interstitial
KALBIM BOOK 1 BY MAMUHGEE

KALBIM BOOK 1 PAGE 37

37
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga  jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/JMSe2The4Q2F5tLdzGduyC
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494

********
Screen Sayd ya zubawa idanuwansa yana kallan yanda ake nuna musu cutar take a zuciyar dan adam.

AY idanuwansa da sukai jajir har suna radadi ya zubawa dr din kunnuwansa na ji masa mummunan labarin dayafi rasa komai da komai daya mallaka muni.

Dr kuwa cigaba yayi da cewa

“Zaa dorata akan activities da zaa fara kiyayewa da dorata akai tin yanzu batareda an daga mata hankali tasan meyake damuntaba dan tayi qanqanta data san hakan kuma sbd Nata baiyi nisan da zaa cire rai ba sedai kuma bamusan abinda gaba zatai ba wadda idan har ankai stage din da baaso to sai anyi mata heart transplant din wanda samun donor shine abinda yakeda wuyar datafi komai a duniyar nan”

Hotuna da videos na yanda ake heart transplant ya kunna yana cigaba da musu bayani cikin kwantar musu da hankali da kokarin ganin ya fahimci komai tareda sanin ba wani abu ne me mugun tashin hankaliba sbd ciwonta baiyi nisa ko girman da zai gagaresuba insha Allah.

Sayd dagowa yai ahankali daga jinginen dayake yana saukar da idonsa da kyau akan hotinan dake yawo akan babban screen din na heart transplant da asalin tabon dayake bari a kirjin da duk aka cire zuciyar ko dasata.

Kasa dauke idanuwansa yayi daga hoton wanda ya saka kunnuwansa daukewa daga jin sautin bayanin da doctors keyi sbd mamaki me tsananin gaske da shock dayake neman shigarsa sbd sanin wannan shine irinsa sak a kirjin Ummitah wanda bai taba saninta dashi ba dan ko ranar da zaa kaita asibitin haihuwa shine ya saka mata kaya da kansa dan bazata iya ba kuma babu wannan dinkin a kirjinta sai bayan rasuwarta ya gansa.

Juyawa kansa ya farayi sedai kuka Cs akai mata aka ciro Falaq,
Ana cs na haihuwa a kirji ne??
Girgiza kansa yayi idanuwansa na sauyawa yana kokarin tina babu dinkin cs da akai mata a mararta.

Jin yayi ya dena gane komai kansa na yin dum..

Jajayen idanuwansa da suka sauya gaba daya a take ya kalli dr Raheem ya bude bakinsa muryansa a shaqe yace

“Dr a wane gefe na kirjin ake aikin?
A jikin dan adam akwai inda zaa iya masa tiyata a cire ‘da bayan cikin?
Meye dinki a kirji kuma a bangaren hagu yake nufi??

Kallansa dr yayi yana mamakin tambayarsa
AY kuwa sam bayama cikin cikakkiyar hayyacinsa na fahimtar me Sayd din yake tambaya yana zaune shiru idanuwansa sunyi laushinda ayau zaka gane rauninsa a bayyane.

Cikin bude masa komai da kyau dr yace

“Babu inda ake iya cirewa mace baby bayan cikinta maana qasan cikinta wanda wasu ana yankan tsaye wasu kuma na kwance,amma idan har kana magana ne akan wannan yankan na setin zuciya wanda ya tafi daidai irin wannan da kake gani to idan a jikin rayayye ne akwai tabbacin antaba masa aiki a zuciyar, idan kuma matacce ne to tabbas shima anyi masa aikin ne a zuciya kokuma ma an cire zuciyarne tinda a macen yake”

Jiri ne ya dauki Sayd daga zaunen da yake sbd kansa kasa gane komai yai
Jin yake kamar bai taba zama aji karatu ba sbd jin yayi turancin ma kamar ya dena ganewa dan haka ya juyo idanuwansa da sukai nauyi sosai ya kalli AZIZ wanda shima kwata kwata jinsa yai qasa akan bayanan likitocin gameda ciwon daya bayyana lokaci daya a tattareda rayuwar yarsa wadda bayan kuruciya ma yanzu babu abinda zata gane a ciwon ko anmata bayani…..

“Innalillahi wainnna ilayhi rajiun,Ya salam”

Ya fada yana tallafe goshinsa da hannuwansa biyu idanuwansa na rufewa ya budesu tareda jimawa shiru kafin ya dago ya kalli kowannensu ya bude baki baki yayi musu godia tareda miqewa.

Sayd ma miqewan yayi baa hayyacinsa ba sbd yayi mugun zurfi da nisa da tinanin dayake sake toshe kansa.

Ta email akaiwa Sayd forwarding copies na results dinta da sauransu sbd duk inda zasu sauya ganin likita ko qasar ma zai zamana sunada record dinta.

Tafiya suke babu me magana hakama babu wanda yake cikin cikakkiyar hayyacinsa har suka isa mota suka shiga kowannensu yayi shiru.

Sayd kasa tada motar yayi sbd bayajin zai iya driving cikin daurewa ta juyo ya kalli LIMBA da babu abinda yake iya cewa sai yaji tsananin tausayinsa dan ganin rauninsa da karyan kowa ne yace ya gani.

Jin yayi jarumtarsa ta dawo dan shine tamkar bangon dayake taresa a duk lokacinda rauninsa ya taso dan haka yake koyaushe a shirye daya basa kariya koda shi zai rasa nasa ran sbd kaunar Ummitah data hadasu haduwa ta har abada.

Numfashi me sanyi da ciwo ya sauke yana dora hannunsa ya tada motar yana tattaro nutsuwa da karfin hali ya hau hanyar gida.

Tafiya ce ta damuwa da rashin haske ko kadan a cikinta sukai har suka isa gida..

Suna isa kai tsaye babu wanda ya gansa ya shige bangarensa ya rufe kansa sai alokacin yaji kirjinsa nai masa radadi da ciwon daya sakasa zubewa palo qasa yana dafe kirjinsa yana lumshe ido yana karban radadin sbd babu yanda zai iya dauresa.

Yana jiyo ihun falaq din da Fiddausi da dayar me aikinsu a baya suna wasan daya sakasa rintse idanuwansa yana jin inama shi Allah ya kaddarowa wannan ciwon ba Falaq ba sbd harko yaushe yana fatar kasancewa da Ummitah koda a fatalwa ne idan har zasu hadu.

Falaq ce jinin Ummitah daya rage masa a duniyar,
Falaq itace take rage ciwon radadin rashin mahaifiyarta daya bar zuciyarsa empty idan har ciwonta barazana ce ga rayuwarta da zata iya rasa zuciyar da itace rayuwar yaya zaiyi da wannan kaddarar da Allah daya kaddaro masa shi kadai ne zai kawo masa dauki…

Zuciya ce zata buqata idan lokaci yayi wanda ba aba bace da tarin dukiyarsa zata siya,
Meye amfanin kaf abinda ya mallaka idan har bazasu nemo masa abinda zai buqatan ba?

Falaq dake wasan ruwa da water guns dasu Fiddausi farin ciki kawai take jin kanta yana ciketa wasa sukeyi sosai batama san daddynta ya dawo ba kuma yana jiyota radadin zuciyarsa na qaruwa duk dariyarta ta shiga kunnuwansa sbd ahankali ahankali wannan farin cikin da dariyar zasu disashe daga rayuwarsu kenan.

Sai magrib suka dena wasan suka dawo ciki Fiddausi na janta daki ta sakar mata ruwan zafi sosai sbd sanyin da sukai wasa dashi karya kamata.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected