KALBIM BOOK 1 PAGE 19
19
*ZUZEAM VENTURES*
Best APHRODISIAC
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
️️️️️️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
**************
Dawowansu Nigeria da dan lokaci Dr Abraham ya bada shawaran dawowansu gabaki daya anan sbd a yanda yaga rayuwar nan din take samun abinda suke so anan bazai wuya ba duba da kusan koyaushe koina kuka akeyi da yanda mutane suke bata ko ake kashewa dan haka anan komai zai tafi musu a sauki sabanin can da akwai wani irin tsananin tsaro da binciken da zai iya kawo karshensu gaba daya.
Wannan ne ya saka gabaki daya Ahalin ZADEEN’s sukai bankwana da komai suka dawo Nigeria inda suka bude sabuwar rayuwa.
Irin suna da tarin dukiya da manyan matsayin dasuke dashi a can qasashen ya saka cikin qananin lokaci suka samu wata irin power a Nigeria sukai suna musamman daman sun jima da yin sunan sbd tsananin taimakon da suke badawa a asibitocin kauyuka da birni da asibitocin gwamnati ma sai ya zamana anata yabonsu ana kaunarsu.
Sam basada sakewa da mutane kaman yanda basa muaamala da kowa sai masu karfin iko,
Ammar gaba daya ya koma ya zama volunteer baya wani zama koyaushe yana gurin yawon asibitoci da kauyuka bada taimakon dan nuna tausayi ga mutane wanda hakan ke qara musu wata irin qima a gurin jamaa.
Daurewa Ammar yakeyi kawai sbd biyan buqatansu amma kaf dinsu babu abinda suka tsana kaman rayuwa da mutane marasa karfi da sukewa kallan kaman dabbobi.
Dawowansu Nigeria yayiwa Mimi dadi sbd Sun samu damar sauyawa Jannah guri da rayuwa,
Jannah ganin yanda familyn suka kasa hakura su dangana sai ta fara kokarin bawa kanta qwarin gwiwan rayuwa dan sakasu farin cikin da kusan suka rasa na shekaru.
Hakan datai ba qaramin tasiri yayiba akansu dan kuwa farin ciki mai tsanani suka shiga sedai kuma qarasa cire tausayi sukai aransu suka cigaba da farautan rayukan mutane.
Ammar ya dena yawon dayake yi sedai ayanzu suna likitocin da suka saka a asibitin gwamnati da manyan na kudi tareda sake kudin da hankali ma baya dauka dan samun zuciya ga wadda haryanxu duk masu musu aikin basu san waye ake nemawa ba dan ko sunanta baa taba fadaba bare wani yaji.
*******
Ummitah dake zaune tana dan dafe gefen cikinta dayake mata wani irin nauyin datake jin kamar zai shigar mata wani gurin rintse idanuwanta tayi ahankali tana dan sauke numfashi ahankali.
Mama dake gefenta sannu tai mata tana cewa
“Kodai zamu tafi asibitin ne Ummitah”
Girgiza kai tayi ahankali tana cewa
“Aa kila zuwa anjima ko idan nasha magani ciwon zai lafa mun”
Kallanta maman tayi tana jin kaman karta bari zuwa anjima su tafi asibitin kawai amma kuma tinawa da ABDULAZIZ yace zai aiko a tafi dasu sbd bayanan yasa ta barta din idan sun tafi kaman yanda ha fada taci gaba da ganin likita acan.
Sayyid ne ya shigo gidan dauke da Farar leda a hannu ta Fruits daya siyo mata yana kallanta yace
“Yaya dai?
Jikin ne?
Mama kodai zamu tafi asibitin ne?
Cigaba da aikin abinci da maman keyi tayi tana cewa
“Eh nace mu tafin amma tace basai antafi ba
A bari zuwa anjiman idan bata dena jin yanayin ba sai mu tafin kawai”
Wayar Sayyid dince tafara ringing da sauri ya daga ganin Hamman ne yake kira.
Yana dauka kai cikeda girmamawa ya gaidasa yana cewa Ummitan ce batajin dadi.
Shiru ABDULAZIZ yayi batareda yace komaiba sbd yanda yaji a zuciyarsa a duk lokacinda akace Ummitah batajin dadi wani irin nauyi da daci yakeji ya cike zuciyarsa sbd ganin kaman ya gaza ne har akai mata auren wuri daya sakata a halinda take ciki wanda bata isaba yake gani kwata kwata hakama an sauya masa tsari da burinsa gaba daya akanta dan kuwa duk gwagwarmayarsa da nemansa akanta ne sbd ita ne,
Komai dayake son ya zama a rayuwarsa sbd Ummitah ne,
Sbd ya inganta rayuwarta ya hanata shiga quncin daya taso a cikinsa,
Sbd ya bata farin ciki da gatan da kowanne da zai samu amma a lokaci daya an sauya masa komai an lalata masa rayuwarta ta hanyarda baida zabi bayan karban hakan hannu bibbiyu dan hakan nema ya karbi Sayyid tareda alqawarin inganta rayuwarsa shima kamar qanin dasuka fito ciki daya.
Numfashi me sanyi ya sauke tareda bude baki a natse yace
“Ku shirya gaba dayanku yau komai dare zaa taho a tafi daku,
Karku bari Ummitah tayi komai hakama basai kun tafi asibitin ba,
Zanyi magana da Ummitah”
Da sauri Sayyid din ya bawa Ummitah waya ta amsa ahankali tareda dorawa a kunnanta ta ambaci sunansa ahankali cikeda kewarsa datake tsananin ji da buqatansa a kusa da ita.
Jin sautin muryanta cikin sanyi daya sauka a kunnensa ya sanyasa miqewa ahankali daga inda yake zaune ya nufi bakin window din dakin ya tsaya yana sauke numfashi mara sauti zuciyarsa na sake daukan wani irin nauyi da dacin rashin kasancewansa a kusa da ita a daidai yanzu datake tsananin buqatansa.
“Ummitah” ya ambaci sunata ahankali cikeda nutsuwa da sautinda ita kadai yakewa magana ahakan sbd matsayinta rayuwarsa gaba daya daban yake da komai.
Hawayene masu dumi suka gangaro mata ta rintse idanuwanta kuka mara sauti na zuwar mata a karo na farko tace masa
“Hammah inason ka dawo dan Allah,
Hammah inason na haihu a hannunka kaman yanda aka haifeni a hannunka,
Hammah ka…….
Kasa qarasawa tayi sbd hawayen da suka tsananta mata gudu haka kawai buqatansa take a kusa da ita sbd ita kadai tasan yanda take jin cikin jikinta.
Mama da sayyid shiru sukai jikinsu na sanyi batareda kowannensu ya iya cewa komaiba saima tsinkewa da mama tayi tana ajiye aikin datakeyi batareda ta juya ta kallesu ba.
Acan bangaren shiru yayi tareda kasa cewa komai dan duk abinda zai samu a aikin daya kawosa ko shine zai qarasa sauya rayuwarsa to tabbas saiya bar qasar ya koma gida a goben nan.
