KALBIM BOOK 1 PAGE 40
Sayd na fita kai tsaye ya katse wayar dayake ya nufi office dinsa yana saka kiran Latif wanda ya dauka take.
“Oga Sayd I’ve Send you every information daka buqata,
Cikakken Sunansa Dr Ismail Saraki,
Yana Nigeria haryanzu sedai yana jinya haka kawai aka wayi gari ya samu stroke baya iya magana baya iya komai yana gida yana jinya tareda familynsa a Jos,
Likitan zuciya ne shima kuma bai taba aiki a kowane asibiti ba Nigeria sai zaaden sbd baa Nigeria din yake aikiba saida Zaadens suka basa babban matsayi a asibitinsu ya dawo Nigeria,
Address da duka sauran bayanin na turo maka komai”
Katsesa Sayd yayi da cewa
“Idan yana aiki a Zaadens a babban matsayi meyasa basu tsaya masa gurin neman lafiyarsa ba ya koma gida??
“Ba shine abin tambayarba Abin mamakin shine Duk wani hanyoyin samunsa sun datse hakama komai ya rasa a qanqanin lokaci wanda kaman ana kokarin hanasa wani abun ne kokuma akwai abinda yayiwa Zaadens din nake ganin”
Ajiyar zuciya Sayd ya sauke yana cewa
“Ngd Latif zan sake nemanka sbd Zuwa jos zai kamaka”
“Ok Thank you Oga Sayd”
Yana kashe wayar ya miqe yana sauke ajiyar zuciya akai akai sbd komai ya fara fito masa sedai tsoron qarasa bincikawan yake ma dan abinda zai binciko kada ya kashe AZIZ.
Sai yamma suka dawo gida suna isowa AZIZ kai tsaye bangarensa ya nufa yai wanka ya shiryo ya fito suka zauna cin abinci a dining falaq nata masa labarai kala kala wadda a duniya ita kadaice take ajiyesa tayita basa labarai da surutai kala kala ya bata kunnuwansa yana saurara batareda yace komaiba.
Suna gamawa suka wuce sallah
Saida sukai ishai suka dawo,
Motarsu na shigowa harabar gidan motar Fahad na shigowa bayansu dan haka a tare sukai parking.
Fahad dinne ya rigasu fitowa sanye cikin three quarter da farar sweatshirt ya nufo motarsu ya budewa AZIZ motar yana masa barka da dawowa.
Amsawa yayi yana kallansa a taqaice ya nufu hanyar studyroom dinsa suka nufi bayansa.
Yana shiga zaunawa yayi tareda ajiye wayarsa gefensa ya dago a natse ya kalli Sayd wanda yake kallan Fahad kafin ya maida kallansa kan Fahad din ya bude bakinsa yace
“Yes,the dets???
Kallansa Sayd yayi da sauri yana matsowa zaiyi magana AZIZ din ya dago manyan fararen idanuwansa yai masa kallo daya take ta dakata yana komawa baya ya saukar da kansa zuciyarsa na tsananin nauyi da tashin hankalin abinda fahad ya samo akan binciken.
Fahad da shima yake a natse sbd a gaban AZIZ din suke ipad dinsa ya daga ya fara budo bayanan yana cewa
“Babu Alaqar kowane business dake tsakanin Zaadens da dr Abraham saina likitanci wanda kaman yanda muka zarga akwai me ciwon Zuciya a familyn sunanta ZEYNAB ZAD sedai kuma ta rasu da dadewa,
Bayan rasuwarta Zadeens sun sake samun mace a familyn wadda duniya ta sheda yanda suke tsananin sonta amma kuma tana tsaka da karatu kawai aka nemeta aka rasa baa sake samun labarinta ba tsawon shekaru sun boyeta batareda an sake taba ganintaba wanda babu wanda yasan dalilin hakan amma kuma a yanzu tana wannan qasar tana karatu sedai ta koma gida a yanzu batanan,
A familyn kowa mun samu bayanin cikakkiyar lafiyarsu banda JANNAH ZAD wadda babu wanda a iya binciken danai babu likitan daya taba ganinta bayan Dr Abraham……”
Dan shiru yayi yana tinani da shakkar abinda zai fada kafin ya dago ya kalli sayd wanda shima shi yake kalla da dukkanin imaninsa kafin ya juyo ya saci kallan AZIZ da yayi shiru yana sauraronsa da dan sassauta murya yace
“A yanda na tabbatar sbd bamu san health status din JANNAH ZAD ba a cikin familyn kuma dr Abraham ne kadai likitanta kuma Shi din likitan zuciya ne Tabbas itace takeda matsalan Zuciyar datake cikin zaadens,
Dr Abraham ya samu zomowa babban likitan dayake cikin manyan doctors na duniya tareda tarin dukiya me yawan gaske daya zamo babba sbd zaadens da suka tsaya masa,
Jannah Zad itace rai da Zad sukafi so fiyeda komai da suka mallaka a duniya…
Dago idanuwansa yayi Ahankali ya saukesu akan Sayd sbd a duka bayanin baiji wani abin daya shafesu ba bayan maganar ciwon zuciyar datai kama data tasa ‘yar dan haka ya zubawa sayd idanuwansa yana jiran bayaninsa wanda bayani kawai yakeso gamsashe batareda wani kwana ko daya ba.
#MAMUH
#BEST REVENGE
#BEST LOVE
#CRAZY LOVERS
#SELFMADE BILLIONAIRE
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*
