Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel

Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel

“Shike nan Yaya insha ALLAHU yanda mukai da shi zakaji”. Daga haka ya yanke kiran. Smart yaji komai dan a hansfree yasa baya buƙatar ƙarin bayani, sai ma ajiyar zuciya da ya sauke dan ya fahimci Uncle Yousuf ɗin da manufarsa akan hakan. Ya kuma daina ganin laifinsa dan ko shine abinda zai yi kenan domin toshe kowace matsala da zata iya ta taso a lokacin…. Ahmad ne ya katse masa tunani da faɗin, “Mawashi a yanzu fa wannan yaƙin naka ne bana wani ba. Kai ya kamata ka nuna mazantaka komai ma za’ayi ayi karka biye mata. Sannan na fahimci kamar ido ka kawo ka zubamata shiyyasa ma take ganin komai normal ne. Dole fa kai ƙoƙarin dashen shukarka dan hana kowace irin barazana tasiri. Dan hatta da ita kanta hakan da zakai zai karya lagonta dan bazata taɓa yarda a tunɓuke wannan shukarba”.

Tsaf Smart ya fahimcesa dan haka yay ɗan gajeren murmushi yana girgiza kai. “Ahmad bazaka fahimta ba. Mawaddat fa ta wuce duk yanda kake tunani. Sannan ni harga ALLAH bana son zuwa gareta batare da amincewarta ba. Shiyyasa na sake mata tare da nuna mata har yanzun a ƙasan nata nake dan hakan ne kawai zai iya karya lagonta harta saki jiki dani. Kuma Alhmdllh naga hakan yana tasiri sosai akanta . Taya kake tunanin yanzu na tunkareta da wannan sigar ai babu zaman lafiya”.

“Humm kaifa na manta ashe sunanka namiji ɗaya tilo a tsakkiyar ƴaƴa mata shiyyasa. Mawashi na yarda da yanda ka tsara ɗin kuma hakan ma hanyar maslaha ce mai ƙyau da anan gaba ita kanta sai tayi alfahari da kai. Amma kai ya kamata ka memo hanyar da zakabi ta amince maka da kan nata ku zama ɗayan. Mudai fatan mu ai ayi shukar dan shi kaɗaine nake ganin zai hanata kowane irin motsi musamman daya kasance a yanzu tanada defenders a gefe kuma masu ƙarfi.”

“Na yarda da kai, amma kuma tayaya zanyi hakan batare dana ɓata abinda na fara ginawa a zamanmu ba?”.

Dariya sosai Ahmad ya shigayi har sai da Smart ya fara ƙuluwa sannan ya sassauta. Ya ce, “Shiyyasa nace kaifa gata yay maka yawa na kasancewarka ɗa namiji ɗaya tilo a tsakkiyar mata shiyyasa abubuwa da yawa kai hoto ne. Karka damu wannan aikina ne. Kai dai yanzu tashi ka koma gida ka maida komai ba komai ba. Amma yaran nan data cika gida da su ka tattarasu gobe su koma gida”.

Cikin ɗan taɓe baki Smart yace, “Dama zasu koma goben ne ai saboda school. Amma ka faɗamin mi zakayi?”

“Babu ruwanka da abinda zanyi, ai kasan dai bazan cutar da kai ba.”

“Na sani, amma dai ya kamata ace na sani ko”.

“Karka damu zaka sani, nima sai nayi mazari”

Daga haka suka fito anan massalacin ƙofar gidan su Ahamd sukai salla. Ya amshi key ɗin motar Ahmad ya wuce gida. Yanzu kam ya samesu su duka a falo suna kallo. Sannu da zuwa suka shiga masa a zatonsu isowar kenan. Ya zauna yana amsa musu da tambayar lafiyarsu. Lulu na zaune a ƙasa tana shan fruits da aka yayyanka a bowl. Ta sauya kaya alamar wanka tayi, dan wando ne da riga marasa nauyi a jikinta. Kan babu ɗan kwali ya dai sha gyaran da sukayo yau sai ƙyalli yake yi. Idanunsa ya ɗan lumshe da sake lafewa cikin kujerar zantukan Ahmad na dawo masa a rai dalla-dalla. Shi yasan akwai ƙura, dan ko za’a kaisa jail sakinta bazai taɓayi ba koda a mafarki ne. Maryam ce data kawo masa abinda yace a masa cikin hikima ta janye su Amrah suka koma ɗaki tunda acan ma akwai tv. Lulu ta bisu da kallo tana faɗin, “Ku kuma ina zaku muna hira?”. Da dariya Maryam tace, “Aunty muna zuwa sirri zamuyi mu dawo yanzun”.

“To ALLAH dai yasa bani za’a ƙullawa ba”.

Dariya suka shige sunayi, yayinda Smart ya sakko ya zauna a ƙasan kusa da ita. Hannunta ya riƙo ya kai apple ɗin data ciro jikin cokalin bakinsa. Juyowa tai ta hararesa. Yay murmushi da ɗan kashe mata ido ɗaya. “Idan ma ke zasu ƙullawa ba gani a kusa da ke ba sai na kunceki tsaf na maida igiyar kansu Madam”.

“A’a Granny ƙarewar Madam”. Ta faɗa tana sake balla masa harara. Dariya yayi yanzu kam fararen haƙoransa na bayyana da ƙyau. Sai da taji wani zuuu cikin kanta amma tai azamar ɗauke idanun cikin basarwa. Shiko ya cigaba da faɗin, “Ai ki godema ALLAH da baki zo a kakar tawa ba. Gaskiya da Kinga takanki dan sai na addabeki”.

“Sai dai ko mu addabi juna. Dan kaima kasan Lulu ƙamshi ba kanwar lasa bace.”

“Niko nasan haka”.

Ya faɗa cikin ɗage gira. Kankanar data tsiro ta tura masa a baki tana harararsa. Ya shiga shan abarsa yana murmushi. Itako ta maida hankalinta a kallon da sukeyi dan tana matuƙar son film ɗin duk da horro ne. Shima gyara zamansa yayi ya matsa jikinta sosai ya jingina bayansa da kujera kamar yanda tayi. “Wai sai sha kike baƙya bani ALLAH sarki autan Ammah akwai haƙuri”. Ya faɗa a mararairaice. Juyowa tai ta kallesa, sai kuma ta kalla fruits ɗin. “Oh kace kwaɗayi ya zaunar dakai nan ɗin ba kallo ba ashe?”.

“To kusan haka”.

Ya bata amsa yana shafar sumar kansa da bata da yawa can sosai, sannan tafi saisaye kuma. “Kwaɗayi dai mabuɗin wahala ne” ta faɗa tana tsiro abarba ta miƙa masa. Maimakon ya amsa cokalin sai ya riƙe hanunta ya kai abarbar bakinsa a haka da nata hannun. Batace komai ba ta janye hanunta daga nasan. Sai ta koma idan ta sha saita tsira ta miƙa masan, shi kuma ya riƙe hannun nata ya kai bakinsa. Harda ɗan kwanto kansa a kafaɗarta kaɗan. Shagala datai a kallon yasa bata maida hankali ba duk da tabbas tana jin kan nasa a kafaɗarta sai dai ba sakar mata nauyi yay ba sosai.

“Wai ko ki tambaya inda naje, da zan tafi baki tambaya ba. Ina can munyi waya baki tambaya ba. Na dawo ma haka. Anya zaman tare yace haka Mawaddatan’warahmah”.

Yanda ya kirayi sunan nata sai da taji zuciyarta ta motsa. Duk da kuwa Uncle Yousuf kan kirata da sunan lokaci zuwa lokaci. Kansa da ke a kafaɗarta ta ture da faɗin, “Mi haɗina da tafiyarka da dole zan dage sai naji. Ko salan a kirani mai gulma kuma”.

“Haka ne kuma fa”.

Ya bata amsa cikin rashin damuwa. Sai kuma ya jawo tray ɗin da Maryam ta ajiye ya buɗe ƙaramin flaks da ta saka kunun madara a ciki ya zuba a cup, kaɗan yasa suga. Ya fara sha ya lura tana kallonsa. Kofin ya miƙa mata batare da yayi magana ba. Sai ta ɗan yamutsa fuska tana girgiza kanta.

“Da akwai daɗi fa, ɗan-ɗana kaɗan kiji”.

Kamar bazata amsa ba sai kuma dai ta amsa ɗin, kaɗan ta ɗibo a spoon ɗin takai baki. Sai ta ƙara ɗibowa tana kallonsa. “Akwai fa daɗi, ni dana ga tanata haɗa-haɗa sai na ɗauka jagwalgwali ne kawai”.

Murmushi yay mata da amshe spoon ɗin yana faɗin, “Karkuma ki shanye min to daga tayi”.

“Oh ashe ba daɗi ni ka shanye mun fruits ɗina.”

“Tofa gori ne abun? To shikenan musha”. Ya faɗa yana miƙa mata. Amsa tai ta sha ta miƙa masa itama, haka suka dingayi yanzun ma dai da spoon ɗaya suna kallo. Ya ƙare ya sake ƙara musu wani. Sai gashi sun shanye kunun flaks ɗin duka. Farfesun dake cikin kwanon kuma bai ciyu ba. Suna a falon har sai da Film ɗin ya ƙare. Shi ya kwashe kayan ya kai kitchen tare da kashe komai ya rufe ƙofar. Ita kuma ta tattara kayanta ta wuce ɗakinta ko sai da safe babu. Da kallo kawai ya bita yana girgiza kai, shima sai ya nufi nasa ɗakin. Sai da ya kammala komai na al’adarsa kafin kwanciya sannan ya canja kayansa zuwa na barci yasa turare yay brush ya fice. Lulu na zaune a tsakkiyar gadonta tana aiki a system ya shigo. Kallonsa take da mamaki daga sama har ƙasa. Kafin cikin ƙarfin hali ta ce, “Lafiya kuwa?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected