AMATULMALEEK Complete Hausa Novel
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK Complete Hausa Novel
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
1
BismillahirRahmannir Raheem
Shiru tayi tana sauraron yanda muryar kawunta ke tashi sbd yanda yake daga sautinsa cikin fushi da bacin rai,
Fushi da bacin rai ne sosai tareda gajiyawa bayyane a fuskarsa datake a hade Babu sauki ko rahama ko kadan,
Duk wannan fushi da bacin ran tareda daga sautin mahaifiyarta Dake zaune tana sauraronsa yakewa,
Daga ita maaman har ita ‘yar tata datai girman da ciwo takeji sosai aranta a duk lokacinda aka zaunar da mahaifiyarta ana mata irin wannan fadan takeji Babu Wanda ya dago acikinsu ya kallesa bare tankawa fadan dayaketa tada jijiyar wuyansa Yana yi,
Shi kansa kawu bellon akoda yaushe ransa tsananta Kuna da Baci yakeyi a duk lokacinda zaizo ya ringa zazzaga kwandon masifarsa a gabansu Amma Babu Me tankawa acikinsu Seya gama maama din ta bisa da yayi hakuri kawai,ita JANNAT ko kanta Bata dagowa bare tai magana.
Wannan Karan fadan nasa da maganganun nasa sunyi tsauri akansu Dan haka idanuwanta Dana maama din duk sun ciko da kwallan da Babu dayansu dakeson yaga hawayen Dan uwansa.
Zufan goshinsa ya share da babbar rigar jikinsa cikin maimaitawa maaman kalman karshe yace
“Tabbas idan Abdulhameed ya sake zuwa makarantar bokon Nan aka kawo min qararsa wlh tallahi almajiranci zan Kaisa bazan iya da baqin ciki ba ‘dan uwana ya mutu be barmun komaiba Se lalurarku,
Idan bazaki tsaya inda Allah ya ajiyeki ba keda yayanki to ki tattara ko qara gaba bazamu iya ba”.
Juyawa yayi yabar gurin batareda ya Dena masifa da fadan da yake yi din ba harya bar kofar qaramin sashen nasu da Tin bayar rasuwar mahaifinsu suke su kadai cikinsa.
Numfashi maamah din ta sauke batareda Kalli gefen da AmatulMaleek din take zaune ba itama tana cigaba da dinkewa Abdulhameed wandonsa Daya barke da allura duk Bata Wani iyaba sbd shekarunta Basu Kai ta iya din sosaiba.
Dukkaninsu Babu Wanda yace komai sbd AmatulMaleek din tsananin zurfin cikinta yayi yawa duk da yarintarta Amma sosai ta iya danne abu ta boyesa a ranta.
Maamah datasan AmatulMaleek din ba magana zatai ba sai kawai ta hadiye hawayenta sbd kada ma AmatulMaleek din ta Gani ta miqe daga zaunen datake ta nufi kayan wankin data fitar masu shegen yawa tafara yi.
Satar kallanta AmatulMaleek tayi tareda ajiye allura da zaren hannunta tana zubawa maamah din fararen idanuwanta batareda tace komaiba,
Abu Daya ne koyaushe yake yawo aranta shine idan har Mommy ‘yar uwar maamah dince meyasa koyaushe Se dai a Turo musu kaya da abinci Amma takasa rabasu ta daukesu daga wannan azabar rayuwar wulaqanci da tozarcin da suke ciki a hannun dangin mahaifinsu,
A duk lokacinda abincinsu ze qare qaninta dayake qanqani sosai bara yake zuwa yayo ya samo abinda zaici su kuwa Se dai su wuni su kwana ahakan Kokuma maamah tayiwa matan gidan aikin abincinsu na dare idan ta gama a San mata Wanda zataci da ‘yayanta.
Babban mamakinta a duk ranar da aka kawo musu kayan abinci daga gurin mommyn a ranar ake taruwa a rarrabe komai abarsu da Wanda iyakacinsu kwana biyu ya qare sun koma cikin tsanani..
A rayuwar dasuka taso gidan dayake dauke da iyayensu Maza yanne da qannen mahaifinta kowannen da iyalinsa daga me mace biyu sai me mace uku harma dame hudu Dan haka gidan yake na taro,
Kowa acikin gidan kansa ya sani sai iyalansa,
Babu me iya taimakawa Wani sbd kowa nauyin dayake kansa ma yafi karfinsa Dan haka kusan rayuwar kowa tasa ta fishesa akeyi.
Su biyar ne manyan gidan Maza Kuma kowannensu Yana cikin gidan da nasa iyalan Babu Wanda ya bar gidan duk kuwa da zaman matsuwa da akeyi a gidan,
Babanta shine qaraminsu gaba Daya Kuma shine yayi karatun Boko Kuma shi kadaine yake aikin gwamnati a primary school din Dake qauyen nasu wanda Babu yanda baayi dashi yabar kauyen yaje abasa Wani aikin Amma yakasa tafiya anan yake vice principal har manyanci yaxo ya rasu yabar matarsa da ‘yarsa Daya AmatulMaleek dakuma jaririn qanin Amatun Wanda aka mayar masa sunan mahaifinsa Abdulhameed.
Kafin rasuwar Babah rayuwarsu acikin gidan ahalinsu me suna Sanda Fulde rayuwa ce data bambamta da duk ahalin gidan sbd gata da kulawa da Babah ke Basu itada mahaifiyarta,
Babah baitaba raayin Kara aureba sbd matsi da rayuwar gidan take ciki dakuma ganin yanda tarbiya ma Neman gagara takeyi ga Yan uwansa sbd yawan iyalai duk da kusan da yawa yaran gidan shine yake dauke da lalurarsu sbd nasu iyayen bazasu iyaba ba hali Kuma ahakan bawai sun Dena haihuwar bane.
AmatulMaleek itace hasken idon mahaifinta sbd burinsa da buqatansa na son kebantar da tarbiyarta daga sauran yaran gidan da tarbiyarsu takeda qaranci duk da Yana iya kokarinsa gurin Basu tarbiyar Amma Yana yi ne iyayensu na warwarewa Dan haka ya tsayu sosai Akan tasa ‘yar wadda yake burin tata rayuwar ta ingantu dama sauran kannanta da zasuzo Dan haka baiyi qasa a gwiwa ya Sakata karatu Wanda kaf gidan a mata ita kadaice ta shiga karatun bokon.
Ya rufe idanuwansa tareda kunnuwansa ga duk abinda zaa fada akan ‘yarsa da rayuwar Daya zabar mata Dan haka ita kanta AmatulMaleek din ta taso tamkar miskiniya Bata Hulda ko iya shiga mutane sosai hakama Bata iya fita daga sashensu zuwa kowane sashe agidan sbd sunyi yawan sosai a gidan da kusan daga Wani bangaren idan zaka Wani bangaren sai Wani acikin mazan gidan ya tare yarinya ya lalatata a hanyoyin gidan dasukeda duhu wasu lokutan,
Da yawa yaran gidan wasunsu sun lalace ne a tsakaninsu Wanda haka ake rufe idanuwa ana daura musu aure da junansu.
Wannan shine Mafi girman abun Dake daga hankalin Babah da maamah akan rayuwar AmatulMaleek data fita daban a cikin yaran gidan Dan haka Sam Babu inda Amatun ke fita idan ba tareda mahaifinta ba Koda kuwa aike ne to tabbas hannunta na riqe dana mahaifinta.
Akwai tsautsayin Daya taba kusan afkuwa ga AmatulMaleek din Wanda shine abu na farko Daya daki zuciyar Babah ya Sakar masa ciwon zuciyar Daya zamar masa ciwon jiki Wanda daga karshe kusan shine ajalinsa.
Daga Aiken Amatun can kuryar gida Wani babban Dan kawunta ya dafeta cikin soron gaba ya rufe mata Baki batareda ya bari ta gansa ba yaso illata rayuwarta batareda laakari da shekaruntaba.
Babah ne da kansa ya riski wanna mummunan kaddarar data Saka Yanke jiki ya Fadi Allah yasa Babu abinda ya faru din AmatulMaleek din ta tsira Dan haka ya tattara masu kayansu itada mahaifiyarta zuwa Abuja gurin ‘yar uwar Kuma Aminiyar maamah sukai zamansu acan sai bayan kusan watanni masu tsayi suka dawo.
Bayan dawowansu zuciyarsa Bata taba samun nutsuwa ko kwanciya ba da rayuwa acikin gidan Kuma ba Dan haka ya kama haya a kusa da gidan ya koma da iyalansa,
Acan rayuwarsu ta inganta hankalinsu ya kwanta a lokacin ne AmatulMaleek tafara wayon sanin alaqar mahaifiyarta da ‘yar uwarta Mommy abeeda wadda gabaki daya rayuwarta data maamah ta bambamta Kuma bambamci me girman gaske.
Da farko Bata taba sanin ba uwa Daya Uba dayane ya haifesu sai daga baya idan sunje gidan mommyn Taga yanda mahaifiyarta ke aiki cikin masu aiki tafara fahimtar tabbas ba uwa Daya ce ta haifesu ba Amma har lokacin tana Saka ran Uba Daya ne ya haifesu.