KALBIM BOOK 1 BY MAMUHGEE

KALBIM BOOK 1 PAGE 36

36
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494

 

***************
Kasa motsawa tai daga inda take tsayen hakama iskan qurin ta sauya gabaki daya da qamshin data tabbatarda nasa ne sbd shine ya doki hanci da fuskanta a lokacinda ya wuceta batareda yasan da akwaita bama,

A rayuwarta kaf tinda ta taso bata samun kanta a inda aka taba nuna baasan da existence nataba,

Idan baa kulata da bata kulawa tareda nuna mata mahimmanci ba sbd Sunan familynta to zaayi sbd dukiyar datake dashi kokuma sbd kyau da daukan ido datake dashi amma a karo na biyu an nuna baama san da matsayinta n yar adamba kuma duka daga mutum daya.

Tsananta bugawa zuciyarta keyi hakama ta kasa juyowa ta kalli bayanta da dukkaninsu suka nufa dan bin bayansa zuwa ga doctor.

Muryansa daya ambaci sunan doctor dashine a wani irin nutsuwa ya saka numfashinta fita da wani irin tsananin sanyi daya sakata juyowa ahankali sedai ta kasa kallansa sbd yanda zuciyarta ke bugawa.

Juyawa tayi tabar gurin tana fitowa harabar gurin sbd jin tai tana suffocating.

Tana ji wayarta na ringing kuma tasan Ammar Zad ne amma bata iya dauka sbd nunfashinta toshewa yake haka kawai sbd bugawan da zuciyarta keyi.

Ringing wayar taci gaba dayi amma sam bata iya ko dauko wayar daga handbag dinta.

Taxi ta tare ta fada tabar asibitin ta koma saloon sbd motarta nacan ta baro.

Doctor kuwa kallan AZIZ din yayi yana sauke ajiyar zuciya me tsananin sanyi da nutsuwar abinda yake son fada masa kafin ya bude baki yace

“Muna saka ran zata farfado kowane time sedai a abinda muka bincika ya kawo mata collapsing shine ta samu bugawan zuciyan da yayi triggering matsalan datake dashi a zuciyanta wanda muna jiran fitowan sakamakon duka binciken da muka fara yi mata na dan abinda muka gani tukuna.””

Shiru gurin ya dauka sbd babu wanda ya motsa a cikinsu kallan likitan suke kamar basu fahimci abinda ya fadan ba dan haka ya kallesu shima likitan daya bayan daya tukuna ya tsayar da kallansa akan AZIZ da shima bayanin yake buqatan sake ji sbd a lamarin daya shafi iyalinsa yanason a ringa masa dalla dalla.

Ganin hakan dr ya sauke ajiyar zuciya yace

“Mun dan gano tanada matsala a zuciyarta sbd yanayin bugun zuciyar nata da muka duba vayan dawowansa ba bugun zuciya bane na cikakkiyar lafiyayya,
Bai taba bayyana va sai yanzu data samu bugun zuciyan dayayi munin daya bayyanarda ciwon gaba daya,
Amma muna jiran sauran result da kuma wainda zamuyi mata dan tabbatarda komai”

Hawaye ne masu tsananin zafi suka tsinkewa Fiddausi suna gangarowa akan fuskanta tayi baya tana komawa nesa dasu ta zauna tana cusa kanta cikin kafafunta.

Mama kuwa gaba daya bata gane turancinba dan haka sayd da AY din take kalla tana jiran reaction dinsu ya bayyanar mata lafiya ko ba lafiya ba.

Sayd wani irin nauyi ne ya danne kirjinsa da daci dayake gauraye bakinsa gaba daya idanuwansa na sauyawa sedai bai bari hakan ya bayyanaba ya danne tareda dagowa ya kalli AZIZ AY LIMBA wanda kafafunsa suka so kasa daukansa duk jarumtarsa.

Saurin taresa mama da sayd din sukai tare ya kasa dago idanuwansa ya kalli ko dayansu sbd yanda sukai jajir a take cikeda mafi girman ‘dacin zuciya da wani irin nauyin daya danne kirjinsa da babu komai a cikinsa sai fili da tarin quncin daya taso a cikinsa.

Kujeran aka kawo masa da sauri ya zauna har lokacin bai iya dagowa ba bare iya cewa komai.

Sayd ne ya kalli dr din da jajayen idanuwansa da suka sauya sosai shima sbd su bazaka iya controlling nasu ba ya bude baki yana kokarin daidaita kansa yace

“Ok dr zamu jira results din da duka sauran bayanan,thank you”

Juyawa dr yayi ya koma ciki tareda nurse data fito kiransa.

Shiru gurin yayi babu wanda ya iya magana sai sayd da mama take sake tambayar ayi mata bayanin meya samu Falaq din sbd itama tin bata jiba ganin yanayinsu ya sakata jin ciwon zuciyarta na neman tasowa dan kirjinta toshewa yafara yi fargaba na shigarta me girma.

A taqaice sayd yayi mata bayanin abinda aka fadan yana dorawa da kada ta damu insha Allah khairan.

Duk yanda taso daurewa kasawa tayi kirjinta ciwo yake mata dan haka Fiddausi dake kuka sayd ya saka ta kawowa maman ruwa ya bata yana cewa nurses su kira doctor ya dubata.

Yanda ya zauna baice komaiba shiru yayi sukaci gaba da zaman jira.

Sallah sukaje sukai suka dawo cigaba da jira amma ba wani zance karshe dai an fito da falaq din zuwa vip room dayake can sama dan haka suka koma can.

Shiru dakin babu maganar komai sbd uban gayyar baicewa kowa komaiba har lokacin
farfadowan falaq din yake jiran gani tukuna har doctors din ya samu magana dasu kafin su wainda suke tareda ita da abinda ya faru.

Mama dai dole aka maidata gida sbd duk ta rikice jikin nata ya tashi dan haka gida aka maidata gida tareda Fiddausi ma da nurse da sayd ya daukan mata.

AZIZ dinne ya kwana a asibitin a zaune sai sayd da shi duk inda ko inuwar AZIZ take yana nan.

Guraren 8 na safe ta farka cikin tsananin sanyi da rashin walwala ta ciwon daya sauyata a lokaci daya.

Tana bude idanuwanta akan Daddynta ta fara saukesu hawaye masu dumi suka gangaro mata ta gefen fuskanta ta bude baki Ahankali tace

“BestDaddy”

Har cikin ransa yaji saukan sanyin muryanta wani irin daci da qunci yafara cike koina a zuciyarsa ya bude idanuwansa da suka kasa komawa daidai ya zuba mata yana tayar da ita zaune ahankali yana dora hannunsa akan fuskanta ya shafa ya bude baki da muryansa me nutsuwa yace

“Hey Falaq Aziz limba,how are you feeling?

Wasu hawayen ne suka gangaro mata ya ciro handkerchief dinsa yana goge mata ahankali yace

“Yaya dai?kina jin ciwo ne?
Where?a aina?

Kwantawa tayi jikinsa tana girgiza masa kai alaman batajin ciwo koina.

Dr ne ya shigo ya qara dubata dakyau kafin yace zuwa anjima ma zasu iya tafiya gida ba damuwa ko matsala bane.

Angama dube dube da sauran duka test da full checkup da AZIZ yace ayi mata sbd yanason a bayyane masa komai daya danganci abinda yake damunta komai yanason a bincika a sanar masa zai nema mata lafiya indai Allah ya yadda ta samu lafiyar koda zai rasa komai daya mallaka.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected