KALBIM BOOK 1 PAGE 39
39
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/IyDlSVdw1rDIlCNNQMel68
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494
***************
Neman toshewa kirjinsa yakeyi yana jin numfashinsa na neman yankewa idanuwansa sukai jajir ya daga hannunsa daqyar baya gani sosai ya kamo wayarsa dake yashe a qasa ya saka kiran fahad sedai kafin fahad din ya dauka numfashinsa ya sarke a gurin.
Fahad na dauka cikin girmmawa ya fara magana yaji shiru.
Cire wayar yayi daga kunnensa ya duba yaga kiran na tafiya ya sake dorawa kan kunnensa yana ambatar sunansa da girmamawa.
Jin shiru saiya kashe ya saka kiransa tafara ringing harta katse baa dagaba
Sake saka kiran yayi yana kallan time kafin ya juya kan motarsa kawai zuwa LIMBAs din batareda ya dena kiran wayar ba.
Koda ya iso Babu wanda ya fito gidan tsit hakama baa zuwa bangaren AY sbd a ciki yake sosai bare yaje yafara kai masa gaisuwa dan haka Fiddausi da masu aiki ne sukai masa barka da zuwa dayake shima kowa a gidan ya sansa tinda duka yaran Limban ne.
Amsawa kawai yayi ya nufi bangaren Sayd
yana isa so daya yayi knocking kafin ya bude kofar bedroom din nasa.
Abinda ransa ya basa na cewan ba lafiya ba ne yaci karo dashi sbd a kwance Sayd din yake a qasa yana kokarin samun attack sbd numfashinsa dake kokarin yankewa sbd shock.
Da saurin gaske Fahad yayi kansa yana ambatar sunansa tareda basa taimakon gaggawa sbd kada numfashin nasa ya yanke sedai kaman hakan bazaiyiba dan haka da sauri ya kamasa ya maidasa kan lafiyayyan gadonsa dake dakin ya daga wayarsa da sauri yana kiran dr.
Yana samun likita da sauri ya sanar dashi suna buqatan taimakon gaggawa a gidan.
Yana kashe wayar kansa ya koma yana kokarin taimaka masa gurin saisaituwan numfashin yana miqewa da sauri ya dauko abu yana fifita masa sbd ya samu iskan shaqar sbd kamanma suffocating yake.
Andauki mintina sosai kafin dr Raheem ya iso gidan wanda zuwansa ne yasa mutan gidan suka san abinda yake faruwa dan haka cikin tashin hankali mama da Fiddausi sukayo dakin bayan maman ta kira wayar AZIZ ta sanar dashi Sayd ba lafiya.
Kansa dr Raheem yayi da sauri yana kallansa yasan attack ne ya samu…
AZIZ dinne shima ya iso dakin a natse babu walwala a fuskansa Kallansa mama tayi cikin kulawa da damuwa tace
“Kaima kaman bakada lafiyar AZIZ,
Lafiya kuwa?
Jamaa meyake faruwa?
Baice komaiba ya nufi Sayd din wanda Dr Raheem ke dubawa yana ambatar sunansa cikeda kulawa.
Gefe Fahad ya matsa cikeda girmamawa yana masa barka da fitowa.
Amsawa yayi yana kallan Sayd din ya jefawa Fahad tambayar
“Me faru?
Meya samesa?”
Dagowa Fahad yayi yana kasa kallan AZIZ din dika yace
“Bansaniba,mungama waya dashi akan reports da profiles na Doctors da aka buqata ne dana turo masa,
Sai kuma daga baya ya sake kira ya tambayeni qarin bayani akan daya daga cikinsu na fada masa abinda na sani akai wanda it seems like ya sansa kokuma makamancin hakan sai kuka gashi ya sake kirana banaji koda na iso na samesa ya samu attack so i called Dr Raheem”
Shiru AZIZ din yai yana sake maida idanuwansa akan Sayd da idanuwansa sukai jajir numfashinsa ya fara daidaituwa sedai yaqi dago kansa ya kalli AZIZ din wanda yake nazartan yanayinsa sbd kaf duniya a yanzu bayajin akwai abinda zai saka Sayd din samun attack yanda zuciyarsa ta kangare ya zama wani irin me tsananin karfin hali dan haka koma menene akwai abinda ya sakasa samun attack din lokaci daya.
Kan Dr Raheem ya maida idanuwansa dake juyawa ahankali ya bude baki a natse yace
“Yaya?All good,right Dr?
Juyowa Dr Yayi ya kalli AZIZ din yana dan sauke numfashi yace
“Yes attack ne due to shock kawai ba komaiba amma yanzu insha Allah zai daidaita tinda numfashinsa ya dawo daidai”
Numfashi me sanyi da nutsuwa ya sauke yana kallan Sayd din yace
“Ka kashe wayoyinka ka huta dakyau coz lafiyanka na gaban komai ka kula,Allah ya tsare gaba”
Gyada kai sayd yayi yana kasa dagowa sbd sam baya iya ko hada ido da AZIZ din sbd tsoro ma yakejin yana rufesa da wata irin tashin hankali na fargaban abinda zai iya biyowa baya idan abinda yake gani yana shirin zama gaskia
Juyawa sukai kowa ya fice daga dakin dan barinsa ya huta ko zai sake warwarewa.
Fahad kadai aka bari wanda Sayd ya dago jajayen idanuwansa ya kalla yana sauke wani nannauyan numfashi mara karfi sbd karfinsa da yayi kasa sbd attack din.
Fahad ma kallansa yayi cikin kulawa yana sake masa sannu ya tattara ipad dij sayd din da qasu abubuwan da suka zube ya sauke ya dauka a table dayake tsakiyar dakin yana kallan time yace zai tafi yaji da office tinda yau daga shi har Ogan kwata kwata bame shiga office din.
Cikin nauyin muryansa datai kauri sosai sbd nauyin dayakeji a kirjinsa na tsoro da tashin hankali tareda wani irin masifaffen tiriri da zafi ya bude baki yakira Fahad din.
Dakatawa yayi tareda juyowa yana dawowa cikin girmmawa ya bude baki zaiyi magana Sayd ya katsesa da cewa
“Dr Abraham a wane asibiti yai aiki a Nigeria??
Ipad dinsa ya koma motarsa ya dauko ya dawo yana bude duka bayanan daya samu akansa na fili dana boye ya fara karanto masa
“ZAADEN HLTH CEN/SPEACIALIST,
Yayi aiki tareda Dansa kaman yanda na fada maka,
Yanada kusanci da ZAADENs sosai coz sun zama tamkar family”
Shiru Sayd yayi yana shiga tinani kafin ya sake bude baki yace
“Alaqar menene a tsakaninsa dasu da suka samu kusanci? I mean wane hulda ne tsakaninsu?
Is he a business man apart from being a Doc??”
“Nope” fahad ya fada yana sake duba profile din Dr Abraham din dakyau wanda aka hada aka turo masa.
Dagowa Sayd yayi ya kalli fahad yana sake shiga tinanin dayake nauyaya kansa ya bude baki yace
“Shine family doctor na ZAADENs kenan?
Yes”
“Meya hadasu da likitan zuciya da iya aikin zuciyar ya sani dazai zama family doc dinsu wanda har suka taho dashi qasarsu?
“I don’t know that Boss Amma akwai yiyuwar sunada patient me heart problem din shiyasa ya zama family but…..
Katsesa Sayd yayi cikin Wani irin sautin daya saka fahad din kallansa da sauri..
“Inason full background details na ZAADENs tin daga Kakansu asalin Zad din har zuwa yanzu,
Inason medical history da health status dinsu da komai,
Idan nace komai ina nufin har wanda bai kamata a saniba inason full dets,
Ko nawa zaa kashe ina son samun wannan bayanin komai kada a bari kota yaya koda hakan na nufin kidnapping wani ne i mst get the dets”
