Hausa NovelsZafin Kai Hausa Novel

Zafin Kai 90

Harta zuba a bakinta taji Bazata iyaba tayi saurin fito dashi tana gobe bakinta ta mayar dashi leda ta jefar tsakiyar dakin tana shiga Sabon tashin hankalin Neman mafita Dan haka gwara dai ta gudu inda zata tsira da rayuwarta.

Gurin drawer na aje kudinsu ta nufa ta Bude jikinta na wata irin rawa tahau diban kudi ta cika qatuwar handbag dinta babba ta dauki passport dinta ta saka tareda sauran id cards nata.

Tana fitowa Safnah dake dakin itama nata idanuwan kaman na Panda duk sun fito sunyi baki sbd tashin hankali da rashin rintsawa ta fito sukai Karo a palon.

Kallan juna sukai ta kalli momyn a tsanake itama momyn ita ta kalla tana boye tashin hankalinta ta kalleta tana Dan bayyanarda kulawa tace

“Bari naje na dawo yanzun Nan nayi Miki bayanin Wani abin mamakin kiji.”

Gaba tayi tana Hana yanayinta bayyana.

Harta fice Safnah batace mata komaiba sai jakar hannunta data hango kudi masu tarin yawa aciki musamman daloli.

Mamaki ne ya kamata Dan haka ta Bude dakin momyn ta shiga ta nufi inda suke ajiye kudi taga babu komai se yan canja,

Passport din momyn ta duba Bata gansa ba nata kawai ta Gani Dan haka ta sake shiga matsanancin mamaki da tashin hankali.

Juyawa tayi zata fice ta hango ledan robar qwayoyin dasukai amfani dasu tsakiyar dakin take ta fahimci akwai babban Abinda yake faruwa.

Fitowa tayi da sauri daga Palo ta nufi harabar gidan har momyn ta kusa ficewa da kota ta tsayar da ita ta qarasa gurinta tayi qasa da glass Safnah tace

“Momy nesa ne zakije??

Cikin girgiza Kai tace “aa yanzu fa zan dawo,Dana dawo zakiji komai fa.”

Jan motar tayi ta wuce Safnah ta bita da Kallo tana goge hannunta daga ledan qwayoyin data sakawa momyn bayan motarta batareda ta saniba.

Momyn na ficewa itama motarta ta dauka ta fito da sauri tabi bayan momyn.

Sun ficewa motacin jamiaan tsaro gudu uku suka iso gidan maigadi ne ya nuna musu motocin su Safnah dasuka fice yanzu Dan haka take suka bi bayansu Suma.

Hanyar barin gari momyn ta kaman tana kallan madubinta ta lura da motar Safnah dake binta Abaya.

Wani mummunan faduwan gaba da zufa ne ya keto mata sbd Safnah taci gaba da binta akwai babbar matsala zaa iya kamasu duka tare Dan haka suna sake ficewa daga mutane ta tsayar da motarta tana kallan motan Safnah datai parking bayanta.

Fitowa mota Safnah tayi cikin tsananin baqin ciki da takaici tareda tafasan zuciya sbd har lokacin ta kasa Gane me momyn ke Shirin aikatawa.

Tana tahowa momy sai dataga ta fito motar ta nufota kafin tayi gaba kadan da motarta tayo reverse cikin Wani mummunan gudu ta taka Safnah din da motarta Bata tsayaba ta buga da mugun speed tayi gaba tana Hawa titi sosai da gudu.

Cikin mummunan yanayi na karywar qafarta Daya da fita fit a take jamian tsaron suka iso kan Safnah wadda ke cikin halin Rai ko mutuwa Dan hatta fuskar kusan tayi dameji suka kwasheta sauran motacin kuwa suka bi bayan momy.

Asibitin da aka Kai Ababa Wanda tini Shima gurin cire bullet an qarasa lalata qafar acan aka kaita itama da qafarta Daya Bata hayyacinta sbd fuskarta datai damage.

Momy gudu takeyi sosai tana qarawa hankalinta na tashi tana waya da qaninta dazai Siya mata ticket a Daren ta wuce Lagos daganan zata Bema visa tabar qasar gaba Daya.

Checking point na sojoji ne suka tsayar da ita ganin yanda take gudu sosai tana mace.

Jakar kudin dake qarqashin qafafunta suka fara gani take suka buqaci tayi parking.

Parking tayi tana Dan kame kame tana murmushin karfin hali kafin tafara magana saiga ledan qwayoyin abayan motarta.

Koda jamian dasuka biyo motarta suka iso gabaki Daya kamanninta sun sauya daga hannun sojojin Dan haka take case dinta ya girmama aka fara daukanta hotina mutane ana korarsu sbd harda bindiga a Jakarta.

Kamata Akai babu tausayin halinda take ciki da mummunan dukan datasha da kan bindiga a hannun sojojin aka saka mota ko tafiya Basu fara ba itama ta sume kaman matacciya hancinta da bakinta suna jini hakama idonta Daya ya tsiyaye.

Same Asibitin itama aka kaita inda su Ababa da Safnah suke babu Wanda yasan inda Kansa yake haka itama aka Bata gadon batasan inda kanta yakeba jininta na tsiyayewa.
saisun farka su samu Daman karban hukuncinsu.
##MAMUH#

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected