interstitial
Ajiya A Duhu BOOK 1 Na Billyn Abdul

Ajiya a Duhu Na Billyn Abdul Page 94

????9??4??

______________

 

……….“Nifa wannan yanayin na Ajwaad ya fara bani tsoro babban Yaya. Anya babu abinda ke damun yaron nan? Ko wanda bai san ala?ar baya data shu?e tsakaninsa da Maanal ba ya kalli idanunsa yasan akwai soyayyar ta a ciki, amma batun aure ya?i ya amsa. Wannan abu na birkita min tunani”.
Nannauyan huci Babban yaya ya furzar, idanunsa akan Fawzan ya ce, “Bakai ka?ai ba, ni kaina a wannan ga?ar zuciyata ta fara shiga nazari. Fawzan mu dukanmu mun san soyayyar Maanal ce ta hana Ajwaad aure, ka duba kaga jiyyar da yayi, yasha wahala matu?a, amma ace yanzu haka na faruwa? Wlhy nayi zaton duk randa Ajwaad ya ha?u da Maanal sai yasa an ?aura musu aure a washe gari koda tsiya-tsiya”.
“Kowama irin wannan hasashen yake yi Babban Yaya. Amma kaga yanda abubuwa ke tafiya.”
“Yanzu yana ina?”.
“Ai sashensa ya nufa”.
“Inaga muje mu sameshi”.

Ajiyar zuciya mai ?arfi Abah dake bayansu batare da sun sani ba ya sauke. Yayinda zuciyarsa ke faman kai-kawo. Tabbas shima a yau irin tunaninsu yake yi, dan al’amarin Ajwaad ?in ya fara bashi tsoro, yaro kamar mai aljanu. Yayi zaton a wannan zaman da sukayi yanzu zai amsa abinda suke bu?ata ne koda jin abinda ke shirin faruwa. Shin mike faruwa ne? Mike damun yaronsa?. Da wannan tunanin ya juya ya koma sashen Oum.
A hankali Saheeba ta fito daga ma?oyarta itama. Ta ri?e ?ugunta da duka hannayenta biyu tana hararar sashen Oum, sai kuma kamar wadda aka tsikara zaram ta zabura hanyar sashen AA. Dan ya kamata tasan mi su baban Yaya zasu tattauna da shi anan ?in ma….

______?

A bazata sallamar su Babban Yaya ta shiga kunnen AA dake bedroom ?insa. Sai da ya ?an rumtse idanu kafin ya mi?e cike da ?arfin hali daga kwancen da yake a cikin sofa dake a bedroom ?in. Tissue ?in daya zubar a saman lallausan carpet ?in gaban kujerar fari tas yasa hannu ya tattare. Toilet ya nufa da su ya zuba a dusbin ?in can, dan baya bu?atar kowa ya gani daga abinda ke jikinsu. Bayan ya wanke hannunsa da fuskarsa ya fito daga bayin, ruwa ya ?auka yasha sannan ya daidaita yanayinsa ya fita. A bakin ?ofa suke tsaye har yanzu, sai kawai ya basu hanya suka shiga. Saman sofa ?in ya koma ya zauna, su kuma suka zauna a bakin gadonsa duk idanunsu a kansa.
Fuska ya ?an yamutsa, tare da shagwa?e ta cike da son danne komai ya ce, “Wai lafiya kuke kallona?”.
Babu wasa sam a fuskar Fawzan ya ce, “Ajwaad mike damunka ne?”.
“Kamar ya? Yaya Fawzan”.
Harararsa Fawzan ?in yayi, kafin Babban Yaya ya amshe da fa?in, “Ajwaad ka tsaya da pretending ?in nan naka haka nan. Munzo nan ne domin tambayarka. Kuma gaskiya muke bu?atar ji. Shin akwai wani ne dake maka barazana akan lamarinka da Maanal shiyyasa ka kasa amsar aurenta duk da soyayyar da kake mata”.
Wani irin girgiza zuciyar AA tayi, amma da yake namijin duniya ne sai ya danne. Idanunsa a cikin na Babban Yaya ya ce, “Barazana kuma Babban yaya? Ni kuma wani zaima barazana kamar ?aramin yaro. Kawai dai ku kun kasa fahimtata ne tun farko. Yarinyar nan ina mata kallo ne tamkar ?aya daga cikinmu. Ina mata soyayya ne irin ta ?ar uwa ?anwa ciki ?aya, shin miyasa ku kuke fassara hakan da wani abu daban…..”
“?arya kake Ajwaad, wlhy son Maanal kake soyayya irin ta aure, soyayya irin wadda baka ta?a yima wata ba a duniyar nan idan aka cire iyayenmu. Soyayya kake mata irin wadda zaka iya rasa rayuwarka ma idan babu ita a ciki. Kalleka Ajwaad, kalla yanda ka zabge a kwanakin nan.  Sannan a kwankin baya na bayyanar Maanal sosai hankalinka ya kwanta, farin cikinka ya dawo. Idan kuma ba haka bane ka rantse baka sonta, mu kuma mun maka al?awarin barin ka, ko kuma ka fidda matar aure mana!!”.
Cikin matu?ar pretending AA ya mi?e yanama Fawzan da yay maganar fusataccen kallo. “An?i a rantse ?in, shin Yaya Fawzan kai ubana ne da dole saika titsiyeni na amshi abinda kake so, kai kaje ka aurenta mana ko an hanaka ne. Nifa bana son takura!!”.
A fusace shima Fawzan ?in ya mi?e, yaje gaban AA ya tsaya yana kallonsa cikin ido. A matu?ar kausashe ya ce, “Hummm Ajwaad kenan, ka godema ALLAH zuciyata a matsayin ?anwa kuma masoyayyar ?anina take kallon Maanal, amma wlhy da sai na baka mamaki a wannan ga?ar, da sai naje na auri yarinyar nan naga yanda zakai. Kuma ko a yanzu, da ace wani abu bai ta?a shiga tsakanin kai da ita ba na ?addara wlhy da sai na aureta ?in, sakarai kawai mai mugun hali”.
Ya hanka?esa ya wuce fuuu. Wani irin masifar rawa jikin AA yake yi, gaba ?aya fuskarsa ta gama birkicewa. Cikin ?acin rai ya kalla Babban Yaya da kamar al’ajabi ya sashi suma shi kam. Fawzan mutum ne mai matu?ar ha?uri, nuna fushinsa akan Ajwaad yau ?in nan ya girgiza babban Yaya. Sannan abubuwan Ajwaad ?in sun sake birkita masa tunani. Kamar AA ?in zaiyi magana sai kuma ya fasa. Fuuu ya zagaye Babban yaya ya wuce bathroom ?insa. Yanda ya wani bugo ?ofar da masifar ?arfi ya dawo da babban Yaya hayyacinsa. Ya jima yana kallon ?ofar bayin kafin ya fita jiki a sanyaye, dan shifa zuwa yanzu ya fara wani kuma tunani daban….

AA kam yana bugo ?ofar a jikinta ya manne, ya wani kalar runtse idanunsa da suka gama juyewa. A saman lips ya furta, “Kayi ha?uri Yaya Fawzan kayi ha?uri kaji”. Zuuu wani damshi ya gangaro daga hancinsa, yasan minene, dan haka bai damu da bu?e ido ya kalla ba, haka abin ya cigaba da zirara masa akan gashin gemunsa har zuwa ?irjinsa sai da yaji jiri na neman kada shi a wajen kafin yaja ?afa da ?yar zuwa ?ar?ashin shower ya sakar ma kansa ruwa. Ya jima a haka kafin ya fito da ?yar, a haka jikinsa na zubar ruwa da sumar kansa ya fa?a saman gado yaja bargo ya ?udundune. Dan wani irin sanyi yake ji da zazza?i da ciwon kai.

?Tuni Saheeba ta kaima Mamy rahotan abinda ke faruwa tsakanin Fawzan da AA. Dan haka hankalinta ya ?an so tashi, Fawzan nada ha?uri sosai a cikin yaran, amma idan yay fushi koya ?wafama abu sai fa yasan asalinsa da tushensa. Bata bu?atar kowa ya fahimci wacece ita a tsakanin shi da Fadeel a yanzu sai anyi auren Ajwaad, dan aga?ar take son fara shirinta na dawowarsu hannunta. Dan haka ta mi?e, bedroom ta nufa ta ?auka waya tai kiran layin AA, sai da tana gab da tsinkewa ya ?aga, duk da yanda taji muryarsa ya motsa zuciyarta amma sai ta dake. Maganganu masu zafin gaske da dogon garga?i taja masa akan ?an uwan nasa guda biyu, batare da jiran cewarsa ba ta yanke wayar.
A karo na farko al’amarin Mamy ya saka AA sakin murmushi mai ciwo. Kowa da tashi jarabawar a rayuwa, su kuma mahaifiyarsu ce tasu jarabawar. ALLAH ya basu ikon cinyewa. Musamman ma shi da ya da?e da sanin wacece ita a duniyarsu. Bawan ALLAH haka yasha fama cikin zazza?i har dare, koda Oum ta kira shi a waya sai yace mata barci yake. Data bukaci yazo yaci abinci yace a kawo masa kawai sashensa zai ?an yi wani aiki ne. Bata kawo komai a ranta ba duk da itama dai halin da take ciki na tunani da neman mafita akan al’amarinsa da Maanal yasa bata so yazo ya ganta a yanda take. Gefe ga garga?in Abah na tada mata hankali. Amma babu yanda zatayi…

*_JUMA’A_*

Ranar juma’a jirgin ?arfe goma suka bi zuwa Kano. Kowa ka gani a cikinsu sam babu walwala a tare da shi. Sai ma AA ?in ne ke ?an nuna dakiya. Sai dai a kallo guda zaka fahimci yanda yay wata irin zabgewa ta rama a tsaye. Sai manyan idanunsa da suka sake fitowa fatarsa ta sake haske ga gashin fuskarsa ya fara taruwa fiye da yanda yake barinsa dan ya?i yay gyaran fuska. Shi ka?ai yasan irin dogon garga?in da yasha akan Mamy a safiyar yau da daren jiya. Shi yanzu al’amarin mahaifiyar tasu yama daina bashi mamaki ko tsoro. Abinda kawai bata sani ba ko bata cigaba da takurashi da garga?in ba a shirye yake ya mata biyayya koda kuwa hakan ne zai zama ?arshen rayuwarsa. Dan shi ya sani a wannan ga?ar babu kuma abinda ya rage masa a wannan rayuwar sai jiran mutuwar.
A gefe kuma Oum sai dama-dama take da shi. Tun daga jiya zuwa yau sai faman lallashinsa da lalla?ashi take akan batunsa da Maanal ya sanar mata ko akwai wani abu da basu san da shi ba ne. Baya son tada mata da hankali, dan haka murmushi kawai yake mata yace ta kwantar da hankalinta ALLAH na tare da kowa. Duk da bata fahimci abinda yake nufi ba ita dai lalla?ashi take yi akan in sunzo koda an tambayesa ya fa?i yana da wadda yake so. Dan ita bata ?auki wani batun kai ku?in Rafeeq gidan su Maanal ?in da muhimmancin da zai hana komai ba. Kawai garga?in Abah ne ma ya hanata kiran Rafeeq ?in ta masa tas, dan yaja mata dogon garga?i akan hakan. Shi kuma Rafeeq ?in kamar yasan abinda ta shirya masa ya?i komawa Abujan. Ko waya ya?i kiranta ma.
Mahmud da Hassan ne sukaje ?aukarsu a airport. Koda suka iso gidan Baba Sardauna sun samesa cike da dukkan ahalinsu. Dan kamar ma su ka?aine basu kai ga isowar ba sai Gwaggo Khadi data taho daga Yola. Dan sai da sukai kamar awa ?aya ma sannan itama ta iso da tata tawagar. Itama dai bayan Mahmud data mallakama Baba Sardauna a wancan lokacin tana da yara biyar a yanzu. Uku maza, biyu mata. Mazan biyu sunyi aure. Hamza da Lami?o. Sai Nuwaira da Raihana. Sune ?ammata da take damuwa da rashin yin aurensu. Sai autanta Abdullahi, shi kam da sauransa. Koda yake koshi ?in yanzu akama auren zama zai yi da matar sumul.
Tuni an kacame da hirar zuminci a ?aton falon gidan Baba Sardauna da dama an tanadesa domin irin wannan ha?uwar. ?a?a da iyaye anata zabga hira cike da farin ciki. Akwai irin AA marasa yawan magana a cikinsu, amma idan akai irin wannan ha?uwar kakanji bakin kowa ya bu?e. Hatta shi AA ?in yakan ?an saki jiki ka?an. Sai dai yau tunda aka gama gaisawa yama zame jikinsa yabar falon. Sai da Oum ta farga baya nan ta fara jajensa. Sai Modibbo ke sanar mata ai yana waje yana waya, jin haka yasa ta cigaba da hirarta, duk da rabin hankalinta na kansa, wani kuma tsagi nakan rashin ganin Rafeeq. Wasa-wasa AA bai dawo falon ba sai da za’a fara meeting. A lokacin ne kuma Rafeeq shima ya iso tare da Abbu, dama shima bai kai ga isowaba. Alhaji ?arami da Mah-mah ne kawai sai Rufaidah. Bayan addu’a ga wanda suka rasa da kuma su da suke raye aka fara abinda ya tara kowa. Nasiha ce mai ratsa jiki Baba Sardauna ya fara sannan ya tafi kai tsaye kan abinda yasa su tara wanan taro na gaggawa. Ba komai bane face auren da suke son ?ullawa. Maganar Rafeeq itace farko, Baba yay bayanin sun riga sun kai ku?i kuma an amsa nan da sati uku biki, dan haka zasu ha?e da sauran suma ayi a huta kawai. Amma an bama AA da Najeeb da su Nuwaira dama idan suna da wanda suke so su fa?a. Da Najeeb aka fara kasancewar uba a wajen su AA ?in. Kansa a ?asa yace shi baida wacce yake so, amma su ?ara bashi lokaci zai kawo. Baba Sardauna yace Sam bashi yiwuwa, babu wata dama da zasu ?ara basu, ya za?a a cikin ?a?an dangi gasu nan. Rasa abin cewa Najeeb da ransa ya gama ?aci yayi, sai kawai yace shike nan ya basu dama kowacce suka za?a masa. Albarka aka shiga saka masa. Kafin aka koma kan AA. Sarai yana kallon irin kallon da Oum ke masa, hakama Mamy, hakama Yaya Fawzan da Babban Yaya. Abah ne kawai baya hangowa da ?yau. Amma duk sai ya ture komai cike da dakiya yace shima ya basu dama duk wadda sukaga ta dace su bashi. Da ?arfi Oum ta runtse idannunta, yayinda Fawzan kema AA wani irin kallon takaici da jin haushi. Mamy kuwa murmushi ta saki tare da sauke ajiyar zuciya a cikinta. Dan tasan dai za?inta data ba su Baba Sardauna zasu bashi. An koma kan su Nuwaira sukace suma sun bada za?i.
Sai dai me, bayan an sakama AA albarka shima bu?ar bakin Baba Sardauna sai cewa yay, “To Alhamdullahi, munyi farin ciki da wannan biyya taku. Dan haka bama sai anje da nisa ba. Mun yanke shawarar ha?a auren ku ku hu?un lokaci guda, zakuma muyi amfani da ranar Rafeeq da aka tsaida dan ayi a wuce wajen. Tunda ku dukanku ba muhallin zama kuka rasa ba. Babu kuma wanda bai da abinyin da idan yau akace za’ayi nasan zaku shiga ku fito. Balle ma bama bu?atar komai daga kowanneku, ku shirya tarbar matayenku kawai. Magana ta ?arshe akwai zaman da mukai shekaru uku da suka wuce a wannan falon game da Ajwaad na auren yarinya da aka bashi wadda ta fito daga ke ?angarenki Kamila”. Da sauri Mamy ta kalla baba Sardauna ranta fal farin ciki amma tana ?oyewa. Cigaba yay da fa?in, “To ban manta ba, dan haka zamu tuntu?i iyayen nata in sha ALLAHU. Sai yarinya daga Kaduna da ?anin mahaifinyarta da kansa ya kirani itama yazo da batunta akan tarayyar su da Ajwaad ?in dai suka kuma bamu damar zuwa tsaida magana itama in har ya shirya zamuje ayi magana tunda shi da alama da mata biyu zai fara, ya nuna mana duk ya fimu gwarzantaka har mu dake iyayen naku”. Yanda yay maganar da ?ar raha ya saka wasu yin dariya. Yayinda mamaki ya gama lullu?e wasu, Ajwaad ne wai da auren mata biyu lokaci ?aya, duk wannan jin kan nashi tab ?in. Oum kam suman zaune tayi, burinta su ha?a ido da AA amma ya?i yarda. Haka Abah da su Babban Yaya ma. Ran Mamy kam fes. Haka dai akai addu’a taro ya tashi………??

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected