AURAN SOJA BOOK 1 COMPLETE
Compiled By Umar Dalha Funtua.
Copied By Feenerh.
*AURAN SOJA*✈
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
*Am back Fan’s duk kan yabo da godiya ya tabbata ga Allah ubangijin kowa da komai da yabani ikon dawowa Acikin sabon littafi na ina fatan Allah kasa A amfana da shi kuskuren dake ciki Allah ya yafemin*
_jinjina gareku_
✍Golden pen writers Association.
_ina Alfahari daku Mun Amsa sunan, ZAMANA AMANA Allah yakara mana kaunar juna_
1&2
_A kofar gidan na hango motoci Ajere kamar wani sarki ne ko ince gwamna Amma abin mamakin Samarine matasa reras Akofar gidan_
_Koda na matsa domin in dakko muku labarin Abinda ke faruwa sai naga Abin mamaki_
_matashin saurayi ne Azaune kyakkyawa Ajin farko wato (first class) duk inda kuke tunanin shi ya kai,_
_bawai fari bane a’a chocolate colour ne kala mai tsada, ga cikar zati da kuma haiba,_
_gadai samari masuji da jini Ajika Amma duk cikar wurin ba kamar shi,_
_mamaki na to wai waye wannan da samari suka za ga ye shi haka?_
*KAMAL*
_Lieutenant colonel kamal Ibrahim kenan (the youngest colonel)_
_gaba daya matasan suna zagaye dashi, shi kuwa ba abinda yakeyi sai faman danna tsadaddiyar wayar dake hannun,_
_ya wani kishin gida kamar wani sarki, kana ganinshi kaga miskilin soja ga wani irin kalai laita kamar wata mace,_
_hirarsu kawai sukeyi atsakanin su Amma shi hankali shi na kan wayar shi,
_can naga wani matashi Wanda bazasu wuce sa o ‘I da kamal din ba ya karaso kusa da shi,_
_ya duka saitin kunnen shi ” Don’ yakamata kayi wani Abu gayun nan su watse kasan Alhaji na jiran isowarka ko_
_cikin ginshira kamar kuma bayaso yayi maganar, “do something’_
_gayen yayi murmushi tareda girgiza kai ya Ciro wasu bandir na y’an one one thousand ya mikawa daya daga cikin su,_
” Kuyi hakuri da wannan kafin ya gama ganawa da mahaifin shi zuwa gobe,
_cikin tsananin farin ciki samarin suka fara yimai godiya da kirari “Allah yayima General shugaban matasa kafin su watse,_
Yarage daga shi sai wannan gayen da naji wani ya kirashi da Samir,
_”Don yanzu zaka iya Ajiye wannan wayar mu shiga daga ciki ko kuwa ya fada cikin kuluwa_
_mikewa kawai yayi cikin kuzarin su na sojoji ya kama hanyar shiga cikin gidan,_
_Hmm Ajiyar zuciya na sauke domin yanzu ne na kare mai kallo da kyau dogone sosai Wanda ya Amsa sunan shi namiji_
_Allah yayi mai k’ira irinta jaruman sojoji Masha Allah,_
_Abin mamakin shine nasan sojoji basa mu amala da manyan kaya Amma shi gashi harda hula ga lafiyayyan Agogon Rolex takalminshi wow_
(He is damn handsome Fan’s)
_Sun nufi cikin gidan kai tsaye, direct wani part naga sun shiga saboda na lura gidane mai dauke da parts da d’ama,_
_wani dattijo na hango kishin gide acikin wani ma dai daicin falo w’anda akalla zaiyi sittin ko fiye da hakan,_
_Yanada cikar zati irin na girma da kuma haiba, ganin irin littafan dake cikin falon ya tabbatar min da cewar malamine_
_sukayi saurin karasawa kusa dashi bayan sunyi sallama, kamal yayi saurin cire hularda ke kanshi cikin girma mawa ya duka Agaban dattijon_
_baba munsameku lafiya? Cikin tsananin farin ciki ya amsa ” sannu kamalu’ kun samu shigowa; ai tun dazu nakeso infita saboda kafadamin zaka iso na tsaya jiranka_
Samir ma ya gaishe shi,
_”Allah yayi muku Albarka ya kuma kareku daga dukkan nin sharri_
Suka Amsa da Ameen cikin girma mawa
” nasan mutanen Ku na jiranku don haka zaku iya tafiya idan kun huta sai muyi magana,
Cikin tsantsar lad’abi yace “Baba ai mun sallame su, a’a duk da haka Ku shiga daga ciki Ku gaida sauran mutanen gidan ko,
Suka mike cikin natsuwa tareda yima tsohon godiya yana binsu da kyawawan Addu’o’i,
*Alhaji Ibrahim Khalil* malamine Wanda yasan Abinda yaka mata,
_Suna zaune ne Acikin Garin Zaria Acikin unguwar ban zazzau, gidan da yake ba shi kadai bane, yana tareda kanninshi_
_Alhaji Ibrahim shine babba sai kuma mai binshi wato Alhaji Suleiman sai kuma Autansu Alhaji umar,_
_Kowannen su yana zaune da iyalinshi acikin wannan gidan dake cikin ban zazzau,_
_part hudune agidan part na farko shine na Alhaji Ibrahim sai kuma na Alhaji umar na Alhaji Suleiman ne na uku sai part din karshe na mahaifiyar su,_
_wato tsohuwa mai ran karfe, hajiya Rabi’a wadda suke kira da gwaggo,_
_bawai gidane irin na masu Arzikiba a’a sunada rufin Asirin su ba Abinda ya fi karfin su Arayuwa tun ma kafin yaransu su girma suzama wani Abu_
_gidane mai cike da had in kai da kuma zumunci sunada iyali ba laifi Amma bazaka taba gane waye ya haifi waniba saboda tsabar hadin kai da zumunci_
_Duk kaninsu sunada mata Amma Banda Alhaji Ibrahim tunda matarshi ta rasu shekaru biyu da suka wuce kuma duk tsawon zamansu Allah bai basu haihu wa ba harta koma ga Allah_
Y’an uwan shi sunyi ta fama dashi yayi Aure Amma yaki yace “ya’yan su sun isheshi Arayuwa,
_idan ba Anfada maka ba bazaka taba sanin bai haihuba Agidan saboda komai na yaran gidan shi ya dauke tun daga karatunsu har hidimomin su,
Musamman Dan gatanshi wato kamal ga badaya yaron yatashi Agabanshi ne, shikan shi kamal din saida ga baya yasan basune suka haifeshiba,
_Kamal D’ane ga Alhaji Suleiman wato mai bin Alhaji Ibrahim su hudune Adakin su shine babba duk agidan sai safwan bilal sai Autar su Zainab_
_Alhaji umar kuwa yaranshi uku duka mata duk biyun sunyi Aure sai Autar su wadda take sa ar Zainab ce wato Asma’u Wanda suke kira da *HUSNAH*_
Atakaice gidane bawai mai yawan cikar ya’ya ba
*KAMAL*
_Wato Don yanda Abokansu suke kiranshi yasamu shiga aikin soja ne saboda tsananin kaunar da yakewa aikin tun taso war shi_
Bayan kammala diploma dinshi yasamu shiga makarantar horodadda sojoji dake cikin Garin Kaduna wato N.D.A Wanda yafito da babban matsayi,
_gashi yanzu harya kai ga matsa yin lieutenant colonel Acikin shekara talatin da y’an kai_
_Akwai girman kai Wanda bawai kanninshi mata kawai ke shakkar shi ba har ma da kanninshi mazan y’an Jami’a_
_Zainab da Husna sun ma tsani ace yau ya shigo Garin baya duka baya zagin su Amma kallo kawai ya ishe su_
*Husnah*
Tafi kowa tsanar lamarin shi saboda tafi kowa sanin wanene shi tun taso warta, acewarta yanada Fuska biyu Annabi a fuska firauna A zuciya……………..✍
*taba ka lashe yanzu nafara acigaba da gashi my fan’s*
[3/8, 8:37 AM] Feenat Marubuciya:
*AURAN SOJA*✈
_patients love & sacrifice_
Story writing by
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
3&4
_Samir shine Abokinshi tun suna kuruciya tare suka taso unguwar su daya har zuwa lokacin da suka fara aiki shima sojan ne Amma kowa yana serving awuri daban_
_Akwai zumunci mai karfi atsakanin iyayen su kasan cewar su a unguwa guda kuma dukansu malamai yasa Amintar su ta core_
_Alhaji Ibrahim baida wani Amini da ya wuce mahaifin Samir saboda kaunar dake tsakanin ya’ya n su,_
_Husnah da Zainab sun taso cikin kaunar junan su kamar ciki daya suka fito saboda suntaso sunga kan iyayen su ma duk Ahade ba wani mai nuna ma wani banbanci_