Rainon Soja Book 3 Hausa Novel

Rainon Soja 72-73

72-73
*Littafin na ku?i ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment?500 Vip payment?1000 SPC payment?1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409….?????#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Tana furta hakan da sauri ta juya cike da ?afa tana ficewa daga falon . Bin ta da kallo mami tayi kamin ta furta “ Ikon ALLAH! Wannan yarinyar daga ina take haka? Kar ki damu Mami kiyi Ha?uri, zan sa a binciko mun naga yar gidan uban waye? . Khalil ya furta yana janye idanun sa daga hanyar da Nasreen ta wuce . Mom Hajara ce ta furta “ a yau nake so ba sai gobe ba! Murmushi Khalil yayi yana furta “ Kiyi Ha?uri Momy yau inshallah ”. Juyawa yayi yana bin bayan Nasreen don shima ran sa sosai ya ?aci da ita …..Bin bayan sa Suka yi da kallo Mami na sauke wani irin gwauron Numfashi kana tace “ Ya tabbata Ali yana kula watsatstsun mata irin wannan yarinyar kenan? . Ta furta zancen tana kallon su tare da fa?awa cikin wani irin yanayi na daban.

Kallon ta jidder tayi tana kallon mom Hajara wacce itama har a lokacin take cika kana tace “ ?warai mami to kina tsammanin Ya Khalil ba gaskiya zai fa?a ba kenan ?”. A’a ba haka nake nufi ba , Kar ki manta Khalil na son ma’eesha a jikina ina jin Haidar na yin wani abun amma ban ta?a kawo masa wannan cikin rashin jin sa ba .

Gimtse fuska Mom Hajara tayi tana gyara Zaman mayafin ta kana tace “ Ohhhh wai ke Mamin Haidar bakya ta?a magana ne ba tare da kin saka sunan ma’eesha ba? Komai Ma’eesha Ma’eesha haba don Allah….! Ita yarinya wata can ?asa gajera ga ?iba mara sha’awa mtswww…..” ta ja dogon tsaki tana komawa tare da zama bisa kujeran dake kusa da ita .

Uhm”. Jidder ta furta tana ?aga ?afarta tare da cewa “ Mom sai kinyi ha?uri , Ai wannan ma ka?an ne tun da bata gurin , suyi ta mata ?arin jiki kamar wacce aka ce Aljannar su na ?ar?ashin ?afafunta . Ni yanzu zan tafi 1:30pm muke da shiga exam .

?agowa Mom Hajara tayi tana kallon ta kamin ta kalli ?aton agogon falon , ba distance learning kike yi ba ? . Yessss Mom shi nake yi , Amma exam kin san a?wai wasu da dole sai Mutum yaje hall ya rubuta . Ok Allah ya bada Sa’a . Amin Jidder ta furta tana gyara mayafin ta . Kana ta kalli mami tare da hugging ?in ta “ Bye bye mom sai na dawo ”. Ta furta tana ficewa daga Falon .

Murmushi Mom Hajara tayi cike da son nata ta furta “ Yarinya mai hankali kenan! . Kallon ta Mami tayi tana ca?e baki kamin ta zauna , Muryar Mom Hajara na cigaba da cewa “ Kin ga har Khalil yasa an binciken yarinyar , Ga taxt din shi ya shigo . Ohk duba ?iyar Wacece? Mami ta furta tana kallon Mom Hajara wacce take scrolling chart ?in. ?an gyara zaman medical Glass din ta tayi kana tace “ Waye Alhaji Adamu Billionier ? Wai inkiya ?in sa kenan .

Kallon ta mami tayi tana furta kai anya Alhaji Adamu Billionier ina dai jin sunan sa kamar ?an kasuwa ne babba , amma ban tabbatar ba gaskiya . ?ar sa ce kenan? . Girgiza kai Mom Hajara tayi kana tace “ eh a abin cikar da aka yi ba. Amma yanzu zamu sani ai …daga gobe zasu bata wadataccen tarbiyyar da idan taga mutane zata san yanda ake masu magana da dadin lafazi ”.
**

Gaba ?aya Ma’eesha ta gama birkicewa kuka take yi kamar ran ta zai fita . ?o?arin controlling kan ta take yi amma ta gagara , Wayyo Uncle ban ?yauta ba , na zalunce ka , ban maka halarci ba ban kuma maka Adalci ba . Ka yafe mun Uncle………….?? Tana maganan tana jin yanda yake jawabi ta Mick cikin Arrogant voice ?in nan nashi na jarumta . Muryar sa ta ji yana kiran sunan ta wanda gaban ta sai da ya fa?i….cikin sauri ta fara dai daita natsuwar ta tana rufe diary ?in kana ta goge hawayen fuskar ta wanda bata tsammanin zasu iya daina zuba har ta isa gare sa ”. ?ammata da manyan mata kowa a wurin crushing ?in Wannan soja ake yi , wanda in his young age ya zama major . Da dama na tambayar baya da mata ko? Suna jin an ce eh sai ko wacce ta kara gyara zama tana jiran a gama taro ta amshi card numbern sa .

Cike da Wannan takon nata with confidence na RAINON SOJA take takawa ixuwa inda Yake . Gaba ?aya hankulan mutanen ya dawo akan Wannan kya?y?yawar yarinya wacce ta shige zu?atan mutane da dama . Sunan murmushi take yi amma wasu irin hawaye ne ke bin kuncinta wanda ta rasa fahimtar na menene ita kan ta . Nisha?i take ji ko akasin haka , ga narkakkiyar tausayin sa dake tsuma ta . ?anwar sa ce hala? Kaji wurin an fara maganganu ?asa ?asa . Wow she’s beautiful…..Muryar Aliyu ne ya kuma katse su inda suka ji ya yi magana ta Mick da cewa “ That’s my wife ?? uuuwhmmmmw?? ya hura mata Wani irin sumbata a Mick ….ihu aka saka da Tafi sojojin wasu na ?ara ?amewa na girmamawa . Abun ka ga mace mai fara’a tuni Ma’eesha baki ya?i rufuwa a hankali ta isa gare sa cikin sauri yana ware mata hannu ta rungume shi ?aaaam tana sakin kuka , shafa bayan ta yake yi yana ?an rarrashinta duk da bai san dalilin kukan nata ba . I Always proud of my husband Ina Sonka Uncle Haidar…..Maganan ta ne ya fita ta Mick don basu lura da Mick ?in na kusa da bakin ta ba . Ihu kika ji na mata da maza har sojojin Tsuma suke yi bisa ga nin irin wannan soyayya mai da?i da sanyaya zuciya .basu taba ganin so a ?waratan irin haka ba , bare kuma sojoji da ake gani basu iya soyayya ba . To yau dai ya ?aryata . Murmushi yayi yana kai hannun sa tare da goge hawayen fuskar ta , a hankali ya kamata suna sauka daga wurin ….Muryar Mata kake ji suna furta “ Sweat couple 4 life ?? ”.

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button