BAYAN WUYA BOOK 1

BAYAN WUYA BOOK 1 COMPLETE

[5/21, 8:02 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*Book 1*

By
*Mariam sani Riamcool*

 

*MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION*

*Bismillahirrahmanirrahim dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki gagara musali da zai bani damar rubuta wannan littafi,Yadda na farashi lafiya ya Ubangiji ka bani ikon kammala shi lafiya, kuma ya Ubangiji ka bani damar Rubuta Abinda Al’umma zasu amfan

بسم الله الر حمن الر حيم

 

*Page 1 &2*

Duƙe take a cikin ɗan kurkun kichen ɗinsu tana ta faman, fura wuta hayaƙi duk ya cika kichen ɗin,sai uban hawaye take, da ƙyar ta Samu ɗanyun itacen Suka kama da wuta, fitowa tayi daga kichen ɗin don ida kaye_kayen kayan da ke cikin ɗan ƙaramin gidan nasu,ga wani Hadari da ya harhaɗu garin yai baƙiƙƙirin, Sai uban zafi,

Sauri_sauri ta dunga yi harta kammala kaye_kayen,tana kammalawa taje ta kaɗa miya sannan ta shiga wanka,tana fitowa ƙasa_ƙasa ta dinga jin ana kiran *MUNEEBBA*

Da sauri ta ɗaura Alwalla kasancewar Magriba tayi,ɗaki ta shiga,tana shiga ta iske Mahaifiyarta ta taso tana daddafa bango,Alamar tana son fitowa tayi Alwalla,Da sauri taje ta kamata tana faɗin “Mamma ki daina tashi ke kaɗai kinga, ga ciwon ƙafa sannan ba gani kike ba,kuma kije wajen tashi ki zame ki ƙara jawo wani ciwon,na ce maki idan zaki tashi ki dinga
kirana,” ta faɗa a shagwaɓe tana turo ɗan ƙaramin bakinta,

Murmushi mai Sauti Mamma ta saki,tana faɗin “MUNEEBBA baki gajiya da Rigima,yanzun dai taimaka man nayo Alwalla nan,naji hadari ya taso,”

 

Kamata MUNEEBBA tayi ta taimaka mata tayo Alwalla,Suna fitowa suka shiga ɗaki suka kabbara Sallah,Sun daɗe Suna kaiwa Allah kukansu,

Bayan Sun kammala Sallar ne MUNEEBBA ta tashi ta shiga kichen ɗin ta ebo masu Abincin da zasu ci, da Kuma na Khabir, zuwa tayi ta ajiye a gaban Mahaifiyarta Sannan ta dinga ebo Abincin tana bata,Saida ta ƙoshi, Sannan ta fara eba tana ci itama,saida ta ƙoshi, Sannan ta tashi ta wanke hannunta tana kauda kwanonin da suka ci Abinci,tana gamawa sai ga Nepa an maido,ta haska ko ina,ƙura ma,kyakkyawar Matashiyar da ke tsaye Ido nayi,don ganin Madarar kyau a gurinta,
Doguwar Mace ce wacce ta haɗa tsayi da ƙwari,ƴar duma_duma da ita, ga dara_daran idanu,da zara_zaran gira, hancinta mai tsayi dai_dai misali sai ɗan Cute ɗin bakinta pink lips,fara ce,amma ba irin can ba,ga gashi da ya kwanta yai Luf_Luf a gaban goshinta,da Saje,
Kyawu kuwa Allah ya bata saidai muce Alhamdulillahi da Masha Allah,

Kallona na maida ga wata dattijuwar Mata,dake Zaune, ta tanƙwashe ƙafafunta,itama kyakkyawar mace ce, Fara ƙal da ita don da ka ganta kaga cikakkiyar buzuwa,ga idanunta dara_dara don idan ka kalli idanunta baza ka, taɓa cewa bata bata gani da su ba, Saboda buɗe suke tarau dasu, itama,da ka kallesu Mamma da Muneebba suna kama Sosai saidai Haske da Mamma ta ɗarata,ga diri ba’a cewa komai kanshi,

 

 

Tana Tsaye ne taji an tafka mata Dundu a baya, juyowa tayi a hanzarce tana faɗin “Kai fa Yaya Khabir wallahi ƙetarka tayi yawa kana shigowa kawai sai ka wani sakar man Dundu a baya,” ta faɗa kamar ta fashe masa da kuka,

Fashewa da dariya yayi yana faɗin “Nifa kawai gaisuwa ce na miƙo amma har zaki gwada mana halin auta,”

 

Kallonshi tayi tana turo baki tana faɗin “nidai yanzun ina Alƙawarina? wanda ka ce zaka tafo man da shi,”

Kallonta yayi yana faɗin “Au ke nayi mawa ma kenan? Ni Mamma nayiwa bake ba,” ya faɗa yana tunkaro inda Mamma ke zaune,yana Zuwa ya zauna kusa da ita yana Mammatsa mata ƙafafu,Murmushi tayi tana dafa kanshi tana faɗin “Allah yai maku Albarka Khabir haƙiƙa kunyi man Abinda dukkan ƴaƴa ya kamata ace sunyi wa Mahaifansu yadda kuka yi man Ubangiji ya baku mai yi maku kuma,”

Da Ameen Suka Amsa Khabir na faɗin “Mamma koda yaushe cikin sa mana Albarka kike, tabbas munyi dace da Mahaifiya ta gari wacce ta zauna ta bamu tarbiyya ta ilmantar damu, Sannan dukda Zagin da ake mana a gari na cewar mu dukkammu bamu da Uba,hakan baisa kin bi takan zantukan Mutane ba kikan haƙuri ki danne wa Zuciyarki,kota wannan ɓangaren kin koyar damu iya Zama da Mutane Sannan Uwa Uba haƙuri da juriya,

 

Ƙara Shafa kanshi da na Muneebba tayi tana faɗin “Saka Albarka wa Yaranka a koda yaushe shine zai sa Allah ya kareshi daga dukkan wata taɓarɓarewar Rayuwa, Tabbas wasu iyayen suke Rusa Rayuwar ƴaƴansu da kansu ta hanyar zagi da la’anta, zaka ga Abinda baikai ya kawo ba, Uwa zata jefi yaronta da Mugun kalami, kuma wannan babban kuskurene mu iyaye muke aikatawa,zaka ga yaro Tun yana ƙarami, Idan yai wani abun zata kirashi Sakarai, ko ɗan banza da sauransu dai,haka zalika tarbiyya ita ce jigon Rayuwa, tabbas duk macen da bata ma yaranta tarbiyya ba bata ceto Rayuwarshi daga hanyar lalacewar zamani ba,kuma ki sani duk wani Abu da kika ɗora yaronki da shi to tabbas da kalar halayyar zai tashi, idan hallayar kirki gareki to da ita zai tashi ko kuma akasin hakan,haka haƙuri shine jigon rayuwar zaman duniya,indai kana da,haƙuri tabbas zaka ci ribar rayuwar zaman duniya, duk mai haƙuri zai dace,sannan juriya da jajircewa kan abinda yake dai_dai,shine zai sa kakai dukkan wani mataki na Nasara wanda yake dai_dai,sannan ina sake gargaɗarku da karku sake ku biye Zancen ta Mutane,Don idan ka biye ta mutane wannan shi Ake kira ba shiga ba fita wai an saka mahaukaci a gadin ƙofa,”
Mamma ta ƙarashe zancen da sakin Murmushi,

Dukkansu Ajiyar Zuciya Suka sauke Suna mai tsananin jin ƙaunar Mahaifiyarsu, gefe guda ga kuma tausayin halin da Suka tsinci kansu a ciki, dogon numfashi Khabir ya sauke yana faɗin “shiyasa a kullum muke ƙara gode wa Allah muke kuma ƙara gode maki, bi ga hanyar Turbar da kike ɗoramu,”

Murmushi Mamma tayi tana faɗin “ga kiran Sallar Ishsha’i can Maza tashi ka tafi Masallaci, Sannan ka dawo kaci Abinci,”

 

Da To ya Amsa yana miƙewa,Sannan yace “Auta tashi ga Alƙawarinki na kawo maki, Sannan kije ki dafa man Ruwa ina son dana dawo nayi wanka,” ya faɗa yana miƙo mata ledar hannunshi,

 

Amsa tayi tana zabga mashi godiya har sai da ya ɗallar mata baki sannan tayi shiru,

Yana fita ta ajiye ledar ta Taimaka ma Mamma ta tashi suka kabbara Sallah, saida Sukayi Shafa’i da Wutiri Sannan Muneebba ta tashi ta haɗa ma Khabir Ruwan wanka,tana gamawa yana shigowa,kai Tsaye bayi ya shige, ita kuma ta dawo ɗakin ta Zauna tana jawo ledar da Khabir ya bata, Tana buɗewa ta haɗiye wani miyau don ganin balango mai zafi ga sai ƙamshi yake,ɗaukar Naman tayi takai bakin Mamma, kaucewa Mamma tayi tana faɗin “Auta ki ci Ni na ƙoshi,”

Ɓata rai Muneebba tayi kamar Mamma na ganinta,ta ce “Mamma idan dai baki ci ba Allah nima bazan.ci ba,”

Jin hakan yasa Mamma amsa don tasan muddin bata ci ba itama Muneebba baza ci ba, saida suka cinye tare da Mamma Sannan Muneebba ta ƙyale Mamma,Ruwa masu sanyi a randa ta ebo mata tasha sannan itama tasha,

 

 

 

Koda Khabeer ya fito ya zauna ya gama cin Abinci Sannan ya zauna wajen Mamma tanata basu labarirrika masu daɗi,wanda cikin labaranne take ƙara Nusar dasu Abu mai kyau da kuma Marar kyau,
Sai wajen 9:30 sannan Khabir yai masu Sallama
ya shige ɗakinshi don yin Bacci.

Itama Muneebba Zuwa tayi ta ɗaura musu Net Sannan ta zo ta kama hannun Mamma tana taimakamata ta shige ta kwanta,Suna kwanciya ana ɗauke Nepa, Saboda iskan da ake tayi, maƙalƙale Mamma Muneebba tayi tana jin tsoro, a ɗaɗɗare bacci ya ɗauketa, ita kam Mama bacci ya kasa ɗaukarta,Tunaninka ta dunga yi, wanda ya dinga Tuna mata Rayuwar baya,tunawa tayi da yadda kullum yaranta ke cikin hantara da kuma zagi na cin Mutumci,ga kullum a cikin yi masu gorin Uba ake duk ta sanadiyyarta,hawaye ta dinga jin na bin kuncinta

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected