VENNETE
DUBU JIKAR MAI CARBI Complete Hausa Novel

DUBU JIKAR MAI CARBI Complete Hausa Novel

Ɗauke kai ta yi don ma kar ta ci gaba da kallon wurin da Dubu take ta ci gaba da tsoratata, sai da ta kusa da wurin da Dubu take ta ji muryar marigayin mijinsu raɗau a kunnenta yana cewa, “Wato ita dai rayuwar barzahu daɗi gare ta. Babban daɗin idan ka kawo ziyara tsohuwar rayuwarka sai kuma ka tafi da matarka.” Inna Furai na jin haka ta dafe ƙirji tana ja da baya jikinta har tsuma yake ta ce, “Yau na haɗu da zazzagar rayuwa ni Furaira. Allah na roƙeka karka jarrabe ni ta wannan fannin.” Dubu na jin haka ta miƙe tsaye tana gyara zaman babbar rigar jikinta ta sake kausashe murya ta ce, “Wuni ɗaya har na yi abokai miliyan ɗaya da ɗari biyar a cikin Fatalen har da masu tashi sama. Ƴan sama jannati ku zo ga wani naman mun samu, kuma daga yau mun fara ɗauka kenan a gidan nan. Duk wanda ya wayi gari ya ga likkafani a jikin kayansa shi za mu yi wa ɗaukan amarya.” Inna Furai tuni fitsarin da take riƙewa ya samu sukunin tsiyayowa, sakin butar hannunta ta yi jikinta na tsuma donma bongon da ke bayanta ya tokareta.

Dariya ce ta so ƙwacewa Dubu amma ta maze ta ce, “Ƴan uwana ƴan sama Jannati! Ku zo na fara samo muku ƴar uwa.” Inna Furai ta saki salati tana cewa, “Yau na haɗu da zazzagar rayuwa shi kenan tawa ta zo ƙarshe.” Dubu sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta fara takowa gaban Inna Fuarai ta ce, “Idan kina son fansar kanki sai kin sake shayar da ƴaƴanki tamkar yanda kika shayar da su suna jarirai, tun daga kan Larai (Ita ce babbar Ƴar Inna Furai) har zuwa kan Sabi’u (Shi ne autanta) idan kika kuskurewa haka tabbaci haƙiƙa sai mun zo ido biyu mun tafi da ke babu wanda ya isa ya hana.”

Baba Sule tuni cikinsa ya ɗuri ruwa yana son fita domin ceton Matar Mahaifinsa tsoro ya cika masa ciki, bai gama tsinkewa da lamarin ba da ya ji an fara kiran yan sama jannati. Dubu don ta ƙara razana Inna Furai ta sake dakushe murya ta ce, “Ki isarwa da mutanen gidan nan saƙona muddin suka ci gaba da kwanaki sai na yi musu ɗauki ɗaiɗai. Shi kuma na ɗaki da yake laɓe yana sauraronmu, shi kuma ɗauke shi za mu yi gabaɗaya.” Dubu na cikin magana sai gani ta yi Inna Furai ta zube ƙasa. Gabanta ne ya faɗi ta ji fargabar kar tsohuwar mutane ta mutu a hannunta. Da sauri dubu ta waiga sai kuma ta kurma ihu tana maƙe murya ta zunduma ihu, sannan ta zuba a guje ta yi cikin gida. Ta nufi ma’ajiyar kayan Baffa ta lallaɓa ta shige ta kwanta.

Ihun da Dubu ta yi ba ƙaramin razana Baba Sule ya yi ba da jim kalaman da da aka ce za a ɗauke shi matuƙar ya saki hannun matarsa. Yana daga gefen gado da sauri ya matsa ya kama hannuwan matarsa ya riƙe ƙam, don kar a neme shi a rasa. Cikin bacci Sahura ta fara masifa da yake Allah ya yi ta masifaffiyar macece. Tana jin ya riƙo mata hannu ta ce, “Don Allah sakarni Uban ƴan naniƙa.” Da yake bacci ya hau kanta bata kuma tanka masa komai ba.

Daga ɗaki mai kallon gabas Baba Auwalu ne ya ɗaga labule yana haskowa da fitila zaraf matarsa Yahanasu ta miƙe tana tambayarsa da yake su sabbabun amare ne. Daga can nesa suka hango Inna a yashe tana ko numfashi bata yi. Gabansa ne ya faɗi yace, “Wa nake gani kamar Inna a ƙasa.” Sahura ta dafa kafaɗarsa ta ce, “Auwaluna ni ban yarda ita bace kawai magauta ne suka yi maka ture.”

Duk duniya babu abin da Auwalu ya tsana sama da a ɓata ran Yahanasu amma tabbas wannan karon ba zai iya haƙura ya bar Mahaifiyarsa a wannan yanayin ba. Kasancewar dare ne amma bai hana sakar mata murmushi ba ya ce, “Allah shi zai kare ni amma bana tunanin wani zai yi mini ture cikin dare.” Kafin ta yi magana tuni Auwalu ya yi gaba, ganin haka ya sa ta ja tinga ta tsaya don har ga Allah a tsorace take musamman da ya kasance ranar ne aka yi rasuwa.

Hankali a tashe ya fara yayyafawa Inna ruwa ganin ta fara motsi ya sa ya kamata yana bubbuga ƙofar Baba Sule, Baba Sule na ji ya yi fakare kamar mai bacci don gabaɗaya ya gama rikicewa. Sama-sama Sahura ta fara jin bugun ƙofa firgigit ta miƙe sai ji ta yi Sule ya riƙe hannunta gam, tana shirin yin magana Baba Sule ya janyota cikin raɗa ya fara cewa, “Kada ki yi magana za su yi sama da ke” Waigawa Sahura ta yi tana kallon ƙofa don ita a tunaninta masu buga ƙofar ne za su yi sama da ita. Suka ƙarajin bugun ƙofa Auwalu yana cewa, “Yaya Sule fito ka taimaka mini jikin Inna ya yi tsanani ina jin makewayi za ta ta faɗi.” Sahura ta ja guntun tsaki ta ce,

“To! Sai ka tashi tun da ta ka ji muryar Auwalu.” Baba sule ya sake ƙasa da murya yanda daga shi sai Sahura ne za su ji abin da yake faɗa ya ce, “Ki koma ki kwanta kawai ina ji a jikina waɗannan ƴan sama jannati ne suka rikiɗa. Takaici ya kama Sahura yanda ta ga Maigidanta yana rawar ɗari ga shi ba lokacin zafi ba, ta miƙe tana fusgar hannu ta ce, “Sakarni ko ƴan ƙasa jannati ne babu abin da zai hanani fita.”Tana jan hannu Baba sule yana ja don a tunaninsa muddin ta saki hannunsa shi kenan za su yi sama da shi.

Sororo Sahura ta yi tana kallon ikon Allah, don ita a iya saninta da Sule ba su taɓa irin wannan wasan da shi, don haka ta sake ɓata fusaka ta ce, “Sule wai wani abu ne yake damunka ko gamo ka yi cikin dare n sani ba?” Baba Sule ya yi wura-wura yana kallon hagu da dama ya sake ƙanƙance murya ya ce, “Sahura a kowanne lokaci za a iya yin sama da ni.” Wani takaicin ne ya sake rufe ta, ta miƙe tana ƙoƙarin fisge hanunta amma abin ya ci tura don ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya.

Auwalu da ke jin ƙusur-ƙusur a ɗaki sai ya sungumi Inna don a ganinsa bai kamata ya sake buga ƙofar ɗakin ma’aurata cikin dare ba. Can sashen su Inna Furai ya nufa Yahanasu ta ƙwalla masa kira tana cewa, “Auwaluna ina za ka ni dai tsoro nake ji.” Auwalu ya waigo ya ce, “Shiga ɗaki Inna zan kai na dawo.”

Dubu na daga ɗaki tana jin duk abin da yake faruwa, tana jin Baba Auwalu ya tafi ta yi zaraf ta fito cikin sanɗa sai da ta zo daga bakin ƙofar Yahanasu ta yi gyaran murya ta sake kausashe murya irin ta Marigayi mai carbi ta ce, “Wato ita rayuwar barzahu daɗi gare ta ni Mamman. Yanzu tun da na zagayo rayuwata ta baya dole na ɗauki mai ɗakin nan.” Cikin Yahanasu ne ya kaɗa nan take jikinta ya hau karkarawa kamar mazari. Dubu ta yi irin tarin tsofaffin ta sake cewa, “Amma ita Yahanasu za mu ɗaga mata ƙafa sai dole ta bi sharaɗinmu ko ba haka ba ƴan sama jannati?” Dubu ta sake sauya murya ta ce, “Ai dole ma ta bi umarninmu ko yanzu mu faɗa ɗakin.” Yahanasu bata san lokacin da ta yi farat ta ce, “Wallahi ku faɗa ko meye zan bi.”

Dubu ta maƙale murya ta ce, “Dole ki zama makauniyar ƙarfi da ya ji muddin kika buɗe idonki sai dai ki wayi gari a ƙiyama.” Tun Dubu bata rufe baki ba Yahanasu ta runtse ido biyu ta ce, “Wallahi na rufe har abada ba zan sake buɗe su ba amma don Allah karku cutar da ni.”

Dubu har da ƴar tsawarta ta ce, “Kin tabbata kin rufe ko na aiko da Ƴan sama jannati su shigo?” Yahanasu ta sake runtse idonta tana cewa, “Na rufe wallahi na rufe.” Dubu ta saki murmushin mugunta a ƙasan zuciyarta tana cewa, “Yau zan ga ƙaryar soyayya kullin a ishe mu da Auwaluna.” A fili Dubu ta ce mata, “Maza tashi tsaye ki rungume bango.” Da sauri Yahanasu ta fara lalaube-lalube har ta taɓo bango.

A hankali Dubu ta zura kai ta leƙa ta hango Yahanasu na rungumar bango, zuruf ta faɗa ɗakin cikin sanɗa. Sai da ta je daidai wurin Yahanasu sannan ta ɗaga zabgegen Carbin Marigayi ta zabgawa Yahanasu a ƙeya, sai ta fara wani gunji tana cewa, “Gargaɗin yan sama jannati kenan.” Tana faɗar haka har ta fice daga cikin ɗakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected