Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi'ar Zuciya 4

Cikin sanyin jiki umma ta waiwaya ta dubi kaltum,ganin mitar innar taqi qarewa,muryarya can qasa tace da ita sanda inna ta miqe ta shiga bandaki,daga nan ma suna jiyo qananun mitocinta kamar ba’a makewayi take ba
“Kaltume…..baiwa inna kudin nan”
“Kiyi haquri ummanmu…..wallahi bazan iya bata ba” ta fada cikin qwarin gwiwar dasu fatsima suka bata
“Ashe ban isa dake ba?” Umman ta sake fada,wannan karon kubra ce data cika tayi fam tayi magana
“Umma,kiyi haquri,amma maganar gaskiya kaltume ta fi inna gaskiya,itafa inna maganar gaskiya hadamammiya ce kawai,umma saidai kiyi haquri,amma banda haka mu kanmu mama nawa ta bayar mu kawo mata?,amma da muka kawo ma gani take kamar mun rage wani abu ne a ciki,maimakon ma ta gode mana,maganar kaltum gaskiya ce,kada ta bada komai wallahi” shuru kawai umman tayi tana dubansu,ganin yadda suka hade kai suka daurewa kaltum qarqashi,a haka innar ta dawo daga bayan gidan,saita zauna tana duban umma
“Tashi ki shiga madafi,akwai tukunya,ki zubomin naman dake ciki” duk da cewa akwai yara a wajen,amma bata sanya kowa ba sai ita,amma ita umman sam bata damu ba,hakanan bata kawo komai a kanta ko a ranta ba,kasancewar inna uwa ce,ta isa da kowa,ta kuma isa ta sanyasu kowanne irin nau’in aiki ne.

Harta isa bakin madafar ta qwala mata kira
“Kinga daukomin tukunyar gaba daya,don ban yarda dake ba,an dade ba’a gamu ba,kada aje yimin dauki ɗai ɗai,a qulle a gefan zani,a tafi dashi gida” sosai maganar ta daki kaltum,ta waiwaya ta duba ta tabbatar umman tasu ta shige madafar,saita kalli innar
“Kinsan ai dama ana gadon hali fa”,innar ba qaramar yarinya bace,hakanan da hankalinta ras,shekaru kuma ba qarya bane,ta fuskanci me kaltum takeson fada a fakaice,don haka cikin mamaki take kallonta
“Kattume?,ni kike cewa barauniya?” Abun sai yaso bata dariya baya ga mamakin daya lullubeta,ashe dai abinda taso kiran tata mahaifiyar a gabanta kenan?,ashe dai abun babu dadi
“Yaushe kika ji na fada haka?,ni?” Ta fada tana nuna kanta.

Tun ba yau ba tasan halin kaltum sarai,cikin yaran zuwairan ita daya ce idan ka nunawa uwarta yatsa kokai waye saita lanqwasashi,don haka bata da mafita saita soma kwararawa umma dake qoqarin dauko tukunya kira
“Zuwaira…..zuwaira,fito fito” tunda taji kiran ta tabbatar wani mummunan abunne ya sake afkuwa,banda Allah ya taimaketa saura kadan tukunyar ta subuce saman ciwon dake qafarta,ta daukota ta fito da ita ta dire gaban innar,sannan tace
“Gani”ciki haki tsabar bala’i da masifar dake cinta ta soma nuna kaltum
“Dama takanas kika dauko diyarki kuxo ta cimun mutunci saboda baki daukeni uwarki ba ko?” Cikin tashin hankali take duban innar
“Inn….” Bata barta ta qarasa ba ta dora
“Ni yarki zata kalla ta cewa barauniya?” A birkice umma ta maida dubanta ga kaltume,batayi wata wata ba ta shimfide yatsunta guda biyar saman fuskarta
“Wallahi ummanmu bi ban fada ba,ga fatsima da kubra nan ki tamb…..” Tsawa ta daka mata ba tare data barta ta qarasa magana ba
“Tsugunna ki roqi gafararta,inna uwata ce da nake neman albarkarta” tabbas innar babu darajar wanda taci saita ummanta,ba zata taba iya musu da ita ba,don haka ta matsa kusa da ita ta bata haqurin,sai data maimaita sau uku sannan ta sauke kumburin da tayi tace ta haqura,tana direwa taja tukunyar naman gabanta ta budeta,sai umman ta juya da sauri tabar wajen ta nufi dakin innar,tana jin wani rauni da tausayi yana ratsata,tasan cewa tabbas akwai wani abu da ba haka yake ba,saidai bata isa ta tanka ba,a tsarin tarbiyyarta ma ba zata taba tankawar ba.

Kayan sawar innae ta fara fitowa dasu masu datti,wanda ta saba kusan sunnarta ce,duk lokacin data xo gaida innar koda bata da cikakkiyar lafiya saita hada kayanta ta wanke mata,duk da cewa ita din bata wanki sam sam,kaltum ta dauke nauyin wankin kayanta,data wanke kuma bilal xai hada wuta ya goge mata,duk da cewa ba wani yawa garesu ba,ba kuma wasu tsada bane,a nata ganin tunda bata mallaki abinda innar keso ba,bata kuma da abin bata,ko yaushe bata farinciki da ita,wannan wala’alla shine abu guda da zata dinga yi wanda zai faranta mata.

Tasha shan mita da qorafi a wajensu kaltum harma da bilal,bilal da kansa yace xai dinga zuwa a madadinta yana yiwa innar wankin harna da guga,amma tace sam,ai uwa batafi uwa ba,hakanan itama tana neman albarka,bugu da qari ba zata turasu suje su batawa uwarta rai a madadin wanki ba.

Duk da cewa ko sau daya bata taba yaba mata ba amma bata fasa ba,idan taso ma wani lokaci tayita bin zannuwan tana cewa basu fita ba idan ‘yan tsiyar a kusa suke,koda a gaban qannenta ne,idan basa kusa kuma ta tafas ba zata ce mata ba,har tayi ta gama,tayi mata sallama ta tafi,koda kuwa a gaban qannenta ne,a matsayinta na babba,wadda ita ta zamto diya ta farko a wajen innar,amma duk hakan bai taba sawa ta daina ba.

Laifinta guda daya ne saboda bata da abun duniya,laifinta guda daya bata da komai bata mallaki komai ba,laifinta shine tana auren miji talaka ba mai abun hannunsa ba,hakan bai taba damun ummanmu ba,ta sani ta kuma yi imani Allah shike zartar da komai,shike azurta bayinsa aduk sanda yaso hakan.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,ZASU FARA ZUWAR MUKU CIKIN YARDAR ALLAH DAYA GA WATAN JANUARY 2022,GARZAYA MAZA KI BIYA NAKI KUDIN,DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA DUKA LITATTAFAN,KO KUMA WASU DAHA CIKINSU,ZAKI IYA TURA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

*SAIKI TURA SHAIDAR BIYANKI GA WANNAN NUMBER*

08184017082

*KATIN WAYA TRANSFER KO VTU KUWA,ZAKI TURA TA NAN NE*

09134848107

 

*DABI’AR ZUCIYA*
*LAST FREE PAGES*
05

*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,zaki iya biyan naki kudin ta hanyar tuntubar wadan nan numbers din guda biyu*

08184017082
Ko
09134848107
______________________________

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected