Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel

Furar Danko Book 1 Complete Hausa Novel

“Kar kiji shakkar komai, Aliyu na *_SONKI_*, yana kuma buƙatar ki matsayin uwar ƴaƴansa abokiyar rayuwa ta har abadan Mawaddatan’warahmah. Na miki alƙawarin bazaki taɓa dana sanin zama mallakin Aliyu ba, in sha ALLAH sai na nunama duniya Mawaddatan’warahmah ba Lulu da suke kallo kawai bace akwai wani babbar nagarta tattare da ita”.

Murmushi ta saki mai ɗan sauti ta buɗe idanunta data sake rufewa suka zubama juna ido. “Mi kake nufi Aliyu?”.

“Baki LABARI kawai zai baki, amma gangar jiki tabbatar wa zatai kafin zuciya ta amayar da sirrin da ke cikinta. Alƙalamin ƙaddara ya jima da bushewa Mawaddat, hakama takardu sun daɗe da ɗaguwa. Miya rage garemu? ƙarasa zuwa filin yaƙin da zai bayyana Aliyu mijin Mawaddat ne kawai domin hutar da zukata masu farautar igiyar da UBANGIJI ya riga ya gama ƙadarta ƙulluwarta tun kafin haihuwar mu…..”

“Bana gane zance a curkuɗe ka buɗemin kawai Aliyu, kana saka ni a duhu da dogon nazari a duk sanda ka ɗauki wannan tsagin na curarrun kalamai”.

Goshinsa ya kai saman nata, hancinsa na gogar nata suna shaƙar numfashin juna. Ya saki murmushi mai sauti. “Ki bani damar baki gaba ɗayan kundin curarrun kalamai na, ni kuma zan kasance miki malami mai fassara miki su feji bayan feji a mabanbanta zangunan da masu neman ilimin kan jima basu cimmawa ba Please Mawaddatan’warahmah, na fara gazawa, ni kuma bana buƙatar shiga makarantar da babu shaidar samun damar ɗaukar darasi a cikinta, dan zata kasance min tamkar ɗan yawon buɗe ido ne kawai”.

“Mi kake buƙata da ga gareni?”.

“Yarda”.

“Karka zama bahagon malami”.

“Ki zama ɗaliba mai kaifin basirar ƙarɓa da haddacewa, domin ranar amsar sakamakon jarabawa ki ɗauki first class”.

“Jarumta da kaifin basira a jinina suke”.

“Ni mai yarjewa ne ga dukkanin furucinki, domin tabbatar miki da hakan muje matakin farko na tabbatarwa *_ALJANNAR DUNIYA TA_*”.

Saukar lips ɗinsa akan nata ya hanata damar furta abinda ta so faɗar, hannu biyu ta amshesa kasancewar ita a karan kanta bata sana wacece ita a wannan fagen yaƙin ba. Abinda kawai ta sani gangar jiki da zuciya duka sun karɓa saboda hakan ne mafi ƙololiwar miradinsu a wannan gaɓar bisa tirsasawar abinda tasha batare da sani ba. Al’amari fa kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan su duk biyun cikin mata kai kowa ya fara kaima ɗan uwansa hari irin na ƙasa da ƙasa. Kafin kace mi sun birkice ma juna daga haka fa labarin ya canja a yanda su duka ba haka sukai tunanin rubutuwarsa ba, dan kuwa dai tabbas wannan daren yazo ne a bisa rubutun alƙalamin ƙaddarar da basu isa canjata ba koda ace sun so hakan. Lokacin da al’amari yay nisan zango Lulu ta fara dawowa a hayyacinta da fahimtar mike shirin faruwa. Sai dai me, Smart ya kai matakin da _Uranium_ ya ke shirin jefawa fa a ƙasarta ba nuclear bomb kawai ba.

“Aliyu! Aliyu!! Hydar!!” ta shiga ƙwala kiran sunansa a matuƙar firgici na fita a hayyaci numfashinta na barazanar barin ƙirjinta saboda tsabar shiga firgici, sai dai ina wannan yaƙin na bashin gaba ne ba na kece raini kawai ba. Kuka ta fashe da shi da cigaba da kwala kiran sunansa da magiya kai harma da tabbatar da zata halakashi amma ina, turnuƙun ƙurar yaƙi ta lulluɓe ji da ganin idanu da kunnuwa sa, yafayi alƙawarin yau sai ya kai duk wani shegen tsageran kafiri ƙasa ko shima a lissafashi a jerin manyan jaruman mayaƙa da suka amshi turar ƙasa data MUSULUNCI a hannun dama. Wannan da shi ake kira TURNUƘU faɗan ibilisai, yaro bai gani ba balle ya raba….

A wannan turnuƙu duk wani wanda Lulu kema kallon defender a rayuwarta harma da ƴan koron abi yarima a sha kiɗa irinsu Deen sun sha kiran kawo ceto sai dai da alama ko fankar ɗakin tsoron ya hanata iya juya kanta balle su da ke nesa da jinta maybe ma wasu suna can a cikinsu suna mafarkin aljanna da naman kaji da madara.

(ALLAH kasa munada rabon zuwa ba’a mafarki kawai ba mu da masoyan mu baki ɗaya. Amma fa safiyar gobe dole a sake maimaita ƙaramin yaƙin basasa kona wucin gadi ne tsakaninmu da Smart team sai sun mana dalla-dallar yanda akai aka kawo mana wannan yaƙin sunƙurun haka)

____________★

Zaune take hakimce uwa wata sarauniya a makeken falonta tana ma ƴaƴan itatuwa tsinci ɗai-ɗai. Mai aikinta na daga ƙasa tana tausa mata ƙafafu. Kamar wanda aka jeho da ga sama ya faɗo falon, zaburar da mai aikin tata ta ɗanyi ne ya saka Dada janye idanunta da ga kan tv ta dubeta, masifar tata tai shirin balbaleta da ita, sai kuma tai tsit saboda gyaran muryar da yayi. Gaba ɗayanta ta juyo ta dubesa, sai kuma ta saki baki alamar mamaki.

“Sulaiman? Kai ne?”.

Murmushi yayi a karo na farko, sai kuma ya cigaba da takowa cikin falon. Kafin ma wani a cikinsu yay magana mai aikin Dada ta miƙe zumbur dai-dai yana kaiwa zaune a kujerar kusa da Dadan da faɗin. “Ni ne fa Dada. Mun sameku lafiya?”.

“Sulaiman bakai fushi ba kenan?”.

Ƙaramar dariya yayi da kamo hanunta cikin nasa, cike da sauke murya ya ce………✍️

 

 

‘…..!!

 

8️⃣7️⃣

 

………“Dada wane ɗa ne zai yi fushi da iyayensa. Balle ma ke nasan baki da laifi akan wannan al’amarin sam.”

“Naji daɗi da ka fahimci haka Sulaiman, dan babu ta yanda zan goya bayan bare sama da jikana. A yanzu haka koda akai min katanga da bibiyar halin da kuke ciki ban zauna ba, kuma nayi alƙawarin sai Mawaddat ta dawo hanun Tajuddeen matsayin mata dan bazan taɓa amsar waninsa ba”.

Wani irin farin ciki ne ya ratsa Alh. Sulaiman, dama shi yasan Dadarsa na tare da su. Dada dake murmushin itama ta ƙara ƙasa da murya da faɗin, “Labari ma mai da ɗi……” Tsaf ta kwashe yanda sukai da Lulu ta sanar masa. Baima san sanda ya lailayo wata ashariya ya dire ba a gaban mahaifiyar tasa. Ya ce, “No wander naga yaron nan Yousuf nata rawan kai, ashe shegen shine ya ƙulla komai”.

“Wlhy kuwa, nima abin ya girgizani Sulaiman. Amma ka kwantar min da hankalinka jibi da kaina zanje na ɗakko Mawaddat ko yaron nan na yawo da ubansa a baya sai ya saketa”.

“ALLAH ya barmin ke Dada ta”.

Ya faɗa cikin wani irin matsanancin farin ciki. Gaba ɗaya damuwarsa ta shafe ma. Bai iya dogon Zama ba a gidan bayan sun ɗan tattauna akan abinda ya samu Baba da ta bashi labari ya wuce gida kasancewar dare ya fara yi, yana tabbatar mata gobe idan ALLAH ya kaimu Tajuddeen zai zo ya gaidata, da dai ya ɗauki fushi bazai sake zuwa wajensu ba, amma yanzu zai lallasoshi, dan zai sanar masa ƙoƙarin da take masa. Sosai Dada taji daɗin hakan, dan ita kam ALLAH ya jarabceta da shegen ƙulafucin ƴaƴanta da ma jikokin duka. Sai dai kuma matan ƴaƴan nata da babu wanda ta ɗagema hula a rashin mutunci, juyasu take san ranta kamar waina a tanda kamar yanda ta kame ƴaƴan nata ram a hannu sai yanda tace musu, Alh. Sulaiman ɗin nema dai kan botsare mata a wasu lokutan dan shima dai halayyar tata ce ya ɗebo tsaf. Shiyyasa takanji shakkarsa duk da kasancewar itace ta haifesa, san nan tana sonshi sosai wannan a bayyane yake a wajen kowa ma, dan sam idan rashin mutuncinsa ya tashi ba raga mata yake ba tun ma yana ƙaraminsa, balle yanzu da yake jin ya gawurta da tumbatsa a gidan ta fanin dukiya da yin suna a cikin ƴaƴan nasu. Amma a kullum Dada bata ganin laifinsa sai ma bashi goyon baya da takeyi….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected