AKWAI LOKACI BOOK 2

AKWAI LOKACI BOOK 2 BY UMMU AFAN

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Story & written
By
The special writer

UMMU AFAN

 

FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION

(F.C.T.W.A)

 

HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER’S OF THE NATION

 

I DEDICATE THIS PAGE TO YOU Hauwa’u idris ( maman daddy )
Allah yabar zumunci inajin dadin comment din ki Allah yabar kauna keep it up

 

 

AKWAI lokaci

 

PAGE 101to105

 

 

PROF yashigo direct dakin amaryar ya wuce sai yaji kofa gam

Kuma gashi bashida spire key
Duk guda hudun suna hade da juna

Ya koma dakinsa yayi wanka
Ya koma kan bed dinsa yadauki waya
Yasoma dialing din number husnah yayita ringing

Husnah bata daga wayar ba

Prof yayi mirmushi Wanda shikadai yasan abinda yasashi murmushi

Ya rufe ido Dan bacci amma bacci yace baisan zancenba

Yadauki wayarshi kawai yakira Ahmad

Saida yakira Ahmad sau biyu kafin ya dauka

Ahmad yace kai ango yadai kira da wannan lokacin

Hakeem yace kai dai bari wallahi man
Wallahi yarinyar nan ta kulle min kofa

aikafin yakai karshe Ahmed yafashe da dariya sosai yayi dariyarshi

Kafin yace amma wallahi husnah ta burgeni
Sosai

Hakeem yace Dan iska dariya zaka min ko

Ahmad yace aikaine abokina duk kabi ka tsorata masu yarinya aidole ta kulle kofarta
Dan batasan mezaifaruba idan akabarku Ku biyu

Hakeem yayi murmushi yace duk tagama buyanta badai ta shigo hanu ba

Zanbata mamaki zata shigo hanu ai

Ahmad yace wallahi dai kabi yarinyar mutane a hankali
Bafa babbar mace bace

Dan nasan kasaba da manyan mata

Yayi dariya yakashe wayar shi

Hakeem cikin murmushi yabi wayar da kallo

Yace zanrama ne

Kafin yakoma amma bacci fa yaki Sam
Daya rufe ido zaiga husnah alokacin da yake kissing dinta

Sai yayi murmushi ya rungume pillow kawai bacci yayi awun gaba dashi

Laila duk abinda kefaruwa tana lebe tana gani aikuwa ganin Hakeem ya burda kofa yaji akulle duk ta gani

Har wayan dasukayi da Ahmad taji aikuwa cikin farinciki ta koma part dinta ta sanar da su hajiyarta da kanwarta suby

Dan basu komaba ita suby auran nata ya mutu shiyasa zata zauna gurin Laila

aikuwa cikin farinciki hajiya rukayya tace aikin banza Ashe ma duk abinda suke yarinya bata so

Suby tace a a karku manta dama boka yace zai sa gaba a tsakaninsu

Watakila aikin ne boka ne yafara aikitakanta

Inbahakaba wazaiki yaya Hakeem a matsayin miji

Hajiyarsu tace tabbas maganarki hakatake

Kunga ganiba gwamma da muka sake mishi kudi gashi anfara aganin cigaba

Laila dai da farin ciki ta kwanta abinta zuciyarta fati kal

 

Karfe hudu dai dai na asuba Husnah tafarka cikin nannauyar baccin da ya dauketa

Tashi tayi tashiga bathroom alwala tayi kafin tayi nafilfilunta kamar yarda tasaba ana kiran sallar asuba tayi sallarta tayi adduointa da karatun alkur’ani

Kafin tacire kayan jikinta Dan jiya bata samu daman cire kayan ba saboda gajiya

Tashiga wanka kafin tafito
Spray kawai da shuwa tashafa sleeping dress tasaka duguwar riga abinta tafada gado abinta

Sosai taji dadin baccinta Hakeem bayan yadawo daga sallar asuba yasake tana dakin husnah shiru bata budeba

Direct dakinshi ya wuce dakinsa
Shima baccin yakoma

Karfe bakwai da rabi dai dai mai aikin mummy ta buga kofa

Suby kanwar Laila ita tabude kofar

Taga me aikin mummyn Hakeem ce

Tace sannu suby ta yatsina baki yadai ina zaki da basket din abinci haka

Tace hajiya ce ta aikeni nakawo ma amarya abin karyawa

Suby ta kebe baki tace to aikuma basu tashiba amma kawo saina na mika mata

Tabata abincin

Suby ta karba tashige dashi part dinsu gurin su Laila da hajiya rukayya

Laila cikin murna tace yauwa suby dauko maganin a side drawer kikawo

Aikuwa haka suka barbade komai da maganin nan

Farfesuf na kayan ciki sai kunun gyada da kosai

Kai kuma farfesun ganda Wanda yasha kayan hadi sosai

Haka suka bikomai suka badeshi tas

Hajiyq rukayya tace maza ke suby tashi kikaimata

Laila tace abarta ta kai Dan tanason ganin amaryar

Hajiya rukayya tace a a idan kika kai dakanki za azargi wani Abu

Zakiganta ai mudai burinmu kawai tabar gidan

Suby tace wallahi nimafa basanin amaryar nayi bama dan haushi

Husnah cikin bacci taji ana buga mata kofa ta tashi tayi hanyar falonta

Tayi kofa tabude sukayi ido hudu da suby
Suby sai tadauka kaman gezo idonta suke mata wannan irin zukekiyar yarinyar kuma daga ina

Husnah ta ce sannu suby tace ina antyntaki

Husnah ta yatsina fuska tace antyna kuma

Suby tace ina nufin amaya
Husnah tayi murmushi tace OK ai tashiga wanka

Tana ganin suby tasauke ajiyar zuciya

Husnah ta kibata hanya kuma
Suby tace ga shi inji hajiyar yaya Hakeem akawo mata

Husnah tace OK angode barin kaimata
Suby ta mika mata basket din husnah tarufe kofarta

Murmushi husnah tayi ta ajiye basket din ta ajiye kan dining kafin ta koma kan bed koma bacci

Sai karfe goma dai dai ta tashi
Ta gyara bedroom dinta da falonta ta badeshi da kamshi

Ko ina yadau kamshi kafin tashiga bathroom tayi wanka tafito ta shirya cikin wani tsadaddar super Holland dark blue sai adon pink ajikinsa

Yadda dinkin yazauna ajikinta shizaifi Baku sha’awa sosai das yamata dinkin ma kawai a in kallone
Matsalarta daya bata son dankwali ta tace gashinta takama da ribbon pink

Kafin ta murza daurin Dan kwalinta abin wuyanta ma pink ne

Gaskiya husnah tayi kyau matuka

Tadauki ta kalminta plate shoe tasaka

Har ta zauna zatafara break fast saikuma taga rashin dacewar hakan

Bata je tagaida mummy ba

Gyalenta tadauka maishegen kyau tayafa

Pink colour

Tafita tayi hanyar kofarta tasaka key ta kulle

Bayan ta fita

Dama dole saitabi ta main falonsu gabadaya tana fitowa kuwa taga mutan gidan gaba dayansu a falo

To itabasaninsu tayi ba
Ganin harda manya yasa husnah ta durkusa tana gaida su hajiya rukayya da kuma Laila

Laila ta watsa mata harara
Wai ita hakimar bata fitowa ne saike

Hajiya rukayya tace inazata fito ansamu duniya
An auri mekudi an asirceshi

Suby ta kalli husnah tace ‘yar buzuwa kotafiya za ayi ne

Husnah ta kalleta tace inje ina ai munsamu gida nida antyna
Dan nadawo kenan gwamma muma muzauna muci arzikin Dan da alama bamu kadai bane ‘yan cin arzikin

Husnah tana gama yada musu magana tayi waje abinta

Har suby zata bita hajiya rukayya tace a a kyaleta kar ajimu tun yanzu mana

Laila race lalle ma Dan talaka be iya samun wuriba
Wannan zakewa haka harda dauko ‘yar riko
To wallahi wannan yarinyar kamar aljana bazata tazauna min agida wallahi

Kalli yadda take tafiya kamar wata ‘yar sarki

Hajiya rukayya tace aibakisan halin talakabakenan idan yasami guri

Kuma ke Laila da kike cewa bazata zauna ba yayar tata ma ba zaman zatayi balle ita ‘yar cin arziki

Nan dai suka muna funcinsu

Husnah tayi sallma a falon mumy shiru ba kowa

Ta nemi guri tazauna a tafkeken falon su mummy

Mummy ta sauko daga sama bata lura ba harzata shige kitchen
Husnah tayi saurin sauka kasa tace mummy ina kwana

Mummy hafsat tajuyo tayi tazali da surukar tata

Tace a a husnah ai ban lura bama meyasa kika zauna nan baki haura saman ba saikace bakuwa

Husnah tace bakomai mummy nan ma yayi

Mummy hafsat tace a a nan gidanku ne ko ina zakishiga
Kina da damar hakan kinjiko

Ya bakunta husnah tayi murmushi kawai batace komai ba

Mummy tace kinci abinci ko husnah tace yanzu zanje nayi

Kafin mummy tayi magana Abdul Hakeem yayi sallama yashigo wata tsadaddiyar shadda milk colour sai wata hadaddiyar hula da ya murza akansa Wanda yasake fito da kyakkawar fuskarshi mai kewaye da kwantacen saje dayakarawa fuskar tashi kyau

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected