KALBIM BOOK 1 BY MAMUHGEE

KALBIM BOOK 1 PAGE 9

9
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
️️️️️️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

 

********
Tashi yayi ya fito cikin duhun ya sauya kayansa yaje toilet ya fito yayi alwala ya dawo dakin
A gefen ummita yayi sallah yafara sabon kuka yana fadawa Allah ummansa kadai yake fatan Allah yabata kyakkyan kariya tareda fatan dawowa garesa.

Har akai asuba yana fadawa Allah ummansa tareda neman jariya da yadda da duk kaddarar da zata tinkarosa a rayuwa ya basa ikon inganta rayuwar Ummitah har mutuwarsa.

A gida yayi sallar asuba bai fita ba kaman yanda yakeyi a baya,

Yana gamawa ruwan zafi yai dubara ya dora yazo ya gasa ummita dasu sosai ya mayar mata da kayanta ya fita yaje ya samo mata koko da kosai ya dawo ya bata kaman ma dura mata yayi.

Bai gama bata ba tayo masa amansa a jikinsa ya tashi yaje ya gyara mata jikinta ya sakeyi wanka shima ya sauya kaya ya sake bata kokon amma wannan karan batai masa amansa ba dan haka ya kwantar da ita tayi bacci har lokacin jikinta akwai zazzabi.

Basuda wasu kayan dan haka ya wanke musu wainda duka lalace sbd kada su fita dana jikinsu su dawo babu wasu na sakawar dan haka yana gama shanyawa ya dauketa suka fice.

Local government ya nufa acan yakaita wani chemist aka dubata akai mata allura aka basu magani ya siya mata bread sa freshYo na roba shikenan kudin hannunsa suka qare suka zagaya sosai nan ma ya bincika ummansa amma ba labari sai yamma sosai suka dawo gida.

Kwantar da ita yayi ya gyare gidan fes kafin yayi sallan magrib suka shige dakinsu ya rufe.

Yana yin sallan ishai kadan yaci bread din data rage da ruwa ya kwanta gefenta tareda rufesu sai a lokacin wani baccin azaba shima ya daukesa.

Seda aka fito sallah ya farka yayi sallah yayita addua har gari ya waye sosai ya fito baida ko sisin siya mata abinci dan haka ruwan wanka kawai ya samar musu sukai wanka ya dauketa suka fice zuwa gurin aikinsa.

Koda ya isa sbd rashin zuwansa kwana biyu tini aka saka wani a maimakonsa dan haka sedai ya tayasu suka dan hada masa dan abinda ya samu ya siyawa Ummitan Wainar gero taci yabata magani daganan ya nufi shagon dayake aiki a baya ko zai samu a karbesa suma.

Yama xuwa shima ya riga ya samu wani amma dai yace ya tsaya ko miqa abu ne idan an siya ya taya wanda yake shagon yanzu a dan ringa basa wani abin.

Haka ya zauna a bakin shagon da ummita wadda take lafe jikinsa har dare suka kai kafin ya basa 200 ya dawo gida.

Suna dawowa tuwo ya siya mata da 200 din taci kadan tasha magani ya cinye sauran yasha ruwa yai sallah ya kwanta.

Washe gari ma haka ya tafi ya ringa yawo garari da ummita yana dan kama aiki ana basa abinda zai siya mata abinda zataci saita rage yaci wani lokacin kuma ruwa kawai yakesha ya dawo su kwanta.

****rayuwa tai masa tsananin gaske dan kuwa daga shi sai ummita suke rayuwa yayi yawon neman umma har inda bai kamata suje ba sunje ba labari dan haka ya maida hankali sosai gurin tattalin Ummita wadda ita kadaice hope dinsa na rayuwa a yanxu,sbd ita ya dage yafara gwagwarmaya da rayuwa,

Tin dafe idan suka fita da ita yake yawon aikin wahalar dayake fama dashi se dare suke dawowa su shige su rufe gari na wayewa suke fita sai kuka wani dare.

Wahalar rayuwa yakesha sosai ga kulawa da ummita wadda ya kasa barwa ko mama sakina sbd tsoron bazai iya rayuwa ba ummitan a tareda shi ba dan haka yake gwagwarmayarsa da ita a gefensa duk da tafara qara wayo sosai kuma itama bata iya rabuwa dashi ko nan da can dan hakama sbd bata tsaro da kariya ya aske mata kanta daman batada yan kunne ya siya mata kayan gwanjo na maza ya maidata namiji sunanta kuwa kwata kwata baya fada cikin mutane kaman yanda ya hanata magana a cikin mutane sbd muryanta.

Ana cikin ya fara examsa dinsa dan haka tare suke zuwa makaranta ya zaunar da ita bakin window dayake ganinta har a gama ya fito ya jata su tafiyarsu gurin yawon nema.

Rayuwa tayi musu nauyin da duk kansa yafara neman kuncewa amma ya riqe sbd Ummitah dayayiwa kansa alkawarin inganta rayuwarta bazai bari insha Allah ta taso cikin qunci da azabar daya taso a cikinta ba,
Shine uwa kuma ubanta dan haka ko rayuwarsa zai iya siyarwa dan inganta tata.

***Ummita a tata rayuwar batada wani hasken data sani bayan BAABAH dinta wanda shi kadai ya isheta rayuwa, ya isheta jin nutsuwa da ganin haske arayuwar ba duhu ba,
Shine uwa kuma ubanta wanda take ganin indai gashi bata buqatan komai hakama shi kadai ne abinda take buqata a rayuwarta.

Daqyar ya kammala exams dinsa sbd babu lokacin zuwa aiki dan haka abincin dazai bawa ummita bama kansa ba yake musu wuya dan haka koda aka gama exams din yayi wani irin rama daga shi har ummitan sun bushe dan haka yana gamawa ya duqufa aikin kamfanin daya sake samu da tsaron shago yana hadawa biyu sai suka fara daidaituwa.

Ahankali abinci yafara wadatarsu kullum sunaci su koshi ya siya mata abubuwan buqata da nasa ma.

Ya siya musu katuwar fitila basa cikin duhu ko kadan yanxu,
Ya siyawa kansa waya yar qarama sbd jamb daya rubuta da kuma jiran kiran fitowar jarabarsu.

Rayuwarsu tafara daidaituwa shine malamin Ummita na karatun addini harma dana bokon dan haka tafara koyan karatu a gunsa kuma tana ganewa sbd yanada qwaqwalwa sosai dan duk tsananin rayuwar da suke ya tsaya ya samarwa kansa ilimi sbd burin dayake dashi akanta.

Mama sakina na cikin tsanani a gidan aurenta sbd baba ila daya tsaneta gaba daya tinda ta kasa cire su abdul a ranta duk ta rame ta qare akan tinaninsu da rayuwar da suke wadda bata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kwata kwata sbd Abdul rayuwarsa ta qare ne akan kulawa da ummita hakama bazai tabbata boyeta a amtsayin namiji na sbd girmanta idan yazo zai nuna hakama tayaya zaici gaba da iya kulawa da ita shi kadai dan haka take cikin damuwa me tsananin gaske da kuma batan Fatima daya tabata itama ta rasa kwanciyar hankali kwata kwata.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected