KALBIM BOOK 1 BY MAMUHGEE

KALBIM BOOK 1 PAGE 38

38
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494

*********
Koda ya shige bayan yayi shirin bacci cikin kayan bacci masu santsi zaunawa yayi yana lumshe idanuwansa Sanyin Ac na ratsasa ahankali sbd babu alamar bacci a tareda dashi tinani me zurfi da mutuwar jiki ya rufesa duk da bazai taba sakin kari ba akan ciwon nata zaiyi yawon duniya ya nema mata lafia sedai idan Allah yayi itama barinsa zatai tukuna amma yana roko da fatar Allah yasa ya fara barin duniya idan har Ciwon nan mai dauketa ne daga duniyar karta barsa..

Sayd kuwa saida yasha magani me karfin gaske kafin gaske kafin bacci ya iya daukansa.

Da asuba bayan sunyi sallah kowa ya koma bacci
Guraren 8 na safe wayar Sayd ta tadasa bacci kansa da yayi masa nauyi sosai sbd maganin daya sha ya daga yana bude idanuwansa daqyar ya kai hannu ya dauki wayar yana dorawa a kunnensa.

Fahad ne cikin girmmawa yace

“Goodmorning Boss,
Duka bayanan daka nema an hada na turo maka ka duba hotinansu da bayanansu tareda sunayensu suna nan”

“Ok,thanks zan duba yanzun nan,i will get back to you akan sauran bayanin”

Ok boss”

Kashe wayar yayi yana komawa bacci sbd koya duba babu abinda zai gane yanzu dan maganin dayasha bai sakasa ba ko kadan.

 

***********Ahankali ta tashi daga kwancen datake idanuwanta biyu ba bacci take ba ta jima da farkawa kawai tashin ne ta kasa sbd a macen da jikinta yake da tinanin fuskan data kasa gogewa daga idanuwanta,

Tinda ta dawo Nigeria ta rasa gane kanta da abinda ya maqale mata a tinani da ido wanda take ganin Shedan ne hakama tsananin ciwo da zafin hakan takeji sbd zuciyarta kwata kwata bata yadda tayi tinanin kowane namijin ba bayan Ammar Zad.

Numfashi me sanyi ta sauke ahankali tareda lumshe fararen idanuwanta ta budesu tana daukan wayarta ta qurawa hoton Ammar dayake gaban wayarta ido tareda Ambatar sunansa ahankali tace

“Ammar zad kai kadaine wanda zuciyar Jannah Zad ke so,
Kaine mijina,kaine farin ciki na,kaine abinda kawai nake buqata zuciyata ta kammala”

Rufe idanuwanta tayi ta bude tana ajiye wayar tareda ziro kafafunta qasa tana miqewa tsaye sanye da kayan bacci riga da wando masu kauri ta nufi toilet tana dafe zuciyarta dake bugawa ahankali tana jin kaman kalamanta ba daga zuciyar taya suka fito ba iya bakinta ne.

Numfashi me qarfi ta sauke tana qarasa shigewa toilet din dan fitar da tinanin komai a zuciyarta.

Brush tayi tana kallan fuskanta a jikin mirror wanda tayi fayau sbd tashinta kenan.

Tana gamawa zare kayan jikinta tayi tana qarasawa bathtub ta kunna ruwan dumi ta shige.

Ta jima kafin ta fito daure da blue towel ta nufi wayarta dake ringing ta duba taga sunan MAN dinta ne dan haka ta dauka tana zaunawa gaban mirror da wata muryan data sakasa ajiye Ipad din datake hannunsa yana duba sako ya ajiye akan table dayake gabansa na bedroom dinsa yana jinginar da bayansa muryan na kashe kowane irin kuzarin jikinsa da zuciyarsa yace

“How are you Love??
Kin tashi?

Numfashi me sanyi ta sauke tana kallan fuskanta tace

“Goodmorning Love,
Na tashi ina shiryawa am coming out for breakfast”

“Ok take your time and kinsha maganinki kuwa?

“Yes love” tafada tana kallan drawer din da maganinta suke ciki.

Aje wayar sukai yana cewa ta kula gurin shiryawa kada ta wahalar da kanta.

Shiryawa ta fara yi a natse tana gamawa ta saka free skirt da riga na Dior da scarf ta ziro flat versace ta fito riqe da wayarta wani lafiyayyan qamshi na tashi a jikinta na woodyLeather.

Kai tsaye palon Dad ta nufa wanda yake palon zaune yana waya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali tareda manyanci da Duniya data gama tsaya masa.

Yana ganinta ya bude mata hannunsa daya ta qaraso ta zauna kusa dashi tana rungume hannunsa a jikinta ta bude baki cikin tsananin kaunarsa da sakewan datake tsakaninsu duka familyn tace

“Goodmorning BestDad” (hakan itama take kiransa tin tana qaramarta)

Murmushin farin cikin ganinta kafai da yayi ya fara sakewa kafin ya kashe wayar dayake yace

“Morning My Angel,
Kin tashi lafiya?
Yaya maganinki kinsha kuwa?

“Nasha kaima kasha naka Bdad?

Amsawa yayi da cewa yasha yana murmushin jin dadi..

Shigowan Mimi ne ya sakata sake lafewa gefensa tana murmushi tace

“Goodmorning Mimi,
Kin tashi lfy?

Qarasowa tayi tana zaunawa gefen dad din tace

“Lfy kalau,kinsha maganinki?

Yes” tace sbd tasan kowa a familyn babu ranar da babu wanda baya tambayar tasha maganinta.

Ko gama magana da Mimi bataiba qamshin Ammar yafara shiga hancinta ta dago idanuwanta ta zubawa kofar sai gashi ya sako kai cikin wani irin class da nutsuwa sanyeda Ash balmains.

Maheer ne shima ya sako kai tareda Anny tana gafensa kowannensu yana fidda nasa kalan qamshin na shegun designer Turaren dasuke amfani dasu masu tsadan gaske.

Akan Ammar idanuwanta suke tana jifansa da kallan daya sakasa zuba mata nasa idanuwan yana jin idan da ya rasata a bayan da yanzu baya duniyar dan wlh bazai iya rayuwa babuta,

Wani irin masifaffen sonta ne Allah ya halitta masa a zuciya da kirjinsa da ko tinanin rasata kadai idan yayi yake qarewa a hannun therapist dinsa sbd zarewa yakeyi gaba daya da iya wannan tunanin dan hakanne yasa yariga yasan babu rashinta a kundinsa saidai idan karshen tasa rayuwar ne yazo dan hakan ne bai taba jin komaiba a rayukan da suka hallakar dan nema mata zuciyar datake bugawa a kirjinta hakama da yau zaa ce wannan dinma ta gaza to tabbas zai koma farautan zuciyoyin mutane matacci da rayayyu dan nema mata lafiya kawai.

Gefen Miminsa ya qarasa ya zauna yana kallan dad da murmushi da farin ciki a fuskansa yace

“Goodmorning Dad”

Amsawa dad yayi yana amsa gaisuwan Maheer shima kafin ta Anny wadda itama ta zauna gefen mijinta.

Saleem ne ya shigo karshe yana waya fuskansa gabaki daya ba walwala.

Kallansa sukai ganin yanayinsa ya saka yana gama wayar Maheer ya kallesa yace

“Issue din Approval na wanda kakeson ne ko yaya??

Wayarsa ga ajiye gefensa yana sauke numfashi me zafin gaske yace

“Yes,sunata rejecting din proposal dina batareda ma an tsaya andubaba”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected