Ajiya A Duhu BOOK 1 Na Billyn Abdul

Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 92

???9??2??

______________

……..“Nasan zakuyita mamaki akan rashin bin bayanku da bamuyi ba a wancan lokacin, a randa kuka wuce a ranar Fateema jikinta ya rikice matu?a, dan yanke jiki tai ta fa?i, dole muka wuce da ita asibiti, amma sai suka turomu Abuja dan al’amarin nata banbane, paralysis na neman kamata. Tashin hankali yasa bamu tsaya Abujan ba kawai muka fara shirin fita da ita waje da tunanin bazamu da?e ba zamu dawo sannan gwaggo ta huce, ashe wasa farin girki, dan shima Ajwaad sai ciwo mai ban tashin hankali ya samesa, ga depression. A haka suna cikin jiyyar su duka biyun Fateema ta matsa ni da Fadeel muka taho Nigeria domin ku, kai tsaye kuma Giro muka nufa, amma sai muka samu cewar wai ai suma sun wayi gari kun gudu, kuma an sanar dasu a majiya mai ?arfi kuna dangin mamanki ba kuma a ?asar suke ba. Bamu da wani dalilin ?in yarda da su, dan haka muka juya muka koma. Amma Fateema naji tace ?aryane, baki da wani dangi a ?etaran Nigeria, ta sake tada hankalinta har takai jikinta dana Ajwaad yayi rikicewa mai ban tsoro, dan Ajwaad akwai daren da ma har mun gama yarda ya rasu, sai kuma ya farfa?o gabannin asuba. Sai da akaita tausarta tare da mata al?awarin a hankali zanta bincikenku sannan, muka maida hankali akan Ajwaad kuma. A lokacin ne kuma aka bani ambassador, shiyyasa bamu dawo Nigeria ba, amma inata ?o?arina batare data sani ba akan neman ku. Sai dai kuma ALLAH bai ?addara ba sai a dalilin samuwar aikin Maanal a kamfanin Ajwaad ta dalilin Rafeeq. Dan ALLAH mu yafi juna Asiya, mu ?auka dukkan abinda ya faru ?addararmu ce babu mai canjata. Mu dawo da zumincinmu tamkar a baya can.”
Hawayen dake gudu a fuskarta Ammie ta share. Ta ce, “Babu komai Yaya komai ya wuce. Ni dama ban ta?a ?ullatarku ba wlhy. Sannan ban san ma Maanal a ina take aiki ba dan basu sanar min ba. Da tun kafin kuzo nan ma nice zanzo gareku, ban dan Rafeeq nada ala?a da ku ba shi da Maman Najma. ALLAH ne kuma bai ?addara ha?uwar tamu ba shiyyasa, tunda gamu tare da Majdiya fin shekara hu?u”.
“Ikon ALLAH ai yafi gaban wasa. Wannan wata hikima ce ga UBANGIJI mai ?oye al’amura ta yanda yaso, a kuma inda yaso. Shi kuma yasan dalilin yin hakan garemu”..
Haka ne. Kowa ya fa?a cikin jinjina kai….

_________?

Da yamma sosai su Abah sukai shirin wucewa, sai dai fa Oum tace suje ita sai gobe in sha ALLAHU. Jin haka AA yace shima ya fasa, ?afar babarsa ?afarsa. Wani irin takaici ne ya turni?e zuciyar Mamy, dan haka kawai take ji a ranta wani abun Oum ke son ?ullawa. Sai kawai catai ai itama kuwa tana nan ?in. Sam babu wanda ya kawo komai a ransa a tsakanin Oum da Ammie, sai AA ne yay wani iri. Daga baya kuma yace to kawai shi bari ya bisu. Yana ganin hararar da Mamy ke masa amma ya basar. Nibras kam wani sanyi taji a ranta, dan har hankalinta ya tashi da zaman AA a tsakiyar kuraye biyu da take kallo. Wato Maanal da Huzna??, yayinda Huznah da keta dama-dama da AA ?in taji kamar tayi kuka. Haka dai babu yanda ta iya suka wuce. Dama Maanal ko’a kwalar rigarta, sai ma hirarsu suke da Fawzan….

Da daddare akai gagarumar dinner ?in datai tsawa da amsa kuwa a garin na Kaduna kamar yanda su Hajiya Sabuwa sukai fata. Yau ma su Ammie sunje, kuma harda Maanal. Inda rigima taso tashi a hall ?in, saboda matsawar Hajiya Majdiya Maanal da su Shahidah sukaje yima amarya da ango li?i. Aiko Yaya Yazeed ba kunya Maanal na li?a musu ku?i yana li?a mata, sai kawai abokansa ?an neman magana suka taso suka rufe Maanal da li?i aka daina li?ama amarya. Nanfa masifa ta tashi, Aunty Sabuwa da Hajiya Yaya suka mi?e zuwa wajen. Wani kalar fisga da Hajiya Yaya taima Maanal ka?an ya rage tai muguwar fa?uwa ALLAH ya ta?aita Yaya Yazeed ya tareta. Wayyo ina wuta su saka Maanal, nan fa ?annen Yazeed sukai ma Maanal zobe wai zasu daketa, sai da Oum ta shigo tsakkiyarsu cikin ?acin rai ta janye Maanal ?in dan daga ita har Mamy sun halarci dinner ?in suma. Gaba ?aya suka bar hall ?in banda Mamy data ma?ale, dan dama damar hakan take bu?ata na ke?ewa da Hajiya Basariyya….
Abu kamar wasa tun a daren ?awayen amarya da ?annen Yazeed suka dinga posting hotunan Maanal a media suna fa?in maganar banza a kanta. Cikin ?an?anin lokaci kuwa abu yayta yawo. Kafin wayewar gari al’amari ya zama babba, dan tunda ahalin su Hajiya Yaya suka dawo daga wajen dinner sabon rikici ya dake ?alle. Ga amarya an kawo amma bata batunta ake ba. Wannan tashin hankali ya saka Maanal ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazza?i. Dole da safe Nene tai shirin wucewa da ita gidanta. Saboda wannan rikici ya zama wani babban al’amari daya bama kowa mamaki, wato zancen fya?e da akaima Maanal sai gashi a bakunan mutane harma da Media dangin Hajiya Yaya na gorantama Ammie da Maanal. Matu?ar tashin hankali Ammie da su Amaal da su Oum sun shiga, dan sun rasa daga ina wannan magana ta fita. Sirrine da babu wanda ya sanshi a gidan daga Daddy sai Yazeed. Ai sai fa jikin Maanal yay bala’in birkicewa, abinda ake gudun dai ya nema kaiwa ga faruwa, sai da akai gaggawar kiran likitanta abokin Yaya Yazeed dake anan cikin Kaduna..
Wannan fitina ba’a samu kwantawarta ba sai da Baban su Hajiya Yaya yazo gidan da kansa. Shine fa yay musu kaca-kaca yace kuma biki ya tashi kowa ya shirya ya koma inda ya fito tunda amarya ta shiga ?akinta. Sauran shagali kuma ya soke su, wanda kuma yake ganin bai isa ba zai yi ga fili ga mai doki. Hakan ya ?ara ba?anta ran Hajiya Yaya da Aunty Sabuwa, sai dai babu yanda kuma suka iya..

Wannan masifa ta bama Oum mamaki, kishi kamar bala’i, ai sai taji ta sake ?aunar Mamy a ranta. Ta kuma sake jin girmanta da kimarta, dan su dai irin wannan masifa basu ta?a shigar koda kwatankwacinta ba. (Nace Humm Oum ai gara irin su Hajiya Yaya da taki kishiyar??). Zuwa yamma Alhamdullah aka samu jikin Maanal ya dai-daita musamman ta bangaren zuciyarta, ganin kuma Oum da Ammie ga Nene ga ?an uwanta duk a tare da ita kowa na lallashinta ta sake ?arfafa kanta. Daddy ma da Baba da kansu suka dinga lallashinta da bata ha?uri. Sai ma taji duk kunya ta kamata. To wai miye ma na damuwar, ai abinda kowa ke fa?an gaskiya ne, ai an mata fya?en. Tunda dai abune da bazai gogu a rayuwarta ba mizai sa ta dinga shiga damuwa dan an maimaita fa?ar an mata da baki. Wanda ma ya aikata ?in alfahari fa yake da hakan. Sai kawai taji wata irin tsanar AA ta sake tasirantuwa a zuciyata. Aiko bayan sallar isha’i ta zauna ta rubuta text massage ta turama RK akan in dai masu zuwa nema masa aurenta suka wuce gobe zata bama wani dama. Dan a yanzu auren kawai take iya kallar ma kanta a matsayin mafita..
Aiko hankalin RK ya tashi da ganin wannan sa?o nata, dan shi bai san mike faruwa ba duk yau bai duba ko ina na media ba sunje wani ?auye da Abbu ya sai gona zai fara noma ne. can suka yini shi da Alhaji ?arami da Abbu ?in. ?o?arin kiran Maanal ?in yayi amma sam ta?i ?aga masa, dole yay kiran Hajiya Majdiya tunda ta sanar masa tana kd ?in gidansu Maanal biki. A bakinta yaji komai dake faruwa, ya kuma shiga media ya ga sauran. Hankali tashe a daren ya samu Abbu da zancen zuwansu nema masa aure Kaduna a gobe maimakon next week Friday da sukace. Babu yanda Abbu bai so ya fahimtar da shi dai ya bari Friday ?in ba amma ya birkice, har abin ma ya bashi mamaki shi da Mah-mah. Dole suka amsa masa da cewar za’aje goben in sha ALLAHU.
A daren Abbu yay kiran Baba Sardauna suka tattauna sosai. Baba Sardauna mutum ne mai fahimta dan haka ya amince suje goben kamar yanda yarinyar ta bada dama kawai….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected