KALBIM BOOK 1 PAGE 36
Koda suka dawo gida gabaki daya babu wata walwala ko haske ko kadan a tattare dashi suma duka gidan jikin kowa a mace yake sedai sbd falaq din su Fiddausi da mama suka sake sunata kulawa da ita da wasa dan ta sake kuma tafara sakewan sbd rashin qarfine kawai na wuni da kwana a kwance yake Damunta sai kuma asalin weakness da ciwon yake sakarwa meshi datake ji.
Doctors sun sanar dashi results da binciken duka suna kammaluwa zasu kirasa yazo ayi masa bayanin komai dan haka duka schedules da ayyukansa na wannan lokacin ya saka sayd yayi cancelling nasu ya bawa falaq time dinsa sosai wanda hakan ya sakata komawa daidai rigimarta da komai ya dawo musamman dataga mama ta dena mata fada dan haka murna ta ringa yi da ciwon datai.
Ryan kuwa tini ya sallamesa aka daukan mata wani drivern bayan an sanar dashi daga lokacinda yayi wani gangancin da ita a mota ya gama aikin.
Shi da Sayd ne a cikin damuwa sosai akan tinanin ciwon nata wanda basu gama sanin yaya yakeba dan haka koyaushe cikin jiran kiran doctors yake hakama sayd Ciwone yake cinsa na tsakanin Uba da ‘ya tinda aka fada ciwon sedai kawaicinsa da yanda yabarwa AY ita bai nuna damuwarsa a fili ba dan haka ya fara bibiyan bayanan ciwon zuciya da matsalolinta.
Ganin hakan sai mama ma suka nuna mata ba wani damuwa bane falaq will be ok insha Allah,
Da wannan maman ta sake itama ta koma yanda take.
Tinda ya taso bayan rasuwar mahaifinsa zuciyarsa tafara bushewa daga mutane da lamarin duniya,
Ya rasa Mahaifiyarsa zuciyarsa ta karbi hakan cikeda jarumta da taurin zuciyar daya reni qanwarsa dashi,
Ya rasa Ummitah dayafi so a duniyarsa fiyeda komai da kowa zuciyarsa ta rasa duk wani emotions daya wuce na falaq,
Ba masu fada ba shi kansa yasan zuciyarsa a bushe take shiyasa a duniyar tycoons ake kiransa da monster amma baisan meyasa yakejin zuciyarsa na neman karyewa akan ciwon dayake tafe ga ‘yarsa daya tak da itace kuzarin datake riqesa daga collapsing a duk lokacinda rashin Mahaifiyarta ke neman illata kwakwalwa da tinaninsa tareda jinsa da ganinsa.
Rufe idanuwansa yayi Ahankali yana hadiye abinda yake cikeda zuciya da kirjinsa.
Sayd ne yai knocking ya bude kofar palon y shigo a natse yazo gabansa ya tsaya cikin girmamawa da nutsuwa yace
“Hospital sun kira the results are out da komaima”
Bude idanuwan yayi Ahankali tareda zubasu akan sayd din wanda ya sauke nasa idanuwan.
Shiru gurin y dauk kafin ya miqe yana daukan wayarsa dake gefensa yana cewa
“Lets go”
Bayansa sayd yabiyo yana zuwa inda keys din motocin gidan yake ya dauko key yana biyosa da sauri.
Mota suka shiga zuwa asibitin batareda kowa yayi magana a motarba har suka isa.
Suna isa kai tsaye office din dr A Raheem suka nufa wanda shine babba gaba daya a asibitin suna isowa shine da kansa ya budewa AZIZ din kofar shiga yana masa barka da zuwa.
Amsawa yayi yana gaisawa da doctors biyu dake dakin wainda manyan neurologist ne wanda sune zasuyi masa bayanin duk abinda ya shafi ciwon yarsa.
Shiru office din yayi bayan Dr Raheem ya gabatar masa dasu fara koro bayaninsa yayi cikin tsananin nutsuwa.
“Mr LIMBA kaman yanda aka fara sanar da kai tabbas ‘yarka na dauke da ciwon rashin qwarin zuciya wanda dashi tazo duniya sedai baya nunawa sbd the more tana girma the more yake kokarin fara bayyanarda kansa,
A yanzu ya bayyana ne sakamakon shock ko mummunan bugawan zuciyar data samu,
Ciwone chances din warkewansa yake 20%
Zaici gaba ahankali ahankali zuwa lokacinda zuciyarta zata buqaci heart transplant maana dashen zuciya kafin tata ta iya dakatawa,
Ciwon wasu yakan zo musu da rami ne a zuciya kaman hole haka”…. ya fada yana kunna musu qatuwar screen din dake office din yana nuna musu yanda ciwon yake.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*
