Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel
Sosai Dada taji daɗi dan haka ta shiga sanya mata albarka. Daga haka ma sai ta miƙe tana faɗin, “To bara na wuce tunda na kammala abinda ya kawo ni. Sai na jiki ɗin”.
Da sauri yabar jikin ƙofar ya shige bedroom ɗinsa. Wani irin harbawa zuciyarsa keyi da sauri-sauri. Dan shigarsu ɗakin babu jimawa ya shigo gidan. Duk da yay mamakin ganin mota baƙuwa a waje yay zaton kota Lulu ce aka kawo saboda bai ga driver ba, ashe ya ɗan fita miƙe ƙafa. Ya shigo gidan yaji shiru, ya wuce ɗakinsa kai tsaye ya ajiye kayan hannunsa shine ya nufo ɗakin Lulu da tunanin ko barci take. Kawai yaji Dada na magana a hanakali cikin salon makirci na tsoffin mata tana bugar cikin Lulu, shine fa ya nutsu. Jin komai ya sake tada masa da hankali, dan yanzu ne ya fahimci ainahin abinda take nufi da wata ɗaya wata ɗaya da take ta ambata masa zata koma free. Zuciyarsa ta sosu da tunanin shima Uncle Yousuf yaudararsa yake kenan? Sai kuma wata ke kwaɓarsa akan kada yay zargi cikin fushi, ya bincika dai sannan. Sunayen ALLAH ya shiga ambata har ya samu nutsuwar ajiye tunanin a ransa gefe, sai kawai ya faɗa wanka. Lokacin da yake fitowa yaji fitar motar data kawo Dada, sai kawai ya ƙarasa kimtsawa da yin shirin fita sallar magrib ya fito.
Lulu da ke kwance a falo ta wani ɗan zabura alamar tsorata da ganinsa. Murmushi ya sakar mata da lumshe idanu yana kaiwa zaune kusa da ƙafafunta. “Matsoraciya relax ba aljani bane ni ne?”.
“Taya zan yarda da haka bayan kace sai gobe ne zaka dawo, kuma ina wajen banga sanda ka shigo ba”.
Murmushin ya sake sakar mata, a nutsensa da deep voice ɗin nan tasa dake fita da sanyin damuwar abinda yaji na tattaunawar ta da Dada duk da yana ƙoƙarin dannewa ya ce, “Mun gama abinda ya kaimu ne shine kawai muka yanke dawowa gida. Sanda na shigo kuma kina ɗaki ne da baƙuwa. Namayi zaton har zan kammala wanka nazo mu gaisa duk da bansan wacece ba”.
Kaɗan ta sauke numfashi da ɗage kafaɗunta. “Dada ce kuma ta wuce. Tazo ne akan maganar zuwa duba Grandpa da aka wuce da shi London jiya”.
“Ya salam jikin nasa ne dai?”.
“Wlhy kuwa, fiye ma da yanda ake tsammani, dan a shekaran jiya doctors suka gano wai anyi poising ɗinsa ne da gubar da bata baiyana kanta sai tai kwanaki a jikin mutum”.
“What! Sai kace wani a film?”.
Lulu ta ce, “Hummm a tunaninka a Film kawai ake waɗan nan abubuwan? To a Nigeria ma a zahiri anayin fiye da haka. Kasan Grandpa ya Bama siyasar nan amanna matuƙa, shiyyasa muke tunanin ko’a cikinsu ne musamman daya kasance a hasashenmu a zuwa Legos ɗin nan da yay abun ya faru. Yanzu dai haka jami’an tsaro sun duƙufa bincike kan al’amarin ma”.
Matuƙa Smart ya girgiza. Dan baiyi zato ko tsammanin wai da gaske irin wannan abubuwan da ake gani a Film na faruwa a zahirin rayuwar mutanen ƙasarsa ba. Kiran salla ta sashi miƙewa yana faɗin, “Ina ƴan hutun naki? Naji gidan shiru”. Bedroom ɗin da suke ta nuna masa. “Suna ciki fa, tunda muka dawo saloon suka kwanta wai sun gaji”. Kallonta ya tsayayi kamar zai yi magana sai kuma yay shiru dan shi dai bai san da wani fitarsu saloon ba. Zuciyarsa ta lallashesa akan a tari gaba. Yanzu zantukan ta da Dada ya kamata ya maidama hankali. Kafaɗa ya ɗan ɗage hannayensa duka a aljihu, ya ce, “Okay bari naje salla na dawo. A ɗan samamin wani abu mai ruwa-ruwa haka yunwa nake ji”.
Harararsa tai da faɗin, “Kafa dawo zaka fara takurama mutane da mulkinka ko”.
“Ni na isa. Karki damu cikin su Maryam wani yayi ki huta abinki. Ki dai tashi kiyi salla. Bara naje sai na dawo”. Daga haka ya fice kafin ma tace wani abu……….✍️
‘…..!!
8️⃣3️⃣
……..Bayan an idar da salla har ya nufo hanyar gidan sai kuma ya dakata. Napep ya tare ya shiga tare da gaya masa inda zai kaisa. Cikin ka ƙanƙanin lokaci suka iso. Ya biya sa kudinsa sannan ya shiga gidan bayan sun gaisa da maigadi. Ahmad na zaune a falonsa ya barbaza takardu ga laptop a gabansa Smart ya shigo. Ɗagowa yay yana kallonsa cikin nuna mamaki. Smart ya watsa masa harara da faɗin, “Lafiya kake kallona?”.
“Inafa lafiya, kai da nake tunanin kana can kana aikin ALLAH yanzu kodan kewar juna da akai amma sai na ganka anan”.
Ƙaramin tsaki Smart yay yana kaiwa zaune da faɗin, “Banza ɗan iska kaifa baka tauna magana kafin ta fito maka a baki”.
Dariya Ahmad yayi da cewa, “Gara na dinga muku ɓaro-ɓaro kuyi ku aurar dani kuma ku huta. Amma fa sai naga kamar kana cikin damuwa. ALLAH dai yasa ba wani abu ka tarar a gidan ba?”.
Smart baida yawan magana. Sannan akwai zurfin ciki. Duk abinda kaga ya bayyana shi ga waninsa to lallai ya matuƙar girgiza shi ne. Sosai ya nisa da furzar da iska mai zafi. “Ahmad akwai matsala ne”.
“Ya salam matsala kuma Mawashin. To tami? Akan kuma mi?”.
Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya ɗago yana kallon Ahamd ɗin da shima ya zuba masa idanu. “Badan ina son fara tona sirrin gidana bane, al’amarin ya girgiza nine ina buƙatar shawara dan kar na aikata abinda ba haka yake ba. Bayan kun saukeni na shiga gida sai na samu…….”
Tsaf ya zayyane masa abinda yaji tsakanin Lulu da Dada na tattaunawa. Shima kansa Ahmad yasha mamaki. Amma sai ya dafa Smart yana jinjina kansa. “Niko kaga ko bana jin shi Yaya Yousuf da wata manufa yay hakan. Domin idan ka auna zancen tsohuwar zaginsa take akai-kaice shima. Sai naga yayine domin ma Mawaddat wayo kawai”.
“To miye na wayon anan Ahmad, aure ne fa kuma ta isa aure tunda ba gunkinta zasuyi su kafe a gidan ba. Kawai dai akwai abinda suke shiryawa a kaina na yaudara”.
“No no relax kar kabari ka yarda da hakan. Sam sam bazaiyi hakan ba. Amma ina zuwa dai”. Waya Ahmad ya ɗakko yay kiran Uncle Yousuf. Da ƙyar ya samu ya shiga kasancewar har yanzu bai dawo ƙasar ba. Sun gaisa cikin mutunta juna batare daya nuna yana tare da Smart ba. Uncle Yousuf daga can cikin tsokana yace, “Yaya dai Auta ko batun auren ne ya tashi akeso na fara haɗo lefe?”.
Dariya Ahmad yayi da faɗin, “Kai haba Yaya a’a. Wannan ai sai kun yarda da zaɓina sannan zamuje wannan matakin. Duk da nasan ma kunaji da gudu zaku amince. Wani abu ne fa da na jiyo ya girgizani. Sai nace bari dai na kiraka ko kasan da zancen”.
“Oh to Masha ALLAH, ALLAH ya tabbatar da khairan sa. Minene kake son ji haka?”.
“Uhm wlhy Yaya nafaje gidan Smart ne ɗazun sai na samu Mawaddat na waya cewar ai ta kusa komawa free nan da 4days aurenta zai ƙare da Aliyu. Abin ya girgizani matuƙa”.
“Ya Arrahaman”. Uncle Yousuf ya faɗa daga can cikin dafe kai. “Yaya kama sani kenan?”. Numfashi Uncle Yousuf yaja da saukewa. Sannan cikin nutsuwa ya sanarma Ahmad yanda akai zancen ya fito, ya ɗora da faɗin, “Ni ko ma Aliyun bamma maganar ba dan ba haka bane a raina. Wannan auren ina fatan sai mutuwa ce zata rabashi. Na saki jiki ne da tunanin tana zuwa gidansa zaibi duk hanyar daya dace wajen mantar da ita wannan shirmen. To ashe wata sabuwa ita hakan na ranta. Dole ne na kira Aliyu na sanar masa komai sannan kuma ya ɗauki duk ma matakin daya dace akan hakan. Amma zanyi ƙoƙarin dawowa nima duk da ban gama abinda nake ba. Dan ALLAH kaima ina son ka zaunar da Aliyu ka nuna masa abinda ya dace akan wannan batun. Idan ma yana ma Mawaddat saku-saku ne ya ajiye gefe ya koma wuta-wuta tasan shi bamu bane ba. Idan komai ya daidaita ya mata sauƙin”.