VENNETE
DUBU JIKAR MAI CARBI Complete Hausa Novel

DUBU JIKAR MAI CARBI Complete Hausa Novel

Yahanasu tun da ta gantsare take hawaye a tsaye sai dai ta kasa buɗe idonta saboda tsoron abin da kaje ya zo.

Duk abin da yake faruwa a kunnen Sahura da Baba Sule, cikin Baba sule ne ya sake ɗurar ruwa. Sahura ita kanta jikinta ya fara sanyi musamman da ta jiyo Ihun Yahanasu, shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta duk masifar da take yi ta daina. Domin da alama zancen Sule ya tabbata.

Lokacin da Auwalu ya ƙarasa ɗakin Inna Furai, har lokacin bata dawo hayyacinta ba. Yana shiga ya kwantar da ita akan ƙaramin gado, sannan ya fara tashin ƙanwar Mahaifinsu Lantan da ta zo daga garin Zariya. Ganin halin da Inna Furai take ciki ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen ɗakin ya yi ba. Auwalu ya juya zai fita Inna Furai ta riƙo hannunsa ta ce, “Auwalu! Yau na haɗu da zazzagar rayuwa. Don haka ka haɗo mini kawunan ƴan uwanka mazan su da matan su a yanzun nan. Idan ba haka ba wallahi sai na zazzagar da albarkasu kowa ya lalace.”

Auwalu da sauran mutanen ɗakin sun yi tsammanin zafin ciwo ne ya sa Inna Furai take sumbatu. Lantan ta ƙara matsawa kusa da Inna Furai ta ce, “Furaira sanu kin ji Allah sa dai ba akan makarai kika faɗi ba.” Wannan magana ba ƙaramin fusata Inna Furai ta yi ba, a zafafe ta ɗago ta ce, “A kan bulikiya na faɗi! Lantan bana son zazzagar wulaƙanci. Kai Auwalu ka tara mini ƴan uwanka a daren wallahi tun ban zazzage albarkar da ke kanka ba.” Kamar sabon munafiki haka Auwalu ya fice sum sum sum daga ɗakin. Haka ya rinƙa bi ɗaya bayan ɗaya yana taso su. Wannan tashin da Auwalu yake yi wa ƴan uwansa ne ya sa kusan rabin mutanen gidan suka tashi daɗin daɗawa idan kowa ya ji ance Inna Furai ta faɗi a hanyar banɗaki sai ya wartsake masu tafiya ɗakinta na yi masu jaje suma suna yi.

Kafin wani lokaci tuni ɗakin Inna Furai ya cika da ƴaƴanta su rai takwas maza biyar mata uku. Sai da ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sai kawai suka ga ta ɗaga riga ta ce, “Larai bisimillah” Larai zuciyar ta ɗaya ta ɗauka Inna Furai so take a ƙarasa cire mata riga, nan take ta fara cikiniyar tuɓe mata riga. Cikin ƙaraji Inna Furai ta fisge tana cewa, “Larai yanzu bijirewa umarnina za ki yi? Ni za ki zazzagewa albarka a ka” Sai ji suka yi Inna Furai ta fashe da matsanancin kuka. Lokaci ɗaya suka kalli juna domin ba su ga abin da zai sa Inna Furai kuka ba. Auwalu ya sunkuyo ya ce, “Inna ki yi hakuri me kike so?”

Inna Furai ta ɗago mamanta ɗaya ta ce, “Mahaifinku ya zazzage mini albarka ɗazu nan domin daga zuwansa lahira har ya haɗa kai da ƴan sama jannati. Ba zan zazzage maka bayani gabaɗaya ba amma Auwalu ungo sha ka ji.”
[7/1, 6:02 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 2

Auwalu sam bai fahimci inda maganar Inna Furai ta dosa ba, don tun da ya ji ta ambaci Mahaifinsu ya tabbatar da zafin ciwo ne yake damunta da kiɗimewar rashin da aka yi musu. Saboda gudun faɗanta ya sa ya wayance da cewa, “Inna ban fahimci abin da kike faɗa ba. Amma kuma duk wanda ya mutu kin san sai dai mu bishi da addu’a ita ce mafita.” Inna ta yi ƙuri tana kallonsa sai zuwan can kawai ta fashe da kuka. Lantan da ke gefe takaici da baƙin ciki gabaɗaya suka turniƙe ta, don gani take kamar har da biyu Inna Furai take lanjarewa. Kasa haƙuri ta yi ta ce: “Furaira don Allah ki shafa mana lafiya ki bar mu, mu ji da abin da yake damunmu. Haka kawai ki tayar mana da balli a tsakiyar dare akanki aka fara mutuwar miji? Ko kuma ke kaɗai kika san zafin miji muna zaune ki ishe mu da zancen fatalwa. Ki barni na kwanta na yi baccin da ban samu na yi shi jiya ba.”

Inna Furai ta fyace majina da gefen zaninta ta waiga ta ce, “Wallahi babu ƙatuwar Matar da za ta zo mini ɗaki ta nemi kawo mini zazzagar albarka ido biyu. Idan ba za ki iya ba ki tashi ki fice dama ni bana gayyar tsintsinya da bulugari, bare kuma mafici abin banza.” Lantan jin maganar Inna Furai ta yi kamar ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta zaburo a hasaale ta ce, “Ban da ƙaddara da rashin ɗan’uwana da na yi, me zai kawo ni ɗakinki kaico Allah ya jiƙanka Yaya Mamman. Wai yau jininka ake wulaƙantawa saboda ƙasa ta rufe mata ido, kai jama’a ɗan’adam butulu. Wanne irin karamci ne Ɗan’uwana bai yi miki ba?”

Inna Furai ta jingina da ƙarfen gado sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, tana yi tana fatar majina. Abin duniya goma da ashirin ne damu su Auwalu, don haka kowa ya yi jim! Babu wanda ya iya tofa magana ɗaya sai gani suka yi Inna Furai ta fara haɗa ƴan kayayyakinta na sawa da ke kan gado. Sabi’u ya ce: “Inna lafiya kuwa wai me yake faruwa ne kike haɗa kaya?”

Inna Furai ta juyo a fusace ta ce, “Zaman ku a nan bai amfane ni da komai ba. Kuna gani ta gama zazzage mini rashin mutumci a ka babu wanda ya tanka mata. Wallahi ko ku bi mini haƙƙin zazzagar albarkar da ta yi mini a ka ko kuma yanzu na fice na baku wuri ku yi yanda kuke so. Gara ni tawagar Malam da ƴan sama jannati ta zo ta ɗauke ni ko kowa ya huta, dama na kiraku ne domin mu kashe mu binne amma da alama ku dai ba ƴan goyo ba ne, don na lura za ku iya zazzage mini sauran albarka da ta rage mini a kaina.

Gabaɗaya shiru suka yi suna nazarin abin da yake damun Mahaifiyarsu, don rikici sun san Mahaifiyarsu mace ce mai matuƙar rikici amma wannan karon gani suke har da mutuwar mahaifinsu da ta taɓa ta.

Lantan na gama sauraron Inna Furai ta miƙe tsaye tana shartar ƙwalla, ɗan ƙullin kayanta da ke ƙarƙarashin gado ta janyo ta fara kiciniyar ɗorawa a ka tana matsalar hawaye. Da sauri Auwalu ya miƙe ya riƙe kayan yana cewa, “Inna Lantana don Allah ina za ki a tsohon daren nan?” Lantan ta kunto mayafinta ta yafa a kanta ta ce, “Auwalu don Allah karka kawo mini maganar da za ta tunzurani har ta kai ga na nemi shaƙe wannan tsohuwar har lahira. Duk irin cin mutumcin da ta yi mini a gabanku baku gani ba za ka taso tsalo-tsalo kana tambayata ka bar ni yau ko ƙasa da sama za ta haɗe ba zan kwana a gidan nan ba.”

Nan fa hayaniya ta fara ta shi a cikin gidan, Inna Furai na gama saurarar maganar Lantan ta sa hannu bibbiyu ta dafe ƙirji a razane tana zare idanu kamar wacce ta yi tozali da kumurcin maciji. Bata tanka musu komai ba sai gani suka yi ta sauko ƙasa daidai wurin da Lantan take tsaye ta fashe da kuka haɗe ta rungumo ƙafafuwan Lantan tsam a jikinta. Tana cikin kuka ta ɗaga kai ta dubi Lantan tana cewa, “Wallahi ba za ki bar ɗaƙin nan ba sai kin zazzage ragowar numfashin da nake shaƙa, Lantan yau ni kike muradin kashewa a gaban ƴaƴana. Ai kuwa ko ba yanzu na mutu ba na rataya a wuyanki Kai Auwalu ku shaida haka.”

Inna Furai ta juya ga su Auwalu tana musu mugun kallo ta ce, “Allah na tuba wacce uwar na haɗa da su bayan alaƙar haihuwa? Da su Auwalu da Sabi’u kuma ni kam gara ma a ce ban da kowa tun da babu mai tare mini faɗa a gidan nan. Har ana niyyar halakani da sauran rayuwa kai jama’a Lantan an ya kina tsoron Allah kuwa? Duk wanda ya kashe wani dai wuta za shi.”

Lantan ta yi tsalle can gefe abin ka da da marar jiki, can gefen babban gado ta matsa tana cewa, “Laƙadi ja’akum… Tuf! Aniyarki ta faɗa kanki karki ja mini masifa ki maƙala mini sharrin kisan kai ina zaune ƙalau.” A wannan karon Inna Furai bata tanka mata ba sai gani suka yi zaraf ta fice daga ɗakin, da sauri iyalanta suka bi bayanta suna roƙon ta dawo ɗaki saboda dare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected