Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 91
????9??1??
______________
……..A falon Daddy akama su AA masauki, kafin Daddyn ya ?aga waya yay kiran Ammie akan a kawo musu abinci. Da to Ammie ta amsa masa, tare da ajiye wayar suka cigaba da ha?a abincin ita da su Shahidah da Hajiya Majdiya. Hakan kuma yayi dai-dai da shigowar su Maanal, Amrah, Najma, Aneesah, Zezaah (?awayen Maanal kenan na sarvese). Dole ne matasan ?ammatan kai musu kallo ?aya ka ?ara. Dan babu wacce batai ?yau cikin tata shigar ba. Taku suke cike da nutsuwa sun kamo kuloli na waina masa da Ammie tasa akayi a gidan Nene, yayinda Almajirai uku ke biye da su da wasu kulolin manya da sukafi biyun da suka kamo. Gaishe da mutanen dake a falon sukayi sannan suka ?arasa kitchen inda akace musu su Ammie na nan.
“Kai yaran nan ALLAH yay muku albarka, kamar kun san yanzu nake tunanin kiranku”. Ammie ta fa?a tana kallonsu. Amsa mata duk sukayi da Amin. Maanal ta matsa jikinta ta rungumeta. Kallonta tai da mamaki. “Lafiyarki kuwa Maanal?”.
Fuska ta ?an ?ata, sai kuma ta kamo hannun Ammie ta ?ora a saman ?irjinta dai-dai saitin zuciyarta. Kamar zatai kuka ta ce, “Ammie zuciyata ce ke bugawa da sauri, gabana kuma nata fa?uwa. Sai nake jin kamar wani abu babba na kusanto ni”.
Shiru Ammie kawai tai tana kallonta. Itama zuciyar tata na raunana. Dan bata raba ?ayan biyu kasancewar Ajwaad a gidan nan ya sakata jin hakan. Ya rabba wannan wace irin tarayya ce haka?. Amma dai bari tai mata tambaya. Fuskar Maanal ?in ta shafa, cike da kulawa ta ce, “Dama yana miki haka?”.
Kai ta girgiza ma Ammien tana sake narke mata a jiki. Ammie ta sauke ajiyar zuciya, tare da shafa mata kai ta ce, “Kairan in sha ALLAH kinji my babie”.
Kai ta ?agama Ammien sannan ta saketa saboda umarnin da Hajiya Majdiya ta basu na ?aukar abincin da aka shirya su kai sashen Daddy. Manaal da Najma ne a gaba, sai dai Najma ?in ma ta gota Maanal, dan itace ta fara shiga falon da sallama Maanal biye da bayanta. Da wani irin sauri Najma ce ta tsaya cak tana mai waro idanunta da fa?in, “Lah wa nake gani kamar su Yaya Fawzan da Yaya AA? Abah! Babban Yaya”.
Da wani kalar sauri itama Maanal ?in ta tsaya, hakama su Amrah duk suka tsaya suna kallon inda Najma ?in ke kallo, sai ma ta ajiye kular hannunta ta nufi inda suke cike da mamaki da farin ciki. Ba ?aramin girgiza zuciyar Maanal tayi ba, dan nata idanun akan AA ?in suka fara sauka. Kamar shima kuma ance ya kalletan sai nasa idanun a kanta. Da sauri ta janye nata zuciyarta na zallo. Cikin ?arfin hali ta maida su akan Abah da ya furta, “Finaly yau dai gani ga Autan Oum”.
?asa Maanal tayi da kanta tana murmushi, sai kuma ta cigaba da takowa cikin falon ta ajiye kayan hannunta inda su Amrah suka ajiye, gaban Abah taje ta dur?usa, har cikin ranta itama tana jin da?in ganinsa. Abah ubane da bazata ta?a mantawa ba a rayuwarta. Ya nuna mata dukkan gata da soyayyar da ko ita ?in a cikin ahalinsa ta fito iyaka kenan. Shiyyasa har gobe shine uba mafi kima da daraja da take kallo a cikin idannunta. Hatta da babu sunan mahaifi kawai yake amsawa a zuciyarta. Amma uba na gaske da bugun ?irji a nunama duniya Abah ne farko. Cikin rawar murya alamar tahowar kuka ta shiga gaishe shi. Shima a mamakin duk wanda ke’a falon idanun Abahn cike suke da ?walla. Amma sai yay jarumtar sakin murmushi tare da kai hannunsa ya kamo nata. Kamar abinda take jira kenan hawayen suka shiga rige-rigen sakkowa.
“My daughter nima so kike nayi kukan?”. Ya fa?a cikin taushin murya da kulawa. Kanta ta girgiza masa. Kafin ta share hawayenta ta ?ago ta ?an kallesa. Murmushi ya sakar mata, itama sai tayi murmushin. “Abah nayi kewarka matu?a”. Ta fa?a a hankali. Gefe ya kauda kansa, yasa babban yatsarsa ya ?auke guntun hawayen daya ciko masa idanu shima. Har cikin ransa yana ?aunar yarinyar, ?aukarta yake tamkar yaransa guda uku daya mallaka a duniya. Sake juyowa yayi gareta da murmushin dai. “Nima nayi kewarki Maanal. Banta?a kwana na tashi babu ke a zuciyata ba. A kullum ina ji a raina akwai wani gi?i da babu a cikin ?a?ana. ALLAH yay miki albarka, ya kare rayuwarki, ya azurtaki da farin ciki mara yankewa. Ya rabbi kasa iyakar jarabawar kasancewa a nesa da juna da mukai kenan.”
Jiki a sanyaye kowa dake a falon ya amsa. Yayinda kan AA ke a ?asa babu mai ganin fuskarsa balle yanayinsa. Gaishe da su su Aneesah sukayi suka fita, sai Najma da Manaal dake gaban Abah suna magana ?asa-?asa da kowa baya ji. Dan hatta Daddy dake a kusa da su baya jin mi suke fa?a. Dai-dai nan Huznah ta shigo hannunta ?auke da babban basket an shiryo abinci, sai yara biyu biye da ita da kayan ruwa da lemuka. Gaba ?aya hankalinta akan AA da kansa ke ?asa har yanzu yana latse-latsen waya. Babu ko kunyar mahaifinta dake a falon kanta tsaye gaban AA ?in ta nufa ta dire basket ?in, murya can ?asa cike da iyayi ta ce, “Barka da zuwa gidanmu Sweetheart”.
?an jimm AA yay zuciyarsa na kai da kawon wai da shi ake ko wa? Ga shi kamar yasan muryar. Sake yin magana da tayi ya sashi ?agowa a karo na farko, manyan idanunsa da suka ?an ka?e ba kamar sanda ya shigo gidan ba da suke fari tas ya zuba mata. Harga ALLAH yayi mamakin ganinta anan ?in, amma sai ya dake ya wani kalar janye idanunsa ya maida akan wayarsa. Duk da zuciyar tata ta raunana da salon nasa haka ta dake tare da basarwa ta juyo tana kallon sauran mutanen falon. Karon farko gabanta ya fa?i sakamakon saukar idonta akan Abah, ya ALLAH, wlhy batasan harda mahaifinsa ba, ai da ta kama kanta. Ita tsabar ganinsa ya firgitata duk zatonta abokansa ne ma. Zaram ta mi?e daga gaban AA ?in ta nufi inda Abah yake. Sai da ta watsama Maanal dake mata kallon mamaki harara sannan ta dur?usa cike da girmamawa tana gaishe da Abah. Amsa mata yay cike da kulawa dan kamannin Daddy a bayyane suke gareta. Ya tambayeta sunanta ta gaya masa tana faman sinne kai wai ita taji kunya. Kafin ta juya tana gaishe da su Babban Yaya. Ta gane Fawzan dan haka bayan gaisuwar ta tambayesa ina Oum da Mamy.
Fawzan da al’amarin yarinyar ya ?aurema kai ya bata amsa cikin dauriya. “Su Oum na tare da Ammie”. Zaram kuwa ta mi?e da fa?in, “Lah ai ban sani ba”. Kafin wani ya samu damar magana har ta fice. Tsabar mamaki daya lullu?e Daddy ya saka shi suman zaune ya kasa magana. Sai kuma Huznah ?in na fita Hajiya Basariyya da Maman Yaseerah suka shigo da sallama. Shi Abah ba wani sanin Maman Yaseerah yayi ba, duk da kuwa ?anwarsa na matsayin kishiyarta. Koda suka gaishesu ya amsa ne da tunanin duka matan Daddy ne, dan kamanin Huznah yafi fitowa a fuskar Hajiya Basariyya. Fuskar Maman Yaseerah da murmushi ta ce, “To wai ni ina surukin namu anan?”.
Karan farko Daddy daya kasa daurewa ya ce, “Suruki kuma?”.
“Eh mana Alhaji. Ai ba?in Huznah ne, nazatama har sun sanar maka, shine muke maka batunsa kwanaki, har mukace ka shirya za’a kawo ku?i kace a jinkirta a gama na Yazeed ko. Kamar AA naji tana ambatonsa da shi ita Huznahr”.
Wani irin ?agowa AA yayi ya kalla Hajiya Basariyya mai maganar, yayinda Abah da su Babban Yaya duk suke kallonsa su kuma. Shi ko Daddy Hajiya Basariyya ya zubama idanun kawai. Sai falon yay shiru akama rasa mai iya yin magana. Wani irin takaici ne ya gama turni?e AA, jiyay bazai iya daurewa ba, dan haka ya bu?e baki a fusace zai yi magana, amma sai Babban Yaya dake kusa da shi ya kama hannunsa ya ri?e. Dole yay shiru, tare da ha?iye maganar. Tsaf Daddy ya lura da abinda ke faruwa. Dan haka a dake ya cema su Hajiya Basariyya, “Okay naji, kuje zasuci abinci tukunna”.
Baki Hajiya Basariyya ta sake bu?ewa zatai magana Daddy ya harareta, dole ta ha?iye. Suna fitowa Maman Yaseerah ta ce, “Kada ki wani damu shirin nan namu fa ya hau, kin san Malam akwai iya tsara abu”.
“Anya kuwa Aminiya, kina ganin yanda yaron ke kallon mutane babu ?igon sassauci, wlhy sai yanzu na fahimci abinda Huznah ke sanar min a kansa. Lallai da ganinsa zai yi ba?in taurin kai.”
“Karki wani damu da taurin kansa, zamu bi dashi ne tsaf ya mata biyayya kamar babu gobe. Yanzu dai kawai muyi ya?in shigarta gidan. Ammafa ni ina mamakin munene ala?arsu da Asiya ne haka wai?”.
“Nima wlhy ina son sanin wannan dangantar, amma ki bari, akwai ta hanyar da zan bincika”.
