Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi'ar Zuciya 4

********
Tafiyar mintina talatin a qasa suka qaraso gidan tsohuwar wato inna,tun kafin sukai ga shiga zauren gidan ran kaltum ya gama baci,idan tana qaunar mutuwarta to tabbas tana son shiga cikin gidan,a duniya babu abinda ta tsana irin zuwanta gidan,saidai don bata da yadda zatayi ne,ba yadda ta iya,haka tabi bayan ummanmu suka sanya kai cikin gidan.

Filin tsakar gida ne babba kamar nasu,saidai su nasu wannan malale yake da sumunti,a share yake fes saboda badai tsafta ba tsohuwar,daga hagunka madafa ce wadda da bandaki daga kusa da ita,wanda akillace suke a gyare ba kamar na sauran al’ummar karkara ba,da yawancinsu a bude suke,hakanan zaka samu tarin turbaya,daga daya gefan hannun damanka dakuna ne a jere,ginin bulo,wanda aka yi musu rumfa gaba daya gaban dakunan,saboda kare rana da kuma zama saboda shan iska,da kuma zama yayin saukar ruwan sama da sauransu.

A qasan rumfar kuwa tabarma ce babba a malale,sai filo daga bayan tsohuwar wadda ke zaune riqe da mafici tana firfita,daga gabanta danta ne zaune wato qani ga mahaifiyar kaltum wanda suke kira da kawu ado,kusa dashi yaransa ne maza guda biyu,bisa dukkan alamu zuwa sukayi dubata,sai jikokinta guda biyu yaran kawu sama’ila suma,kusan sa’anni suke da kaltum,duk da cewa tadan girme musu da watannin da basu wuce hudu ba.

Sallamarsu ce dukka taja hankalinsu,suka amsa musu kafin su gama fahimtar su waye,tashin farko fuskar innar ta sauya sanda suke qarasowa saman tabarmar don yiwa kansu masauki,cikin qanqanin lokaci walwalarta ta ragu,sai kawu ado ne ke maraba da zuwan umman,fuskarsa a sake yana matsar da yaransa gefe don ta samu wajen zama
“Yanzu nake shirin yin maganarki yaaya,tunda nake zuwa ban taba samunki ba,duk sanda nazo kuma inason qarasawa wajenki,sai hira tayi hira nida inna lokaci saiya quracemin,hakanan nake juyawa na koma” fuskar umman a washe,cike da jin dadi yadda har kwanan gobe ado na daya daga cikin jama’ar dake girmamata,gami da ganin mutunci martaba da qimarta,kafin ta bashi amsa innar ta magantu,cikin sautin dake nuna zafinta
“Yo me zakaje kayi mata?,me xaka ce mata ma?,yau gashi tunda akwai rabo kun hadu” duka sai suka kalleta,hatta da jikokin nata fatsima da kubra sai da suka waiwaya suka dubeta,amma ba wanda yace komai,tunda halin innar bawai sabon abu bane a wajensu,hakanan wannan ba baquwar dabi’a bace,don haka umma ta maida hankalinta kan innar tana matsawa kusa da ita,muryarta cike da ladabi ta ambaci
“Ina yini inna?”
“Lafiya” ta amsa a gajarce
“Ya qarfin jikin naki kuma?”
“Mun godewa Allah” ta sake fada a dake,maficinta yana hannu tana kadashi a hankali,ta lanqwasa qafarta ta dama ta dorata saman gwiwar qafar hagu,idanunta kuwa ko sashen da umman ke zaune bata duba ba,duk da haka umman saita dora
“Ban sani ba inna,sai da salisu yazo maqwafta sannan ya shigo ya gayamin,kusan sati inna amma ba’a aiko an gayamin ba?” Wani banzan kallo ta watsa mata
“Idan an aiko mikin me zaki tsinanawa mutane,zuwanki da rashinsa duk daya fa zuwaira” sunkui da kanta kawai umman tayi,tana ji ranta yana mata suya,yayin da kaltume ke gefe tana qoqarin tausar zuciyarta,kada ta furta wa inna maganar da tasan umman ba zataji dadinta ba,shuru ne ya dan wanzu kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa,muryar kaltum tana gaida kawu ado ita ta katse shurun,fuska a sake ya amsa mata ya dora da cewa
“Ku dinma kaltume ba’a ganinku?,kuda umman naku duk kunqi zumunci,idan ita batazo ba aiki kwazo ko?”
“A’ah ado…..dakata,banason kwashe kwashe,na meye sai sunzo gidanka sun matsanta maka kaida iyalinka sun dora maka nauyi,ni banason irin haka”
“Inna naga….”
“Kaga me?,kar na sake jin bakinka,mara kunyar yarinyar,data shigo ma kaga ta gaisheni ne?” Tasan da wannan zata fake dama,don haka tayi wuf ta gaisheta,sai data gama sheqar iska sannan ta amsa mata,daga daya itama kaltum din bata qara ba,saita waiwaya suka soma magana dasu fatsime,inna kuma sukaci gaba da hirarsu da ado,duk da jefi jefi yana sanyo umman,saidai bata fiya tankawa ba,sau tari saidai tayi murmushi kawai,daga bisani saita ja daya daga cikin yaran adon ta soma hira dasu.

Tun hirar batayi nisa ba fatsime tace da kaltum
“Don Allah ranar saukata kuje da wuri keda habiba,sai kuyita dari dari ku kam,kamar bakuson shiga mutane?” Duban fatsime tayi da mamaki saman fuskarta,don su kam sam basusan da wani batun sauka ba,kafin tace wani abu innar ta rigata
“A’ahhhhhhh….fatsima?,suje da wuri suyi miki me?,wai ni don Allah don annabi sai yaushe zakuyi hankali?,kuyita kalan dangi kuna jajibowa kanku nauyi?,wai meye alaqarku dasu kattume ne?,mantawa kukeyi iyayenku uwa kawai suka hada dasu basu hada uba ba?,kunga wannan….” Saita nuna kawu ado da yatsa
“Shine shida yaransa dolenku,sune suka hada uwa da uba da uwarku,sune abokan yin zumuncinku….”
“Haba inna….haba inna,don Allah ki daina irin wannan abun,baifa kamata ba,ina cewa dukkanmu ‘ya’yanki ne,daga cikinki muka fito?,su kuma duka jikokinki ne tunda ke kika haifa iyayensu,kowanne mutum a rayuwa da kalar rayuwar da Allah ya nufata xaiyi,hakanan kowanne da irin arziqinsa,don Allah don annabi inna ki daina,abun bayamin dadi”
“To ubana,idan ka gama wa’azin saika gayamin” tace tana tsareshi da ido,ransa ya baci don haka kawai ya miqe tsaye yana laluba aljihunsa tare da umartar yaran nasa dasu tashi,kudi ya ciro masu yawa ya duqa ya ajjiyewa innar a saman filon dake ajjiye a gefanta
“Gashi,a qarasa siyan abinda babu” caraf ta dafe kudin,bakinta har kunne,kai kace ba itace ke zabga bala’i ba yanzu,tahau godiya da sanya masa albarka kamar zata maidashi cikinta,saita soma cewa yaran su wuce susa takalmansu,shima ya shige ya tafi sanda taga yana maida hannunsa aljihunsa,da alama wasu kudin yake lalubowa.

Ilai ashe kuwa ta fahimci abinda yakeson yi,su fatsima ya miqawa kudin yana cewa
“Gashi kwayi kudin mota” sai tabi kudin kawai da kallo ba tare da tace komai ba,saboda ta sani cewa suma tana morar uwarsu,ya sake dauko wasu ya miqa saitin inda umma da kaltum ke zaune yana cewa
“Yaaya,gashi wannan ba yawa…..” Kafin ya qarasa inna ta yunquro zata cafkesu,tuni kaltum ta fuskanci nufin innar,don haka kafin ta kai ga qarasawa ita nata hannun yakai,ta amshe tana fadin
“An gode kawu ado” yayin da inna ta cafki iska,shima ya fahimta abinda yaso faruwar,kuma hakan da kaltum tayi yayi masa dadi,don haka yayi gaba yana sanya takalmansa,yayin da innar ta tsiri mitar babu gaira babu dalili
“Yanzu kai ado saboda rashin sanin ciwon kai,wannan uban kudin haka ka dauka ka baiwa zuwaira?,yarinyar da zuciyarya ta riga ta mutu?” Baice komai ba illa
“Inna Allah ya baki haquri,sai anjima,Allah ya qara lafiya” ya juya ya fice abinsa.

Kamar jira take ya fita kuwa ta dasa bala’i da masifa kan umma da kaltum,kai bakace ita ke jinya ba,koda yake bahaushe yace sabo dayi……wai gawa da gatsine,kusan masifa da bala’i a jinin inna take,kaf jama’ar unguwarsu babu wanda bai sara mata ba,macace mafadaciya da kowa yasan da zamanta,uwa uba mutum ce ita maison abun duniya,wanda duk girma ko qanqantarka matuqar kana da abun hannunka to kaine mutum kuma abokin huldarta.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected