Dabi'ar Zuciya 4
A daren ranar idan tace tayi isashen bacci to tayi qarya,haka ta dinga baccin rabi da rabi,abunda ya faru ne kawai yake dawo mata daya bayan daya,ta fuskanci kaf rayuwarsu qalubale ne a cikinta kala kala,tako wacce fuska akwai kalar jarrabawar dake fuskantosu,ko sai yaushe al’amura zasu daidaitan musu kamar kowanne mutum?,amsar data kasa lalubowa kenan,har xuwa wayewar gari,sanda ta tsinci muryar ummansun saman kanta tana kiran sunanta.
A kasalance ta miqe,cikin yanayin barcin da bai ishi mutum ba,ta zauna sosai tana murza idanu,tana kuma duban umman nasu,ganinta sanye da hijabin da takan sanya idan zata je wata unguwar
“Ki tashi hakanan…..matar malam ta aiko kije kiyi mata kitso,nizan fita,zanje dubo inna”
“Inna kuma ummanmu?” Ta tambaya cikin mamaki tana duban fuskarta,don ta sani cewa ita dinma aiba isashshiyar lafita gareta ba,ciwo ne a qafarta wanda kullum yake ci gaba,take kuma neman kudin maganin da zatayi,saboda lokitocin cikin gari da suka ja kunnenta kan ta gaggauta yin maganinsa,yin jinkiri ko wasa dashi zai iya haifar mata da komai,ciki harda rasa qafar tata ma gaba daya,to amma ko a mafarki,koda wasa basu taba ganin gilmawar inna cikin gidan da sunan tazo dubata ba,hasalima a kafatanin rayuwarsu xasu iya lissafa sau nawa suka taba ganinta tazo gidan nasu,kallonta umman tayi sosai tana karantar yanayin fuskarta
“Eh ita,ashe kwana biyu bata jin dadi,sai dazu Allah ya kawo yaron nan salisu na kusa dasu yake gayamin” sosai ran kaltum din ya baci,wato kwata kwata mahaifiyar tasu ma bata da darajar da za’a aiko a shaida mata bata da lafiya,sabida bata da abun duniyar da zata bata,tana da yaqinin inda rahama ko zaliha ce koda babu aike innar zata je da jan gindi da kanta ta sanar musu,qoqarin miqewa kawai kaltum tasoma yi,don ba zata bar umman tasu ta tafi ita kadai ba,gwara suje tare,duk da wanzuwarsu a wajen babu abinda xai hana na daga abinda inna tayi niyyar aikatawa akan umman tasu,amma dai biyu tafi daya
“Umma don Allah jirani ja watsa ruwa kawai muje tare”
“A’ah….to kitson fa da ake jiranki kiyi?” Umman ta fada tana binta da kallo,a lokacin har takai bakin qofa
“Zan aika habiba ta basu haquri,idan muka dawo naje nayi musu” saita qara wuta ta fita da sauri don ma kada umman ta sake tsaidata.
Nannauyar ajiyar zuciya ta saukar,tasan abinda yasa kaltum ta nace saita bita sun tafi tare,saboda tafi kowa sanin yadda dangantaka keda tsami tsakaninta da innar,duka sabili da ita,abinda kuma take gudarwar kuma babu abinda xai hana faruwarsa sai wani ikon na Allah,ta sani duk cikin yaranta babu me kishin uwa da qawa zucinta irin kaltumen,bata iya bari ko qyale abinda xai tabata koda za’a yankata ne kuwa,mutum guda take iya daukewa kai,tayi masa wannan alfarmar shine mahaifinsu.
Cikin mintina qalilan ta shirya,duk da yadda take da nauyi wajen yin wanka da sauransu,ta iske umman tasu na barwa habiba sallahu
“Ba dadewa zamuyi ba,yanzu zamu dawo”.
Ta baya sukabi suka yanka,don a qafa zasuje,duk da cewa akwai tazara yar kadan tsakaninsu,to amma babu abun hawan dake zirga zirga daga nan zuwa can,duk da cewa koda akwai dinma babu kudin da zasu hau.
Umman tasu ce tayi mata dole saida suka biya ta qofar gidan matar malam,ta shiga ta shaida mata zata raka ummansu anguwa,amma idan suka dawo ta nan zata biyo tayi mata kitson,sannan ta fito ta samu umma dake tsaye tana jiranta suka ci gaba da tafiya,gefan zuciyarta wani rauni na ratsata,duk sanda zata daga idanu ta kalli umman tasu sai taji wani madaukakin tausayinta yana ratsata,tako ta ina ita din abar tausayi ce,har gwara su suna da uwa irinta.
Sun danyi nisa kadan sukaji ana fada cikin qanqan da murya
“Barka da warhaka umma” a mamakance suka juya dukansu,yusufa ne,daya daga cikin matasan qauyen,wanda yana daga cikin matasan da aka yiwa shaidar nutsuwa da hankali cikin qauyen,ya qaraso kana ya duqa har qasa yana gaida umman,ta amsa cikin fara’a da sakin fuska,saita danyi gaba kadan yadda zata iya hangosu,xuciyarta tana bata sahunsu ya biyo ita da kaltume.
Ba’a rufa minti uku ba taga sunyi sallama ya juya ya nufi cikin gari,ita kuma kaltume ta nufo inda umman ke tsimayenta
“Waye wannan ne?” Umman ta jefawa kaltume tambayar sanda suke ci gaba da tafiyar,murmushi kaltume tayi
“Umma baki ganeshi ba?,yusufa ne fa dan gidan huwailan malam baffa”
“Af…af,saikuma da kika fada naga kamarshi da mahaifinsa….ai ban shaida shi ba,na kwana biyu ban ganshi ba”
“Eh….legas yake zuwa ya dawo,bai fiya zama garin na ba”
“Ma sha Allah,Allah ya taimaka…..” Ta fada tana son jin qarin haske game da tsaida kaltume da yayi,kamar tasan meke kai kawo a zuciyar ummantata saita ce
“Nifa nan babbar yaya ce,bakiga yadda yake gaidani ba cikin girmamawa” ta fada tana dariya,har hasken haqoranta na bayyana,wanda hasken rana suka qara masu sheqi,dan murmushi umman tayi
“Babbar yaya kamar yaya?”saida tadanyi dariya mai sauti sannan tace
“Habiba fa yakeso,wai don Allah na masa hanya ya sameta” shuru umman tayi tana dan qaramin nazari,a nata lissafin kaltume ce gaba,ita zata fara aurarwa kafin habiba,ko kum duka ta hada ta aurar dasu gaba daya,wala’alla walwalar da suka rasa cikin rayuwarsu su sameta a gidajen mazajensu,don bataga alfanun zamansu ba,dukkansu sun tasa,a karkarar sun isa aure,don an aurar ma da wadanda basu kaisu ba,to amma ita kaltume sam maganar aurenma kamar bai gabanta,har gwara jiya da abun nan ya faru taji tayi zancan nasiru.
“Ummanmu…..bakice komai ba,ko baiyi miki bane?” Kaltume ta fada da alamun sanyin jiki,sai umman ta sauke ajiyar zuciya
“Ba wanda bansan iyalan gidan malam baffa ba,yarane nutsatstsu duk da kuwa kusan duka yaransa maza ne,abu daya zuwa biyu kawai nakeso……banason ya fara neman habiba kansa tsaye,ya fara neman izini daga wajen mahaifinku sannan su gana,abu na biyu,kema inason ki shaidawa nasiru…..indai da gaske yake karya qara tsaiwa dake saiya nema izini wajen mahaifinku,saboda gujewa sake faruwar abinda ya faru a jiya” maganar umman tasu tana hanya,amma jin zafin abinda mahaifin nasu keyi ya sanyata ta zunbura baki
“Ni ummanmu baba mamaki yake bani,irin abubuwan da yakeyi umma kamar ba shine ubanmu ba,jarrabar yau daban ta gobe daban,anya kuwa shine ya haif…..” Faf! Taji an doke mata baki,wanda ba kowa bane illa umman tasu,cikin bacin rai take kallonta bayan ta dakata da tafiyar
“Kina cikin hankalin ku kuwa kaltume?…..sau nawa nake ja miki kunne akan irin wannan maganganun ne?,to bari kiji….” Ta fada tana nunata da yatsa
“Yau ya zamana itace rana ta qarshe da zan sake jin magana makamanciyar wannan ta fito daga bakinki,idan ba haka ba ranki zaiyi bacin da baki taba tsammani ba” saita juya zata ci gaba da tafiya tana qoqarin maida qwallar dake taso mata,da sauri kaltum ta cafki hannunta ta zagayo gabanta,itakam tunu qwallar ta soma zuba
“Kiyi haquri ummanmu,in sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba,na miki alqawari” ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,bata iya dogon fushi dasu,musamman kaltum din,dukkansu suna bakin qoqarinsu wajwn yi mata biyayya da kyautata mata,ta sani cewa a irin halin rayuwar da suka tsinci kansu dole akwai tarin bacin rai fushi da saqe saqe marasa ma’ana da zasuyi ta dawafi a qwaqwalwarsu,hakanan tarin damuwa zata yi musu yawa,idan tace zatayi fushi dasu me tsayi dukan saiya musu yawa su rasa na tarewa,amma hakan ba yana nufin zata sanya musu idanu tana gani su kauce hanya ba
“Ya wuce amma kada ki qara,saboda ke din kece babba a cikinsu,dukkan abinda kikayi zaya zame musu mudubi ne kuma abun koyi,dukkan wani tsanani yana tare da sauqi,hakanan kowanne yanayi bawa ya tsinci kansa me wuce wane,kuyita addu’a kuyita jurewa,Allah yayi miki albarka keda sauran ‘yan uwanki.


