ba…..
Harara mai lasisi AA ya wurgama Fawzan tare da wucewa da sauri-sauri kan stairscase ?in. Hakan yasa Fawzan kwashewa da dariya Oum kuma na murmushi. Shi ko RK da bai fahimci inda wa?ar Fawzan ?in ya nufa ba sai ca yay “To ?ana kodai kaima wa?a zaka koma ne?”.
Shi dai Fawzan dariya kawai yake yi yana cigaba da bin AA da har ya gama sauka daga steps ?in da kallo…
