TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK 3 by AsmaU Baffa
[2/13, 7:56 PM] AsmaBaffa: TANTIRIYA
A GIDAN YARI
BOOK 3
~TAIMAKO~
1-5
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA GARE KI
AIDA MAMAN TASNIM
PAGE NAKI NE
MRS CHIEF
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin ‘yar’uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni’ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala’in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau’in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha’ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau’in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had’addun supplement irin wad’anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad’in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu’bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Washe gari Khadija wato Mero komawa tayi ta cikin dakin da take kokarin lallai sai ta fasa shi,tana zuwa taji sheshekar kukansa ta bangaren dakin da yake,yau taji wani a kusa da shi tayi mamaki Jin ana bashi hakuri,Yana cewa itace wacce zan aura shike nan ta rasu ta barni,Ido Mero ta zaro tare da dafe kirji da hannu biyu tace dama Yana da wacce zai aura ma ashe,ta rasu Kuma to Allah yaji kanta idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani” shine yake wannan kukan kamar wani mace sabo da soyayya,shi yasa in ba dole ba me za ayi da me kudi Abu kadan Kuka ba juriyar wahala,talaka kuwa ba ruwansa ya Saba da kaddara iri iri,kasa hakuri tayi da karfi tace to a gobarar ta Kone?Wanda suke cikin dakinsa sun zaci Aljana ce tsoro ya kama su Dan su iya tsayin rayuwarsu basu taba Jin maganar wani ta bayan dakin wani ba bare mace ma.
Matashin magana yayi yace ae gobarar har da ita ta Kone,Mero tace sai ka daga Murya banji baaaaa…….tsaki ya ja da gajiyawa yace da karfi da ita gobarar ta Kone,Mero tace Allah yaji kanta tayi Mutuwar shahada,su dai mazan tashi suka yi suka fice basu yarda da mutum yake magana ba.
Khadija taci gaba da magana ka gama kukan ne? banza ya mata,kyale shi tayi taci gaba bula katangarta yau dai taci nasara ta bula Inda ya tsage yatsu biyu zasu iya shiga,idonta Daya ta manna a jiki ta leka taga dakin gashi nan dai wai a haka VIP ne,tace wani abin sai gidan yari.
Maman Wahida tana gidan yari yanzu Kam ta Saba ta zama Yar gari harkar gabanta take yi,iyalanta suna yawan zuwa dubata bata da matsala a vip take zaune,masu hali basa fadawa matsala,bata shiga harkar kowa indai ba a vip kake ba to tasan baka da gata ko kulaka baza tayi ba.
Mero bata San Maman su Wahida kanwar Mima bace tana dai ganinta kamar su daya da Mummy sai ta dinga mamaki, yau dai gaza hakuri tayi ta nufi wajenta da take zaune tana hutawa abinta.
Mero tana zuwa tayi Sallama sanye take cikin riga da skirt na wani tsohon Leshi Wanda suma Azima me kwana ba wando ce ta bata su Ganinta cikin tsumma,Mero tace Ina yini,Maman Wahida da kyar ta dago ta Kalli Mero Khadija Shekeke tace ya aka yi? Dan ma kin samu na gaishe ki ,na saki ki gaishe ni? Khadija tace na kwace gaisuwa ta ba Ina yini ba,dama kama kike da wata Mummyn Spark,da sauri ta Kalli Mero tace a Ina kika sansu kanwata ce uwar mu Daya uban mu daya,Khadija tace da Mima,da Rafeeq,Misam duk ba wanda ban sani ba a cikinsu,Sai lokacin tace zauna,Khadija tace uhm da kika ji nasan Yan uwanki to ni ba me kudi bace shara da wanke wanke nayi a gidan Mummyn Spark,Kuma rannan Spark yazo wajena.
Maman Wahida tace Spark din yazo wajenki? Mero tace ai shi bashi da matsala shi yake bani kudi da komai,amma ni Ina a matsayin kamar uwarsa ya kasa zuwa mu gaisa,Mero tace laifi kika Masa watakil ai ku halinku sai addua kwana Nan Yar uwarki zata zo ku hadu ku zauna kuyi ta zumunci,Mummyn Spark kwana nan zaki ganta a gidan nan,Maman Wahida tace ubanwa ta kashe ke karki jawo mana masifa a dangi,Azima ce ta fito tana rangwada tace Khadija yau baza kije sakar bane? zanje mana muje to,Khadija ta mike tabi Azima suka wuce Mero tace ke Azima karatun Nan da kyar nake ganewa kin San ni dakikiya ce gwara ma na addini Ashe haka ake wankan tsarki,na dade Ina haukata ban sani ba,ai sai jiya na koya,Azima ta dinga dariya tace gaskiya Jahila ce Khadija,Mero tace ta karshe ma, Gani da suna me dadi me asali amma ban gaji me Sunan ba gaskiya iyayena sun cutar Dani yanzu a gidan yari nake wayewa Kai duniya,ni Kuma a gidan yari nake Ilimi Ina wani zama Yar birni,Azima tace gashi Nan kin koma Yar birni na gyaraki tsaf,rashin kunyar ne har yau baki fara gogewa ba Dan Allah kiyi ki koya ki karasa cika sharudanki na gidan yari,ni kin ganni idan na fita a gidan yari duk Wanda ya aureni ya aurarwa kansa tsiya shi yasa bama na so na fita ni karshe ace nayi aure Kuma ni ba Wanda ya isa ya sani ko ya hanani.
Mero tace uhm Azima ke kam ai baza ki fita bama sai kaddara tunda laifinki ba sharri a cikin,Azima tace thank God nayi nadama ni wlh na Saba da zaman gidan nan ko gida na koma ma bazan ji dadi ba,Mero tace gashi mun hadu wai Azima kin San su Chika da Beauty,Azima tayi dariya tace daina tuna min su,ke gidan da kike aiki baki yi dace ba wlh wasu Yan aikin suna dace acan suke samun Ilimi amma suka barki a Jahilarki Khadija,Mero tace su ai Yan boko ne da karatun Boko suke aiki na addinin suna da shi dai dai gwargwado amma sun manta ma kudi da duniya yasa sun manta ma da wani Ilimin addini bare su koyawa wani,sannan duk talaka baida daraja a wajen su ta ya zasu koya Maka Abu suka San ma me kake ciki bare wacce nake gidanta a cikinsu itace ma tafi kowa lalacewa.
Azima tace itace Danta yake auren Naila Inye lallai Naila tayi prison mijinta yayi prison ga uwarsa zata yi prison su uku rigis duk prison sai kace gado,Dariya suka yi Mero tace gashi nima daga zuwa aiki gidan na fado Ina tsoron Naila karta haifo Dan Birsina,karasawa suka yi Inda ake koya musu sakar,Azima ta wuce bangaren nata ta kayan Sanyi ita kuwa Mero bangaren mificin sarakuna irin na fadar sarki masu kyau da tsada su ta iya,tayi mugun iya saka su tunda tazo ta koya,gashi in sun saka baza a basu kyauta ba sai dai ka siya in kana da kudi,Mero sai da ta siyi biyu wai sai ta yi kyauta.
Bangaren su Malam Jilani suna zaune Dan Indo ya shugo idonsa jajir yace kai akaramakallas gaba dayan ku Jiya Mafarkin Jamilu nayi ya dawo gidan nan,Malam Garzali ya tuntsire da dariya yace wai Dan Allah baza ka manta da Jamilu ba,tayi aure ance tuni,Dan Indo ya jawo tarkacen kayan Naila data bari ya kalle su,ya daga wani katon bujen wandon ta ya furta Allah sarki duniya yanzu wannan Jamilu ta saka shi,Malam Jilani Yana boye dariyarsa yace Matar wani ce dai yanzu,haramun kake aikatawa,Dan Indo yace Allah ya tsinewa yaron nan Spark,zuwansa ba alheri bane ya cuceni,yanda nake Son Jamilu na tabbata baya sonta haka,duk sanda na sake ganinsa a gidan yari ko ziyara yazo sai ya yabawa Aya zakinta,Malam Jilani suna ta dariya,Dan Indo ya sake Jin Haushin su yace ai kune manyan munafukai dama karya kuke Kun San macece shi yasa kuka riketa a dakinku,Kuna fakewa da karatu Yan iskan banza Yan iskan wofi,Malam Sharu yace mu mene namu a ciki yaro dai Jamilu da hannunka kayi Masa hanya ya bar gidan Nan sabo da haka laifinka ne,mu karatun mu muke da addua,ai ba karatun Allah kuke ba ya ja tsaki ya fice.